← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 120

Sashe 91

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Samuyal yace"wallahi Oga tun da muka dawo taƙi yin magana daga ƙarshe ma sai ta yi suman da muka kasa gane kanta,tun jiya muke sheƙa mata ruwa amma taƙi farfaɗowa,gashi kuma tana numfashi da'a lama dai ba mutuwa tayi ba!'Safwan ne ya ɗora da bawa Abdallah labarin abinda ya faru dasu ajiya wajen tahowa da Abigirl ɗin,shuru Abdallah yayi tare da tsurawa fuskar Abigirl ɗin idanu,ɗan jin jina kansa yayi kana ya fita daga ɗakin,ɗakin Saiyyid ya shiga yaja kujera ya zauna yana fuskantar Sayyid ɗin,cikin matuƙar kaushin murya Abdallah ya shiga korawa Sayyid gargaɗi yace"wallahi Sayyid idan ka sake ka kalli inda nake Acikin estate to zakayi nadama balle kuma ka ambaci sunana,kuma bawai ina maka gargaɗi dan ina jin tsoro bane a'a sai dan kawai inason kammala aikina lafiya,zan mai dakai gidan ku amma idan kana sha'awar cigaba da zaman rashin ƴanci to ka gwada yin abinda bana so!'daga haka ya kira Daniyal tare da bashi umarnin ya ɗauki Sayyid ya maida shi ESTATE kar kuma ya bari aganshi yasan inda zai ajiye Sayyid ɗin, Daniyal ya amsa cike da girmamawa kana ya juya ya fita daga ɗakin,Yahya ya kirawo dan ya mayar dashi estate,

Hajiya zulaiha kuka take nasamun rangwamen abinda ke damun zuciyar ta,jin wannan al'amari take kamar almara wai yau Alhaji Baba da kansa ya tara mutane dan sanar musu zai sa afara neman ABUBAKAR,tabbas ta daɗe tana jiran wannan rana me ɗin bin tarihi,hakanan kuma take jin wani farin ciki tun bayan gobarar dakin can,wanda ta rasa dalilin haka, Rahima da bata jima da dawowa daga can egift wajen yayan ta ba,ta matso kusa da mahaifiyar tata,cikin tausayi irin na ƴa ga uwa tace"Ammi yauma dai har da kuka kuma duk da kince kar na kuma magana akan damuwar ki!'da sauri Ammi ta jawo ta jikin ta,tana cewa yau insha Allah zan baki labarin mahaifin ki da ɗan uwanki, alokuta da dama inason yin magana amma sai hakan ya gagara ban san meye dalilin ba, amma yanzu kamar wadda aka cirewa wata ƙaya daga cikin maƙogaro haka nake ji,amma ina fatan hakan ya zama silace ta warware mana dukkan matsalolin mu!'kuka Rahima take yi sosai kamar zata shiɗe bayan ta gama jin labarin mahaifinta da dannuwanta wanda ita a tunanin ta mahaifinta ya mutu,ta kanƙame Ammin kamar zata koma cikin ta,wayyo Ammi na dama wannan baƙar damuwar kike shaƙa shekara da shekaru ke kaɗai ban sani ba,dan Allah Ammi na ki yafe min gurguwar fahimtar da nayi miki Abaya,duk rashin sani ne wanda yafi dare duhu!'ta ƙare maganar cikin ƙara ƙanƙame Ammin,shafa kanta Ammi take cikin san lallashin ta,tace"ba laifinki bane nima kuma ba laifina bane,wan nan abinda ya sameni ba Ni kaɗai bace duk ahlin ALHAJI BALARABE ne,kamar anrufe baki da idanuwan mu babu wanda yake iya furta sunan mahaifinki acikin gidan nan,sai dai kabar damuwar ka cikin ranka tayi ta kassara lafiyar ka,dan haka yanzu godiya zamuyiwa Allah da ya bamu ikon tunawa dasu wanda hakan ma wata babbar nasara ce,a garemu,kinga zamuyi addu'a da bakunan mu mu roki Allah ya baiyana mana su aduk inda suke.

