Sashe 113
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ita kuwa Bintu tana can Hajiya Babba da Ammi da inno kai harma Hajjo da bata gidan suna faman yi mata gyaran da bata samu ba,gyaran gata wanda suke san zautar da jikan nasu a ɓangaren fadamar Bintu,tana yawan tunawa dashi tana kuma mararin ganin sa,sai dai kuma yadda su Inno suka kasa suka tsare yasa bata da hanyar ganin sa ko da daga nesa ne.
Yau kimanin kwana biyar kenan da warwarewar ƙullin dake cikin gidan Alhaji Baba,hankula sun fara kwantawa farinciki ya fara wanzuwa a zukata,yayin da wasu suke cikin halin tsaka mai wuya,kamar dai su Hajja ke nan,wadda tunda abun ya faru babu wanda ta kuma gani a ɓangaren ta,tun daga kan ƴaƴan ta har zuwa ƴaƴan kishiyoyinta da surukanta,dan kuwa Alhaji Baba yayi jan kunne mai tsauri akan kowa dake cikin estate din,duk wanda yaji koda labarin ya kalli hanyar ɓangaren Hajja to bai yafe masa ba, wannan shine hukuncin da ya fara zartarwa akanta,a halin yanzu kuwa kaf ahlin ALHAJI BALARABE babu wanda labarin abinda ya faru bai same shiba,su abdulraman da abdulshakur duk sun dawo cikin ahalinsu farin cikin ganin mahaifinsu da ɗan uwansu shi ya saka su cikin farin cikin da ya hana su alhinin abun alhinin da ya faru,kowa ya dawo da iyalan sa ya kafa sabuwar rayuwar tafarinciki tare da ƴan uwansa,a ɓangaren Taufika kuwa tunda labarin ya sameta ta rude tare da shiga wani irin hali na damuwa, wato dai yanzu ana nufin ace Ya Abdallah ya haramta a gareta,bata jin zata iya wannan jihadin hakan ne yasa ta tattaro daga ziyarar da suka kaiwa mahaifansu suka dawo Abuja cikin ESTATE.
Abdallah ya koma bakinsa,kamar yadda ya saba a baya,ya na cigaba da tafiyar da asibitin sa,amma duk wannan abun da yakeyi ƙarfin hali yake,dan dai kawai Abdallah ya kasance muskilin mutum ne,amma fa haƙika zuciyarshi tana cikin wani yanayi na rashin Bintu, wanda a kwana kin ne ya tan-tance tsakanin ƙarya da gaskiya,ko yanzu dawowar shi daga asibiti kenan,ya shiga shawagi a tsakanin part ɗin iyayen nasu ko Allah zaisa yaci karo da Bintun,sai dai har ya gaji ya yada zango a part ɗin Hajiya Babba wanda ya fi bada tabbacin cewa Bintu tana nan bai ga ko usainar fafi ba bare kuma buntu,yana kwance jikin ƙatuwar kushin ɗin falon idanunshi a lumshe kana ganin sa kasan da akwai gajiya a tare dashi gakuma ƙishin ruwan Bintu da ya addabeshi,Muryar Hajiya Babba ce tasa ya ɗan bude gajiyayyun idanun sa,kai kuma lafiyar ka kazo nan ka kwanta cikin kin kayan aiki?bai kulata ba,sai dai can kasan zuciyarsa yake cewa ina fa lafiya Hajiya Babba kun kama matar mutane kun riƙe,amma a fili sai yayi mata banza dan gaba ɗaya haushin su yake ji,bata nuna ta gane komai a tare dashi ba, tace"ai ya kamata kaje ka kwanta ka huta tunda da alama yanzu ka dawo!'tamkar ba dashi take ba,ko kallon inda take baiyi ba, sai ɗan gyara kashingiɗar shi da yayi,hakan da yayi ne yasa ta gane bai da niyar tashi,ƙwafa tayi tana cewa dani kake zan can!'ta tafi tana ƴan miticinta,bata san kunnen Abdallah da ji ba, har da su cewa ita sam bazata yadda da zaman Bintu dashi ba,dan Bintun bazata iya da wannan halin nasa ba,a saman laɓɓan shi yace"da data zauna dani har zuwa yanzu ke kika zauna mata dani?
