← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 120

Sashe 96

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Daga ɓangaren su Laila kuwa tunda Abdallah ya fita suka taru gaba dayansu a falon,Laila ce ta fara neman da su gabatar da junan su,dan tana son sanin su Dije da kuma abinda ya kaisu gurin nan,Aikuwa ba tare da ɓata lokaci ba Dije ta bawa Ummi Laila duk kanin labarin abinda ke faruwa a cikin zuri'ar Alhaji Balarabe,abinda kawai da bata faɗa ba shine Bint saboda Dije har yanzu bata fahimci inda maganar matar ta nufa ba bare zuciyar ta ya kawo mata cewa mahaifiyar Bintu ce wannan,sai kuma labarin Nafisa wanda bata san duka al'amuran ba,kuma ganin ta bai shafi Lailan ba,ita dai ummi ba tacewa Dije komai akanta ba tunda ta fuskanci bata sani ba.

Cikin son nuna ƙarfin ikon sa,da kuma aiwatar da ƙudurin sa yasa afito da Bintu,lokacin da aka fito da ita hannayen ta ɗaure bakinta kuwa duk yayi alamun jini jini kana dubanta kasan tasha marika,da wani irin sauri Abdallah ya nufeta,sai dai kan ya kai ga ƙara sawa yaji an riƙeshi ta baya ita kuma Bintu wani ya saita wuƙà amaƙoshinta,Dady Mansur yace"yaro ka tsaya iya matsayin ka na gaya maka nan fadata ce"idan ka kuskure abinda nake so yanzu zan sa afarke min wuyar wannan ƙwailar matar taka!'Dady jafar ne yayiwa Abdallah alama da yayi hakuri su gabatar da shirin su ba tare da sun samu tangarɗa ba,hakanne yasa Abdallah danne zuciyarsa, Bintu kuwa duban Dady Mansur take ita ma cike da mamaki dan tunda aka kawo ta gidan bata taɓa ganin shiba,dawo da hankalin ta tayi kan Dady Abubakar da yake magana ƙasa ƙasa irin ta majinyata yace"bazan taɓa sanar da kai abinda kake son sani ba sai dai ka kasheni!'dariya Dady Mansur yayi tare da cewa yo ai bakai zan kashe ba kaga waɗanda zan kashe,wata ƙilma na haɗa da ɗan raino!'ya faɗa yana kallon Dady jafar,cikin abinda bai wuce sakanni ba, Bintu ta dinga tariyo Muryar a ƙwaƙwalwar ta tana kuma auna a wajajen da take jin muryar da kuma fuskar mai Muryar,kamar an fuzgo maganar daga bakinta,haka kuma tamkar dirar mikiya su Abdallah sukaji maganar,nunashi tayi da yatsa bakinta na rawa tace"YAH,,,ABDALLAH WALLAHI,,,,WANNAN BA DADY MANSUR BANE DADY HABIB NEE,,,......