Ta gumi ta zuba ɗan duk sai taji ranta babu daɗi akan abinda Inno da Hajiya Babba sukayi ɗazu a falon Alhaji Baba,ko me hakan yake nufi kuma?dama da akwai wannan kishin tsakanin su?duk sai taji ta tsargu to me Hajiya Babba take shirin faɗa Inno ta tareta?miƙewa tayi tsaye tana cewa tabbas bazan iya haƙuri ba sai na je nasamu inno da maganar dan Ni ban iya ƙunbiya ƙunbiya da munafunci ba dan haka bazan bari ayi min ba,ta zari mayafinta tayi waje dan zuwa sashen Inno,

Daniyal yayi nasarar kawo Sayyid gida ba tare da kowa ya ganshi ba,daƙyar Sayyid ya iya ta kawa zuwa cikin estate ɗin saboda daure war da ƙafafunsa sukayi wajen zama guri ɗaya,yana shiga get ɗin farko ya cikaro da Dady Habib zai fita amota,ɗaga masa hannu yayi kasan cewar baƙin glace ne yasa shi Sayyid ɗin bai gano Dady Habib ɗin ba ya dai gane motar sa kawai,cikin sauri Dady Habib ya taka burki tare da fitowa daga cikin motar jikin sa har rawa yake saboda farin cikin ganin Sayyid, rungumo shi yayi yana duba jikin Sayyid ɗin tare da cewa Sayyidi ina fata dai kana lafiya babu abinda ya same ka suwaye suka sace ka?duk ya jero masa tambayoyin ajere, Sayyid yace"Dady nima ban san su ba,muje ciki a gajiye nake sosai!'cikin rawar jiki Dady Habib ya saka shi cikin motar kana ya zagaya ya shiga yaja suka nufi cikin estate ɗin.

Wata irin zabura Anty Nafisa tayi yayin da taci karo da hotan Bintu a kan scring ɗin wayar,jikinta da zuciyar ta babu abinda sukeyi sai rawa,zubawa hotan ido tayi tana kallon wata fuska acikin fuskar Bintu,shin WACECE BINTU,me tazo yi ESTATE kuma meye haɗin ta da waɗan nan mutanen da Umar yake zuwa wajen su, su ɗin su waye?wai mai ke shirin faruwa da Nine?yana ke ganin fuskar Bintu na juye min da wata fuska da na sani?me yasa tun farko ban fara buncikar yarinyar nan ba na yadda da ita haka?me yashiga kaina alokacin?cikin sauri ta ta danna kira,ana ɗagawa tace"cakewa kayi gaggawar buncikomin asalin mutanen da suke zaune agidan nan, da matsayin su agurin Umar bana son ɓata lokaci kamar yadda katuran hotan nan a yau shima ina so wannan ayau ka bincikon abin da nake da bukatar sani!'yace"angama Hajiya karki damu zaki samu yadda kike so!'ajiye wayar tayi tana ci gaba da kaiwa da kawowa aɗakin dan batajin yau zata iya zama batare da taji sakamakon binciken da tasa ayi mata ba.

Dady jafar ya dubi Dady Mansur cikin mamakin sa yace"dama wannan shine kiran da kayi min amma kuma me yasa kake son kasan inda Abdallah da Bintu suke,meye damuwarka da hakan, kuma me zakayi musu?Dady Mansur yace"Jafar bazaka ne komai ba yanzu amma dan Allah inaso ka taimaka kagayamin inda yake saboda ina buƙatar ganin su da gaggawa!'wani mugun kallo Dady jafar ya watsa masa kana yace"amma Mansur baka ji daɗi ba Nima ka biyoni ne dan kayi min yaudarar da kasaba yiwa mutanen gidan ku?to bari kaji na gaya maka Mansur tuntuni anyi walƙiya na ganka kuma sauran mutane ma zasu ganka insha Allah sai asirinka ya tonu a idon duniya,kuma zaka girbi abinda kake shukawa,saboda ɗan zaki ya riga ya girma shine zai cinye dukkanin mugayen kananun namun daji!'yayi wani irin murmushin takaici me ciwo ya cigaba da cewa Allah ya riga ya nufi zakaran da cara babu yadda zakuyi dashi sai dai kallo!'shuru Dady Mansur yayi saboda ayanzu dai bashi da ta cewa duk bakin sa amma yanzu ya baya iya maida magana,dan haka ne bai tankawa Dady jafar ba har yayi ya gama ya barshi awajen,