kamar anjehota haka ta ta fado cikin falon,dawowarta kenan ko hutawa ba tayi ba,tazo ganewa idanunta abinda taji,turus tayi ganin wanda yake hakimce acikin falon,sai kuma take jikinta ya shiga rawa,har ta ma manta abinda ya kawota,itafa bata jin zata iya daina san Ya Abdallah sai dai idan mutuwa tayi,duk lokacin da ta ganshi saitaji tamkar ana ƙara mata wutar sanshi,cikin sanyin jiki ta ƙaraso tsakiyar falon,kana ta nemi guri kusa da inda yake ta zauna,tare da gaida shi cikin kiɗimewar murya,da lafiya ya amsa mata shi ma badan kallon ƙuril ɗin da take binsa dashi ba,da bazata san cewa ya amsa ba,sai kawai ta samu kanta da ƙarfin halin fara yi masa jaje akan abinda ya faru da kuma fatan Allah ya tsare gaba.
Buɗe idanun ta tayi a hankali,idanun ta nadan komawa suna lumshewa,ita kam ta rasa wannan abu na magani da meyene,gaba ɗaya nema suke su zamar da ita ƴar ƙwaya daga sun banka mata wancan sai wan Nan,wai duk maganin sanyi ake bata,a fadarsu dai,gashi wasu da yawa idan ta sha sai sun sata bacci kamar dai yanzu da wannan ya sakata baccin yamma,saida ta ɗan huta kana ta miƙe har zata shige toilet,sai kuma taji jikinta ya dauki wani sanyi,haka zuciyarta ta shiga bugawa da sauri da sauri,fasa shiga tayi ta juya akalarta zuwa ƙofar da zata maida ita falon Hajiya Babba,a hankali ta buɗe tare da cusa kanta,sai dai kuma tozalin da tayi da Taufiƙa durƙushe gaban Abdallah shi ya nemi hautsina tunaninta,da sauti ta ƙarasa fitowa,sai a sannan ya kula da abinda Taufiƙan takeyi,ruwa ne take tsiyayawa Ya Abdallah a glace cup,tana ƙoƙarin miƙa masa,da sauri BINTU ta rike cup ɗin, ɗagowa tayi dan ganin waye sai tayi ido huɗu da fararen idanun Bintu da kyakykyawar fuskarta da take wani irin glowing na tsananin gyaran da take sha, murmushi tayiwa Taufiƙa da ta daskare a gurin, tana cewa ayya Anty Taufiƙa saukar yaushe ashe kin dawo?ta faɗa tana mai shanye ruwan,yayin da idanunta suke san kallon idanun ogan nata amma sam hakan ya gagara,sai ɗan tura bakinta da tayi,wanda batayi aune ba, taji Abdallah ya sunkuceta cikin sauri sai waje,wani irin kuka Taufiƙa ta shiga yi mai tsanani da ban tausayi,ita kuwa Bintu magiya ta shiga yi masa ya sauke ta kar su haɗu da wani,ba dan hujjarta ya sauketa ba,sai dan baya son kwakwazonta ya janyo hankalin Hajiya Babba,kama hannun ta yayi suka fara tafiya wanda a da taso yi masa gardama saboda tsoran fadan Hajiya Babba,sai kuma taji baza ta iya ba,
Cikin nasara da fatan Abdallah basu tarar da inno a falonta ba,hakane ya ƙara bashi ƙwarin gwiwar jan Bintu har can cikin ƙuryar ɗakunsa,suna shiga ya juyo da ita gareshi yana fuskantar ta,sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsun hannunta,a hankali ya matso daga da ita,kana ya ɗago fuskarta,ita kuma tayi saurin rintse idanunta,zubawa eye lashes ɗin ta ido yayi,yana kissima abubuwa masu yawa can kasan zuciyarsa,a jikinta taji irin kallon da yake mata,dan