← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 120

Sashe 94

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Innalillahi'wa'inna ialaihi raji'un,t faɗa tana da ɗa murza idanun ta cike da mamakin wadda ta gani,ba ƙaramin shock ta shiga ba ganin matar dake tsaye gaban ta,cikin tsananin ruɗani da mamaki gami da tashin hankali take nunata da yatsa bakinta yana rawa ta gaza furta abinda take son furtawa,zuciyar ta babu abinda take sai ta riyo mata irin karamci da Mutuncin matar,kai ita Dije ma zata iya cewa duk gidan Alhaji Baba babu macen da tafi kirki da mutunci a idanun ta kamar wan nan dake tsaye agaban ta,ta tuna lokacin da tazo gidan amatsayin mai neman masauki,itace wadda ta fara karbar ta,tare da bata masauki kafin daga baya ta haɗa ta da ɓangaren Dady Mansur,to hakan yana nufin duk shiri ne?dama da manufa tayi mata hakan?lallai kuwa idan haka ne wannan mata ta cika cikakkiyar makira kuma shu'ma,zilwaja haini,katse Dije tayi da cewa,kinyi mamaki ko Dije?to amma kuma idan kika bi ta wani fuskar ai ba wani abun mamaki bane,yanzu dai duk ba wannan ba abinda nake so dake shine ki tashi ki tattara yaranki da komatsanki zan baki kuɗin aikin ki,ki bar garin Abuja gabaki daya kiyi nesa da ita,bana buƙatar ganin ki acikin garin nan,saboda hakan shine rufuwar asirina!'Dije bata ce komai ba, sai miƙewa da tayi ta haɗa hannuwan ƴaƴan ta suka fara tafiya,matar tace"Dije baki ce komaiba me shurun ki yake nufi?Dije ta ɗan dakata ba tare da ta juyo ba tace"babu abinda shuru na ke nufi sai Alkhairi,kuma bana buƙatar komai daga gareki tunda kin riga kin cika alƙawarin da kika yi min haka ma na gode!'daga haka ta ja yaran ta suka yi waje, zuciyarta cike da baƙin cikin rashin Bintu ko Abdallah a wajen,gashi yanzu bata san yadda za ayi ta haɗu dasu har ta fayyace musu abin da ke faruwa ba.

Wata mashahuriyar dariya ta fito tanayi wadda ke nuni da tsananin farin cikin da take ciki ji take kamar ta samu Abubakar ta gama,gashi kuma ta toshe duk wata hanya da zata iya tona asirin ta,dariyar tace ta tsaya lokacin da tashiga dakin Laila,zubawa ɗakin Ido tayi cike da razani da tunanin inda Laila ta shiga,da sauri ta buɗe ƙofar toilet ɗin dake ɗakin, dubawa ta shiga yi loko da sako,amma babu Laila babu labarinta,cikin wani azababban sauri ta fito tana ƙwalawa masu tsaron su kira,cikin rawar jiki duk suka nufota yayin da ita kuma ta waɗa dakin da fafi yake ciki,ga tsananin mamakinta shi ma baya nan, babu komai aɗakin sai tarkacen kwanikan da ake basu abinci,ihu ta saka tare da zunduma musu wata iriyar gunndume miyar ashar,cikin tsawa da yanayin hauka hauka na zaucewar tunani take cewa,me kuke yi suka gudu? kuna ina aka sace su?ɗaya daga cikin sune yace"ai Hajiya lokacin da kuka shigo gidan nan daga dakin su nake na kai musu abinci!'babban cikin su ma yace"tabbas Hajiya lokacin da kuka zo gidan nan ajiyar ki suna nan,sai dai idan bayan shigar mu dakin nan ne suka gudu!'zubewa tayi agurin cikin ɗora hannu aka take cewa shike nan asirina ya tonu,ya akayi na bari haka ta faru?ya akayi akasan da gidan nan duk takatsan tsan ɗin da nakeyi?dungu yace"Hajiya anya kuwa matar nan tana da gaskiya?anya bata haɗa miki gadar zare ba?wata irin zabura tayi cikin ihu tace"ku bi Dije ku samo min ita duk inda take,ku kawo min ita nan!'ta faɗa tana sharce gumin da yake ta wanke mata fuska,da gudu suka bazama neman Dije.

To ya akayi Dije ta shammace ta haka?tabbas babu wanda ya isa yazo gidan nan sai wanda ya biyo bayan su,to waye ya biyo bayan su?wata zuciyar tace mata Dije ta riga ta shirya komai kafin haɗuwar ku,tabbas wannan shirin dagaDije ne makircin daga Dije ne,dama sun shirya yin komai ita da Bintu,to ya akayi BINTU tasan cewar iyayen ta suna wajenta?a kwai fa matukar ɗaurewar kai a cikin wannan al'amari,bata ga ta zama a wajen nan ba,dole ta tafi estate ta kasa ta tsare taga daga inda al'amarin ya ɓullo.

Dije tana fita ta ɗauki hanya, sauri suke tamkar zasu tashi sama,saida sukayi dan nisa daga gidan kana suka tsaya maida numfashin gajiya,kamar daga sama suka ga mota A gaban su,kafin ta gama mamakin yadda akai mota tazo nan,taji Muryar Abdallah yana cewa yi sauri Mama Dije ku shigo!'Dije bata tsaya sanya ba da a zama ta tura yaran ta cikin motar kusa da fafi,itama ta shiga,da wani azabar gudu Abdallah yaja motar kafin ƙiftawar ido sun bace sai ƙurar motar sa,a daidai lokacin kuma yaran Hajiya suka ƙaraso gurin basu ga mota ba sai ƙurar mota,a take kuwa zargin su ya tabbata,juyawa sukayi jiki a san yaye,dan sun san zasu sha bala'i gurin Hajiya.