Dady Mansur yayi mamaki lokacin da ya koma gida ya samu Sayyid tsaf dashi duk gida ya ɗauka da barkar dawowar sa, sai zuwa sashen Dady mansur akeyi barka kamar wanda akayi wata haihuwa,cike da farin ciki ya rungume ɗan nasa duk da halin da zuciyar sa take ciki a yanzu na rashin walwala da tsananin damuwa amma hakan bai hana shi jin dadin ganin ɗan nasa ba,duk wanda yayiwa Sayyid tambayar waye suka sace shi,to amsar dai ɗaya ce,shima bai sani ba,dole kowa ya haƙora da tambayar ya kama sabgogin sa.

Kamar daga sama ta samu wayar uwar gidan ta, Cikin rawar jiki Dije ta ɗaga, daga can ɓangaren matar tace"Dije ya batun alƙawarin mu?ina fata dai zan samu kyakkyawan labari?cikin farin ciki Dije tace",tabbas kin kira lokacin da ya dace dan kuwa cike nake da ɗokin haduwa dake dan sanar miki abinda zai matuƙar faranta zuciyar ki!'wata dariya ta saka daga can kana tace"shi yasa nake matuƙar ji dake Dije, kuma na koma inuwa nayi zamana hankalina kwance saboda nasan ina dake,yanzu yamma tayi kuma kinga akwai al'amuran da ake dan gabatar wa a cikin gidan dan haka gobe kiyi sammakon fita zan tura miki da wajen da zamu haɗu bayan fitarki!'Dije tace"to ranki shi daɗe,Allah ya nuna mana goben da rai da lafiya,tana kashe wayar tayi wani murmushi wanda yake baiyana ƙwarin gwiwar ta tare da cewa ko ke wacece taki ta kusa ƙarewa gobe i War haka kina nan kina zaman makokin kanki da kanki.

Tun daga farkon shigowar sa gidan yasan cewa komai yana tafiya yadda suka barshi,ga wan can al amarin ga kuma dawowar Sayyid,kai tsaye ya wuce part ɗinsa dan komai dake faruwa ba baƙon sa bane,yana shiga duk sai yaji falon yayi masa faɗi har cikin jinin sa yake jin damuwar ta da kuma kewar ta,ga kuma uwa uba tausayin ta dake neman zauta zuciyar sa,cikin sanyin jiki ya gabatar da al'amuran sa na yau da kullum,wayar sa ce tayi ringin, har zai basar da kiran sai kuma yaga Dady jafar dan haka ya daga tare da yin sallama,ba tare da ya saurari gaisuwar da Abdallah yake masa ba, yace"Abdallah tun tuni na gaya maka ka saka idanu akan Mansur amma ka banzar da maganata,to yanzu umarni nake baka kasa ka ido sosai akan sa dan ina matukar zargin sa,nan ya bashi labarin yadda sukayi ɗazu da yadda ya damu sai yasan inda suka je shida Bintu,numfashi Abdallah ya fesar kana yace"Dady karka damu zan kula da komai!'kafin ya sauke wayar daga kunnen sa wani kiran ya shigo ba tare da ya duba ba ya ɗaga, dan azaton sa ko Dady jafar ɗin ne ya sake kira.

Sannu ɗan zaki to idan kana buƙatar zakanyar ka,ka taho da zakin ubanka ka fanshi zakanyar matarka,idan kuma baka buƙatar ta yanzu saina fasa kanta da bakin bindiga, zanga irin naka halaccin idan ka gama tunani zan kuma kira dan yi maka sauran bayani inda zaka same mu kuma muddin kasarwa na jami an tsaro to wallahi ina tabbatar maka da cewa sai na kashe matar ka koda za akamani, na barka lafiya kayi tunani mai kyau matar ka ko mahaifinka?daga haka ƙit aka datse kiran.

Fatimah Y Adam✍🏽
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

```Page 52 ```
Chapter 91 · 0% Book details