haka ta shiga ɗan ware idanun nata dan ganin abinda yake kallo a jikinta,idanunta ne suka shige cikin nasa,yayin da ita kuma gaba daya ta diririce,cikin sanyin murya da tura baki tace"zan tafi kar Hajiya Babba ta nemeni!'haɗe fuskar ta yayi da tashi kana ya fara magana cikin shu'umar Muryar sa,me saka lakar mutum narkewa,yace"Bint""me kuke nufi dani ne ke da kakanninki?cikin rashin fahimta tace"kamar ya?cikin tura kanshi cikin wuyanta yace"da suka ƙwace minke ke kuma kika biyesu saboda baki damu dani ba,ya kuma tura kanshi a wuyanta yana shaƙar ƙamshin ta da yake neman zauta tunaninsa,yana faɗin Ummm Bint na gaji haka bazan iya ba,bazan iya nisa dake ba,bazan iya raba makwanci dake ba,bazan iya nisan tar numfashinki ba,Ina son halinki,inason kyawunki,inason nasabarki,Bint Ina son wannan ƙamshin naki,komi naki abinso ne,ya ƙara sa faɗa yana sauke mata numfashin sa,wanda yake hadewa da ƙamshin jikinsu yana bada wani irin yanayi mai wuyar fassarawa, maganganun Abdallah sun rikitar da tunaninta sun kuma jefa ta cikin tunanika iri iri,ji tayi ya ɗago kanta cikin wani irin sanyin jiki,ya sumbaci saman lip ɗin ta,kana yace"my Bint,kije Amma ki sani zaki bar mijinki da kewarki da muwar rashinki zata iya jefani wani hali!'daga haka ya saketa ya faɗa toilet,binsa tayi da ido,tana jin wani irin abu na mata yawo a tsakar kanta,cikin mutuwar jiki ta fita daga ɗakin,tana ƙissima yawan damuwar ta akan damuwar Abdallah,
Dady Habib fa yana cikin kin tsaka mai wuya,duk inda ya motsa sai yaji kukan jarirai,babu hali bacci ya ɗan fizge shi sai yayi mafarki da wasu daga cikin ƴan mata da samarin da ya salwantar da rayuwarsu,ko ina yayi babu daɗi,ji yake inama yana da halin ta riyo rayuwar sa da yayi domin ya goge duk wasu kura kurai da ya aikata,idan ka ganshi baza kace wannan hamshaƙin mai kudin bane mai ji da dukiya,su kansu masu tsaran shi sun fara tausayawa halin da yake ciki,dan ganin tun kan aje ko ina Allah ya fara kama shi da irin abubuwan da ya shuka.
A yanzu dai Alhaji Baba ya samu nutsuwa,hankalinsa ya kwanta, duk inda ya juya ƴan uwanshi da ƴaƴan shi da jikoki ne suke walwala,babu wani abu dake damunshi sai ɗan damuwar Habibu,shi yasa yake tunanin kiran Abdallah dan afito dashi haka,a ganin Alhaji Baba ai idan aka barshi da hukuncin Allah ma ya isa,su Alhaji Nasir kuwa tuni ya yanke ma amalar a minta a tsakanin su,sai dai mutumci,har kar kasuwanci da duk wani abu da ya shafe su ya yanke,ta kanas Alhji Salisu mijin Nana ƙarama yazo ya gurfanar agaban Alhaji Baba ya roƙe shi gafara,tare da neman masa gafarar Nana ƙaramar,dan tunda suka koma gida take borin sai ya saketa tunda baya san mahaifinta shi da mahaifinsa,kuma dama ba dan Allah ya aureta ba,dan haka sai ya saketa, Alhaji Baba a take ya kira wayar Nana ƙarama ya bata baki tare da nasiha mai ratsa jiki,babu yadda zatayi dole haka tayi hakuri ta ɗan gana ta zauna a gidan mijinta,