Wash

Fatima y Adam✍🏽
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

```Page 54 ```

Cikin matuƙar mamaki da razana gaba ɗaya suka kalli Bintu hatta da shi kansa uban gayyar,zuba mata ido sukayi yayin da A hankali kuma suka maida duban su kan nanu suna so su gano ta yaya ya zama Habib bayan fuskar Mansur suke gani,cikin tashin hankali Bintu ta kuma cewa Wallahi ba shi bane,ga Muryar sa nan!'daga bayan su suka ji ance tabbas Bintu wannan ba Mansur bane Habib ne,gaba ɗaya suka juya dan ganin mai wannan maganar,cike da mamaki suke duban sa ba kowa bane sai Alhaji Rufa'i,wanda ita Bintu bata san shi ba,ya cigaba da cewa kai kam Habibu ka gama taɓewa duniya da lahira domin Allah ma ba zai yafe maka laifin hada shi da wani ba gakuma haƙƙi wanda shima bazai yafe maka ba har sai waɗan da kacuta sun yafe maka,kuma suma bazasu yafe maka ba har abada!'

Cikin tashin hankali ya nufo Alhaji Rufa'i yana cewa kai kuma daga ina waya kawoka gurin nan?kuma a ina kuke da shaidar cewa Habib ne agaban ku ba Mansur ba?daga bakin ƙofar shigowa suka ji wata Muryar tana cewa Nine tabbaci!' gaba ɗaya suka kuma ɗibar idanun su suka mayar kan Dady Mansur da yake sako kansa falon,kai wannan abun mamaki da yawa yake,to wai me yasa kuke san ruɗa mana tunani,cewar Dady jafar ke nan da ya rikice da mamaki,Dady Mansur yace"karkadamu jafar abun afili yake Nine nan Mansur na ainahi wanda kuke zargi da laifin ɗan uwana!'Dady Habib ma yace"au wai ku kun yadda da abinda kidahumar yarinyar nan ta faɗa da wannan maƙaryacin?da sauri ya dawo kusa da Dady Mansur ya kamashi suka haɗe guri ɗaya dan ya kuma ɓatar musu da tunani,yana cewa Nine Mansur ko kunƙi ko kun so yana so kawai yayi amfani danine dan cimma burin sa!'bintu tace"wai ko dai ka zare ne Baba Habibu?ga Abu afili Amma kana kokarin maida shi rainin hankali,kasani cewa muryarka bazata taɓa ɓoye min ba,idan ka ɓoye fuska to muryarka ta tona ka,dan bata ɓoye ainahinka ba!'Abdallah kamar mutum mutumi haka ya zama a gurin saboda shi dama can bai iya irin wannan surutan ba,sai dai yayi aiki a aikace,da ba dan Dady jafar da ya dakatar dashiba da tuni ya daɗe da ɓalle hannu da ƙafar mutumin da yake kiran kansa da matsayin Mansur, wanda shi dama tun da ya ɗora idanunsa akansa yasan cewa ba Dady Mansur bane Habib ne,yana shirin bayyana hakan sai kuma Bint ta tiga shi bayyana wa,dariya Dady Habib yayi tare da cewa ku kiyayeni saboda yanzu a fadata kuke dan haka ina tabbatar muku da cewa duk wanda yazo gurin nan ba zai fita da ransa ba!'

Har dani mahaifiyarka ta faɗa tana ƙarasowa cikin gurin,kallo ya koma sama''' wan nan shi ake kira da Ali yaga Ali,shuru gurin ya dauka sai fuskokin da suke ɗauke da matsanan cin mamaki, cikin ƙarfin hali da tsananin mamaki Dady jafar yace"Hajjah me kika zo yi nan gurin,cikin nuna damuwa da tashin hankalin da take ciki tace"lokacin da Mansur ya shiga ɓangarena na fuskan ci da wani abu da yake ɓoyemin kuma daga dukkanin alamu abin ba ƙarami bane,shi yasa nayi tunanin biyosa,sai kuma nazo na kasa samun gurin tun ɗazu ina daga waje ina neman hanyar shigowa sai kuma yanzu katsam na ga kofar gurin ta bayyana!'ta ƙara sa maganar cikin rushewa da wani matsanan cin kuka, ta ci gaba da cewa Habibu ka zama ɗan kunama agareni mai harbin uwarsa,me yasa kayi duk wannan?me yasa ka kauce daga hanyar dana ɗoraka?ina ganin Mansur shine jarraba ta ashe kaine bansani ba,tabbas ka yaudaremu dan bani ka ɗai ka yaudaraba,har mahaifinka da sauran ƴan uwanka, mahaifinka yana ganin zaka maye masa gurbin ɗan uwanka da yarasa amma ashe abun ba haka yake ba!'ta faɗa tana durƙushewa a gurin cikin kukan fitar haiyaci,kama daga kan Fatima Bintu har zuwa kan Dady jafar da Alhaji Rufa'i da Mansur saida suka kusa zubdawa Hajjah hawayen tausayi, Abdallah ne dai ba kasafai ake gane masa ba indai damuwa ba akan Bintu ko mahaifinsa ba ne,dan haka bazaka gane kallon da yakewa Hajjo ba,

Cikin tausayawa ta tsakanin ɗa da uwa, Dady Mansur yace"dan Allah Hajjah ki daina kukan nan bana son kina tada hankalin ki!'mansur dole ne na tada hankalina ya za ayi ace duk tsawon shekarun nan da mukayi zuciyoyin mu cikin kewar Abubakar ashe wai yana tare damu bamu sani ba,ya haɗu da sharrin ɗan uwa, ko duk akan me yayi masa hakan oho,har kuma ya dinga ikirarin kashe dansa da surukarsa!'me kake nema a wajen sa haka da yafi girman zumuncin ku?ta faɗa tana kafe Dady Habib da idanun ta wanda sukayi jajir saboda kuka,bai ce mata komai ba sai kawar da idanun sa da yayi ya mayar kan Dady Abubakar da yayi sakato yana kallon abun al'ajabi,yace"to tunda duk kunyar da Nine Habib naji amma fa bazan taɓa nadama akan abinda na aikataba,kuma bazan taɓa saurarawa akan abinda nake da burin aikatawa ba,dan haka aɗaure kuke anan zan iya yin komai ba tare da kun hanani ba,ya cigaba da kallon Dady Abubakar yana cewa ABUBAKAR ƴan fansa sun ƙaru dan haka inaso ka zaɓa, ko ka faɗa min inda dimon yake ko na kashe duk mutanen dake zagaye da kai!'zaro idanu Hajjah tayi cike da mamakin ɗan nata,tana cewa Habibu dama shu'u mancin ka ya kai haka? to Ni kuma ina tabbatar maka da cewa bazan bari ka aikata mugun nufi akan ƴan uwanka ba!'tana gama faɗin haka ta nufi gurin da Dady Abubakar yake zaune akan wheel chair,kama wa tayi tare da fara turawa,ganin haka yasa da sauri Abdallah yace"ki barshi kawai Hajjah zamu san abunyi!'Hajjah tace"bazan bari ba Abdallah ku kuna da karfin da zaku iya ƙwatar kanku kubari na tafi da Abubakar!'zai kuma magana,Dady jafar ya girgiza masa kai,hakan ne yasa ya dakata daga abinda yake son faɗa,Dady Habib yace"kema bazan bari ki fita dashi ba,bare kuma su!'Hajja bata saurare shi ba ta tunkari ƙofa gadan gadan,Dady Mansur kuma ganin abinda yaran Habib suke shirin aikatawa na ƙoƙarin isa isa inda Hajjah take, yasa ya shammace su yayi wata hanya inda makun nan gidan suke take ya kashe duk fitulun gidan,kafin wani lokaci gurin ya ɗin ke da wani irin duhu mai tsanani,cikin ruɗewa da tashin hankali Dady Habib yake bawa yaransa umarnin kar su sake su bar wani ya fita daga gurin,sai dai kafin su aikata hakan tuni Hajja ta daɗe da ficewa da Abubakar, da ke ba ita kadai bace shi yasa,saka shi amota bai jasu lokaciba sukayi gaba dashi ita da yaranta,zuciyar ta cike da farin cikin nasarar dake tasamun rayuwarta,tana ganin tunda tayi nasarar samun Abubakar to bazata gaza wajen shirya yadda mutuwar sa zata kasance ba,bayan ta samu abinda take nema kenan..
Chapter 96 · 0% Book details