← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 120

Sashe 29

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari sai ga Taufiƙa ta kuma biyo Bintu kiching Bintu tana ganinta ta haɗa rai tana gunguni, Taufiƙa ta zuba mata ido kana cikin san fahimtar abinda Bintun take faɗi tace" wani abu kike cewa bintu,?Bintu kuwa kai tsaye tace" Gaskiya Anty Taufiƙa bazan kuma baki girkin oga Abdallah ba jiya baki ga abinda yayi min ba,kuma dama kinsan baki iya ba kikace sai na baki kinyi kalan dama so kike kijamin masifar wannan yayan naku!'taƙarasa maganar cike da baƙin ciki kamar yanzu akayi abin tana tuna yadda yasa ta cinye Abincin nan mara daɗin ɗanɗano, Taufiƙa ta haɗe rai tare da cewa ke karfa kiga na sake maki ki rainani wannan abincin ne baiyi daɗi ba to ko yanzu nayi niya sai na karɓa nayi yadda nakeso, dama ai haka nakeso ya sauke fushin kanki! ta faɗa tana ɗage mata gira ɗaya da wani ɗan munafukin murmushi akan fuskarta,shiru Bintu tayi tana haɗiyar miyan takaici,ba ita taji dai dai ba sai da taga Taufiƙa ta bar kiching ɗin batare da tanemi ta bata girkin ba.

Lokacin da ta kai masa yana zaune A falon cikin ƙayatacciyar shigarshi ta alfarma,ɗan jim tayi sai kuma ta wuce a saɗaɗe ta jera haka tayi har ta gama, tana shirin fita taji tattausar muryarsa yace" zo nan!' dawo wa tayi ta tsaya tana murza yatsun hannunta,tashi yayi ya nufi dining table ɗin ya zauna,bazakizo ba ya faɗa cikin da kakkiyar muryarshi ta zaratan maza mara sa son raini,ƙarasowa tayi batare data dubeshi ba tace"gani!' banza yayi mata ya cigaba da taɓa wayarshi kuma bai taɓa abincin ba, gajiya tayi da kanta ta fara savin ɗin sa ,wani haɗe rai ya kuma yi ya fuskanci yarinyar nan bata da kunya wato ta gane abinda yake nufi amma tayi mursisi nufinta sai ya gaya mata kenan,

Sai da ya kusa cinye chips É—in da ta zuba masa kana yayi mata nuni da ta wuce ta bashi guri,fita tayi tana mita cikin ranta.

Alhaji Farouk ya dubi Anty Nafisa yace"inaso zan shiga wajen inno tunda na dawo daga tafiyar nan banje na dubasu ba! hakanan Anty Nafisa ta dinga jin faɗuwar gaba, shin meyasa take ta ƙoƙarin hana Farouk zuwa ɓangaren inno? tunda ya dawo take ta yi masa dabara wanda tasan bawai dabarar tace tayi mata aiki ba kawai dai shima yana daga cikin waɗan da suke da yawan sabgogi shine dalili sai dai kuma ita kanta bata san dalilin ta nayin haka ba,muryar sace ta katse mata zan can zucin da takeyi, yace" bari naje daga nan zan fita sai na dawo!' kasa magana tayi har ya fita daga ɗakin,jugum tayi ta rasa meke damunta sam ita fa bawai ta daina jin fargaba bane kawai abinda take son cimmawane yasa ta daina yawan damuwa da lamarinta na baya,tashi tayi ta fara zaga ɗakin cike da san samarwa kanta mafitar damuwar dake cin zuciyarta.

Inno tarasa inda zata saka Dady Farouƙu saboda shi mutumne da bai fiye zama ba yana da yawan tafiye-tafiye idan ya tafi kuma yana daɗewa bai waiwayi gida ba, kuma haka baya rasa na saba da babban damuwar da ke cinye zuciyarsa,yaɗan jima suna taɓa hira da inno kafin yayi mata sallama ya wuce harkokinsa.

Farida ta dubi Siddiqa tace"Siddiqa baza mu tsaya mu dogara da shirin Sayyid ba kinsan halinsa ɗan ɗauka da ajewa ne kawai zamu fara ɗaukar fansa ne ba sai mun zauna jiran gawan shanu ba!' Hauwa'u tace" amma duk abinda zamu shirya kar mu sake su amna da Rahima su sani dan zasu iya ɓata mana shiri!'Taufiƙa tace" hakane nima kinga shirin mu yana karɓuwa ta ɓangarena amma shegiyar yariyar bana tunanin zata kuma bani girkin nan amma inta san wata ai bata san wata ba!'hauwa'u tana wani dogon numfashi kana cikin yanayin karaya tace" Ni dai inaga burina bazai taɓa cika ba wallahi tunda nake a duniya ban taɓa tunanin zanyiwa wata halitta son da nakewa yah Abdallah ba,Ina son shi son da baki bazai iya faɗa ba!' sai kuma kuka ya ƙwace mata sosai (har ji nayi kamar na tausaya mata) Taufiƙa rufe idanunta tayi tamkar mai bacci sai dai kuma ita kaɗai tasan yawan wutar dake bab baka cikin zuciyarta da ruhinta, Hauwa'u shirme takeyi sai dai ita baza ta taɓa bari Hauwa'u tasan irin tarin ƙaunar da takewa Oga Abdallah ba,sai dai taci alwashin bin duk wata hanya da tasan zata mallaka mata Abdallah,wannan alƙawarin tane zata ɗagawa Hauwa'u ƙafa na ɗan lokaci kafin tayi maganinta dan tanajin zata iya yin komai a kan soyayyar Abdallah,wannan kenan.

