Sashe 98
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin su A kofar gidan Hajjo ba ƙaramin farin ciki ya saka ta ba,sai dai kuma abin mamakin da suka tarar gidan babu kowa gashi abuɗe sakayoshi kawai akayi,cikin fargabar abinda zasu shiga su tarar suka shiga cikin gidan,a kideme Bintu ta kalli Abdallah tare da cewa to ina suka je dukan su haka?ɗakin Hajjo ta faɗa da gudu anan ta samu wayarta a yashe ƙasan ɗakin durƙusawa tayi ta ɗauka,cikin rawar jiki ta kunnata,tayi sa a kuwa da ragowar caji tunda mutuwa tayi,lambar da Anty Asma'u ta saka mata ita ta kira,zuciyar ta kuwa sai bugawa take saboda tsananin fargaba,ɗan matsowa yayi kusa da ita tare da kamata ganin yadda ƙafafun ta suke rawa, yace"Bint ki nutsu Mana me yasa haka da ruɗewa,tun kafin kiji dalilin barin su GIDAN!'kar ɓar wayar yayi yasaka ta a amsa kuwa,daidai lokacin da Anty Asma'u ta rangaɗa sallama,wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya suka saki atare kamar yadda suka saba,kana cikin nutsuwar sa ta kullum yace"Anty Asma'u mun dawo kuma bakwa nan!'da sauri tace"kai da waye?ina Batula hankalin mu ba akwance yake ba, Allah yasa kar kace mun ba a sameta ba? cikin ƙosawa da yawan maganar yace"tare da ita muke!'miƙawa Bintu wayar yayi ta karba da sauri tare da cewa'Anty Asma'u gani kuna ina ku?sai kuma taji Muryar Hajjo har da kuka tana cewa Alhamdulillah Allah abin godiya, Abdallah Allah yayi maka albarka tabbas kacika gwarzo kuma jarumi Allah Ubangiji ya taya maka ya dafa dukkan al'amuran ku,ya cigaba da kareku daga sharrin maƙiya da dukkan abin ƙi!'amin Hajjo me yafaru ne wai?'ya faɗa yana matsawa jikin Bintu don yaji maganar sosai,nan dai Hajjo ta bashi labarin abin da ya faru gaba ɗaya har yadda sukayi da yaran Anty Nafisa da Abba Umar,hamdala yayi,yana sakin murmushin farin ciki da nasarar da suke samu adukkan abinda suka tunkara, lallai Allah mai ƙudura ne,shi kaɗai yasan ta hanyar da zai kare bayin sa wanda suke tare da shi,cikin farin cikin da ya kasa ɓoyuwa akan fuskarsa ya da ɗa rungumo Bint jikin sa yana cewa to Hajjo Allah abin godiya ne ko da yaushe agaremu Allah ya ƙara wa Annabi wasila da fabila,gaba ɗaya suka amsa da Amin,Bintu tace"Ni kam ma Hajjo dama kukan gulma kikeyi bana rashina bane,tun da gashi har yanzu kin kasa yimin magana!'ta faɗa tana share hawayen da ba wahalar zubo mata sukeyi ba,dariya Hajjo tayi cike da madaukakin farin ciki,tace"wace ni naƙi kula ƴar lelena,mijin nawa ne dole na tsaya na yabeshi dan ya cancanta!'ɗan kallon Abdallah tayi wanda yake ta zuba mata wani munafukin murmushi da kallon da yake haifar mata da mutuwar jiki,abinda ya shiga yi matane yasa ta fara yiwa Hajjo in ina, tace"haj,, haj, Hajjo to zamu taho inda kuke kiyi mana kwatan ce!'karɓe wayar yayi yana cewa Hajjo ba yanzu ba kin san dai abinda nake shiryawa,dan haka sai mun sake waya!'daga haka ya kashe wayar, yana yiwa Bintu sigina A lokaci ɗaya kuma yana cigaba da yimata tafiyar tsutsa a gadon bayanta,kanƙame shi tayi jikin ta na wani irin rawa,cikin rawar murya tace"Ni Ni dai mu tafi gida!'cikin hura mata iska a kunne yace"nan A daji muke?a bazata taji wani irin sanyi cikin kunnen ta, ƙafin ta dawo hayyacin ta, Abdallah ya shiga tsotse kunnenta loko da saƙo,wani irin kyarma jikin Bintu yake yi, wannan abun da Abdallah yake mata wani baƙon al al'amari ne a gareta wanda take, taji duk wata tsiga dake jikinta tana miƙewa cikin biyayya da karban saƙonnin da Oga Abdallah yake basu,bata gama kiɗimewa ba sai da taji hannuwan Abdallah biyu akan nn,ta wanda yasa ta kusa shiɗewa,
Ringin ɗin da wayar ta tayi shi ya dawo dasu hayyacin su duk da cewa Abdallah yaƙi sakin ta,ganin lambar Dije ya sa ta ɗauki wayar da sauri,ajiyar zuciyar da Dije ta saukar shi ya shiga kunnuwan ta da Abdallah yayi musu wankin babban bargo da miyansa,Dije tace"Bintu ina kika shiga haka kwana biyu nayi kiranki har na fidda rai da samun ki!'Bintu tace"Dije na shiga matsala ne amma yanzu komai yayi daidai,ya ake ciki kuwa?Dije tace"sakon da nake ta son baki ke nan,amma yanzu a gurguje abu ɗaya mafi muhimmanci zan gaya miki sauran bayanin sai mun haɗu!'Bintu tace"ina jinki!'Dije ta ɗan ja ajiyar numfashi kana tace"kin san wacece wannan matar Bintu?cikin fargaba, Bintu tace"wallahi ban sani ba Mama Dije!'Dije tace"abin da matukar mamaki da ɗaure kai,ba kowa bace wannan shu'umar matar ba sai Hajjah matar ALHAJI BALARABE ta biyu,kuma uwa ga ALHAJI Mansur da Alhaji Habibu.......
ÆŠit É—it É—it .... FATIMAH Y ADAMâœðŸ½
More Comment
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœðŸ¼*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ðŸ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 55 ```
Wayar ta saki, ta faɗa ƙasa,ita kuma ta koma jikin Abdallah saboda jirin da ke neman kayar da ita,riƙe ta yayi,kana cikin taushin murya yace"Bint calm down Mana me yasa bakya ɗaukar abu da sauƙi? cikin kukan da yake tasan ƙwace mata,tace"ya Abdallah ta tafi da Dady fa,kuma kasan fa ita ma tana son ta ɗauki dimon ɗin nan,dan haka zata iya cutar da Dady!'A hankali ya shiga jijjiga ta kamar wata ƙaramar jaririya,sai da yaga ta ɗan nutsu kana ya kai bakinsa saitin kunnen ta yayi mata raɗa, wanda hakan yasa naga ta saki wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya tare da kuma ƙankameshi har da guzurin wani sassanyan murmushi,shima murmushin yayi tare da kama hannun ta suka fita daga gidan,kullewa sukayi kana suka dau hanyar komawa ESTATE,
Cike da farin ciki suka isa gidan da ta ajiye su Laila,shi dai Dady Abubakar yana kallon ikon Allah ne kawai amma baice komai ba, tun daga yadda suka É—auke hanyar shiga cikin gari yasan cewa akwai wata manufar,
Fito dashi sukayi suka tura shi har zuwa cikin dakin da aka ajiye fafi,daga nan Hajjo ta yi musu kashedi da jan kunne akan su kula su kuma kiyeye kar suyi saƙen da zata rasa Abubakar akaro na biyu akan sakacinsu, dan akan wannan bazata taɓa raga musu ba, saboda samun Abubakar shine cikar burinta,da wannan kashedi ta tafi ta barsu da niyar sai gobe zata dawo saboda yanzu dare ya raba kuma bata son shirinta ya wargaje na yadda zatasanar dasu kufcewar ABUBAKAR daga hannun ta.