Cikin rawar jiki take karanta sakon Dijen wanda take sanar da ita cewa lallai tanaso ta kaucewa haɗuwa da Sayyid saboda Akwai abinda yake shirya mata kuma ita tasan wane Sayyid zai iya aikata komai akan biyan buƙatar zuciyarsa,Bintu ta ajiye wayar cikin zurfafa tunani akan abinda Sayyid ɗin yake shirin aikata mata,to wai meyasa sai ita? meyasa kowa ya kwaso ƙiyayyarsa da ɓakin halinsa sai kanta?me yasa suke san ganin bayanta? to ko sun gane ita wacece?girgiza kanta tayi tanajin waɗan nan basu ne A gabanta ba aikin dake gabanta ya fi sauran ƙananan ƙwarin nan.

Bayan kwana goma da faruwar wannan lamari,rana tsaka inno ta shiga cikiyar babbar sarkarta wadda kakasance tun ta aurenta, yau kwananta bakwai tana nema batare da tayi cikiya ba saboda tana san ta tabbatar da sahihancin nemanta batason tayi cikiyar kuma tazo ta ganta, shiyasa taƙiyin maganar sam sai yau da ta ga dai da gaske ɗauke sarƙar akayi tayi ɓatan dabo,gaba ɗaya ta kira jikokin nata da wanda suke kwana da wanda zuwa kawai sukeyi,dukkansu bata zare kowa ba ta Fara duban su Taufiƙa tace" bari na fara ta kanku saboda daku nake kwana nake tashi,shin babu wanda yaga sarkata da yari A cikin ku? ware ido sukayi har da su Rahima da tambayar bata zo kansuba,kafin kace wannan kowa ya shiga rantse rantse, Siddiqa tace"inno kicaje ɗakinmu mana, yanzu har ta kai da zaki iya tuhumar mu laifin sata mu jikokin ki da KIKASAN bamu rasa komai ba me kuka rage mu dashi dazamuyi miki sata satarma ta abinda mukasan yana da daraja da muhimmanci a gurinki, gaskiya inno baki mana adalci ba!' Sayyid yace" nina ma rasa abin cewa da wannan gagarumin sharri da tsohuwar nan take san manna mana! Inno tace" bazaku fahimci abinda nake nufi ba amma tabbas an kwana biyu da soma yi min ɗauke ɗauke bana son zargi da yawan tashin zance shiyasa bana kulawa da irin wannan,amma yanzu dole nayi magana tunda abin yayi girman da bai kamata na rufe bakina ba!'Farida tace" to inno tunda haka ne ai bamu ka ɗai ya kamata ki tuhuma ba ai naga da ragowar wa anda baki tattaro ba!Nabil yace" tabbas wannan haka yake dolene suma ragowar ki tuhumesu indai gaskiya za abi!' kafin inno tace" komai Taufiƙa ta nufi hanyar ɗakin Bintu,can saiga ta sun fito tare,Bintu sai da gabanta ya faɗi ganin yadda suka zuba mata ido ga kuma ran inno A matuƙar fusace dagani Lallai laifin da akayi mata babba ne,durƙusawa tayi gaban inno tace" inno gani lafiya kuwa!A hankali inno ta kawar da kanta gefe saboda tanajin kunyar ta dubi idon Bintu tayi mata cikiyar sarƙa,Nabil ne ya gyara zaman shi kana yace" Bintu inno ce ta taramu take mana cikiyar sarkarta da ɗan kunne,tajima tana dubawa amma bata gansuba duk ɓangaren nan!' Bintu ta dafe ƙirjinta cikin tashin hankali tace" wallahi ban gani ba!'Sayyid ya katse ta da cewa inno kinsan dai duk cikin mu babu wanda yake shiga ɗakinki ko? ta gyada kanta, kana ya ɗora da cewa' dan haka ki sauke zargin ki daga kanmu ki maida shi kan wanda yake shiga ɗakinki kullum babu fashi!'Hauwa'u tace" inno babu wani ɓoye-ɓoye kawai mu tashi yanzu mu duba ko ina na cikin gidan nan har ɗakinki sai mun kuma dubawa dan haka mu rarrabu Sayyid Ni da kai da Farida mu shiga ɗakin su Siddiqa Taufiƙa da Siddiqa da Bintu su shiga ɗakin inno kai kuma Nabil da Rahima da amna ku shiga ɗakin Bintu kowa ya tabbata ya duba da kyau ke kuma inno ki zauna anan ki jira mu zamu nemo miki sarƙarki yan zunnan...

ana wata ga wata ki a ina za aga sarƙar inno?

Comment.....

Share.....
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

```Page 22 ```

Kafin kace meye sun bazama dukkanin dakunan dubawa suke sosai, sai da suka buncika ko ina basu gani ba,su Bintu ne suka fara fitowa daga ɗakin su Taufiƙa Hauwa'u tana cewa inno ɗakin su Taufi dai babu sarƙa!'kan ta gama rufe bakin ta, su Siddiqa suma sun fito daga ɗakin inno, Taufiƙa tace" wallahi inno babu inda bamu duba ba A ɗakinki bamu ganta ba!' shiru sukayi lokacin da suka ga su Rahima sun fito daga ɗakin Bintu jikinsu A matuƙar sanyaye,gaba ɗaya sukabi hannun Amna da kallo A yayin da take zube sarƙar a kan Centre table,waro ido sukayi gaba ɗaya A firgice, yayin da har haɗa baki suke wajen faɗin A ina kuka ganta? Nabil yayi nuni da Inda Bintu take tsaye,batare da ta fahimci abinda suke nufi ba, zuciyarta ɗaya bata taɓa kawo wai za aga sarƙa A ɗakinta ba tunda tasan bata ɗauka ba.
Chapter 29 · 0% Book details