Kai tsaye falon inno suka nufa,wani abun tausayin inno suka tarar tare da Hajiya Babba daga dukkan alamu ko da rintse basu runtsaba,gaba ɗaya hankalin su atashe yake,da gudu Bintu ta ƙarasa ta zube jikin inno kana ta koma jikin Hajiya Babba wani shaukin kaunarsu ne ke da ɗa kwarara cikin zuciyarta,inno ta dubi Abdallah dake zama kusa da ita cikin damuwa da kulawa tace"Abdallah ina kuka shiga kwana biyu hankalin mu duk ya tashi? tun ranar da kayi min waya ban kuma jin duriyarku ba!'Hajiya Babba ma saka mashi idanu tayi suna jiran amsar da zai basu, jingina yayi da jikin kujerar da yake zaune tare da lumshe gajiyayyun idanun sa,kana A hankali yace"inno na gaya miki aiki ne ya fitar damu shine na tafi da ita!'kallon da suka ci gaba da yi masa ne ya tabbatar masa da cewa basu gamsu da abinda ya gaya musu ba,hakanne ya sa shi mikewa cikin nuna gajiyar dake tattare dashi ya nufi falon sa,da kallo suka bishi har sai da ya shige kana suka dawo da duban su kan Bintu dake kwance jikin Hajiya Babba idanun ta alumshe da alamun dai itama da gajiya da kuma bacci atare da ita, a hankali Hajiya Babba ta shafa kanta tare da cewa Bintu me ya same ki ne haka dubeki kamar wadda aka tsamo cikin shara duk kayanki sunyi datti ga idanunki sun faɗa,wai ina kuka je ne haka da kuke ɓoye mana?kallon jikin ta tashigayi wanda ta riga tasan ya Abdallah bai tsammaci zaiga su Inno a nan ba da tabbas bazasu shigo a haka ba,murza idanunta ta shigayi ta rasa abin cewa,kallon juna su Inno sukayi kana inno ta kuma dawo da dubanta kan Bintu tace"Bintu na nasan da akwai abinda kuke ɓoye mana kawai dai kuna tsoran faɗa ne saboda sirrin junan kune!'cikin sauri Bintu tace"a'a inno kar zuciyar ki ta raya miki wani abu mara kyau,sirrin mu sirrin kune,koda babu dangantaka tsakanin mu zan iya fada muku sirrina!''kallon da taga suna zurfafawa akan ta ne yayi saurin ankarar da ita katoɓarar da tayi,dan haka cikin dabara ta sauya zancen da cewa,inno wallahi kun riga kun zama dangina kuma iyayena shi yasa har nake manta koni wace a gurinku ji nakeyi tamkar nima daga tsatsan ku na fito dan haka babu wani sirrina da bazan iya sanar daku ba,amma kuyi haƙuri ku bamu lokaci!'ta ƙarasa faɗa cikin marairaice fuska,Hajiya Babba tace"shike nan tashi kije kiyi wanka ki kwanta!'tace to tare da tashi sai da tabi kowaccen su da runguma ta tsantsan ƙauna da farin cikin basu zamo daga cikin taɓaɓbuba,kallo suka bita dashi ganin ta nufi falon Abdallah hankali kwance ba tare da tasan suna kallon nata ba,sai da taje bakin ƙofa kana ta juyo tare da huro musu sumbata,san nan ta shigewar ta tana kuma yi musu sai sa da safe, murmushi sukayi kana inno tace"Hajiya Babba ki wuce na rakaki dakin Alhaji!'Hajiya Babba tace"yi kwanciyar ki ba sai kin raka Ni ba abinda ta kofar falonki kawai zan shige!'inno tace"to shike nan Allah ya tashe mu lafiya!'amin Hajiya Babba ta amsa tana shiga falon Alhaji ta falon inno, sai dai dukka su zuciyoyin su cike take da damuwa akan al'amura masu yawa, dake wakana acikin gidan kwana biyu.