Wai Abdallah har gida nawa ne dashi ne?nice nayi wa kaina wannan tambayar,ganin ya kuma kawo su Dije da Laila wani gidan mai shegen kyau, A hankali ya fito da fafy daga cikin motar,Laila ta kama hannun sa suka shiga takawa su Dije na binsu Abaya,sai da ya kai fafy har cikin daki yayi masa duk wani abu da ya kamata,kama daga karin ruwa allurai da sauran su,kana ya Umarci hafiz ɗan Dije da ya zauna a dakin tare da fafy ya dinga kula dashi,su kuma ya wuce dasu sama inda ya bawa Dije da salma ɗiyar ta daki ɗaya,daga nan kuma ya kai ummi Laila lafiyayyan ɗaki,sai alokacin yayi magana da ita,duban ta yayi cikin nutsuwa da girmamawa yace"Ummi ga nan dakin ku zauna a gidan nan gaba dayan ku,saboda kuna bukatar tsaro gaba dayan ku!'juyawa yayi zai fita sai kuma ya tsaya sakamakon jin muryar da yaji tamkar Bint ɗinsa na magana, tace"samari ya kamata kayi min bayanin ko kai waye da kuma dalilin taimakon mu da kayi? ɗan murmushi yayi wanda sai da zuciyar Ummi Laila ta buga sakamakon ganin tsananin kama da ta hanga kan fuskar sa da kuma yanayin sa da mutumin da baza ta taɓa mantawa dashi arayuwarta ba,yace"karki damu ummi yanzu kuna buƙatar hutu zakiji duk abinda kike bukatar ji,amma kiyi haƙuri yanzu da akwai babban matsalar da nake son warwarewa,yanzu zan aiko muku da abinci!'ya faɗa yana ficewa daga ɗakin,zuru tayi tana daɗa kure bayan shi da takun shi da kallo,sak Umar ɗina ta faɗa tana waɗawa toilet dan yiwa jikin ta kyakykyawan wankin da ya dade bai samu ba.

Abdallah bai bar gidan ba sai da ya tabbatar su ummi basu da wata matsala,har satar kallon ummi Laila yake saboda yadda take masa tsananin kama da Bintun sa gashi kuma tayi wanka tayi fes da ita cikin doguwar abayar da ya siyo mata,shi yasa duk damuwar sa ta karu ya ƙagu da yaga lafiyar Bint,tazo ta ga ya cika mata alƙawarin da ya ɗaukar mata akusa,yana matuƙar san ganin farin cikin ta wanda kuma hakan bazai taba samuwa ba har sai ya kuɓutar da ita daga hannun wani can azzalumin ya kuma kawo ta gaban ummin ta da fafyn ta, Daniyal ya kira ya kawo musu take away,kana ya umarce shi da ya zauna tare da su ya kula dasu A matsayin sa na namiji kuma ma aikacin tsaro,daga nan fita yayi shi kaɗai ya ɗauki Dady jafar A gida suka nufi inda suke son zuwa,tashar jirgin sama suka nufa inda suka haɗu da wani farin Bature, daga Ni ma dai ya ɗan jima yana jiran zuwan nasu,bayan dan gaisuwa ta mintuna ya miƙawa Abdallah saƙon hannun sa yana cewa gaskiya kayi sa a, sosai da samun wannan sakon a cikin kwana ɗaya da yini ɗaya! murmushi kawai Abdallah yayi ya juya suka bar tashar.

Dady jafar ya ɗan dubi Abdallah kana ya maida kansa zuwa hanyar da suke bi,yace"yanzu meye mafita ta ɓangaren samun kiran nasa,kaga mun gama shirin mu yanzu shi muke jira!'abdallah yaɗanyi slow da motar kana yace"nima tunanin da nake kenan!'bai gama rufe bakinsa ba, sai ga wayar mutumin,da sauri Abdallah ya ɗauka yana mai fatan samun nasara tunda ya gane ko waye yake kiran,ba tare da ya bari ya saurari abinda zaice ba Abdallah ya tari numfashin sa da cewa,ɗan zaki ya shirya zuwa karbar zakanyar sa!'wata irin dariyar mugunta ya sheƙe da ita kana yace"yauwa ɗan zaki ka kyauta,ke nan ka shirya zuwa inda zaka samu zakanyar ka!'yace"kai nake saurare?cewar Abdallah ke nan,da zuciyar sa ke wani irin tuƙuƙi saboda sauraran Muryar wannan baƙin ƙumurcin,nanu yace"ina mai kuma yi maka gargaɗi akan zuwa da wasu mutane ko kuma jami an tsaro,yin hakan daidai yake da rasa matar ka da mahaifinka,nayi alƙawarin kashe su koda zan rasa rawa rayuwar kuwa!'cikin ƙosawa Abdallah yace"ina jiran address wannan duk na dade da kiyaye su!'hakan yayi kyau ɗan zaki,ka kalli fuskar wayarka zata haska maka inda zaka same mu ba tare jinkiriba!' Dady jafar ya dube shi da sauri yace"maza muje mu dauko Abubakar ɗin kar lokaci ya ƙare!'cikin hikima suka karbi Dady Abubakar daga wajen Malam na zaure,daga nan kuma sai suka dauki hanya,yana tafe yana waya dasu Safwan akan shirin kama su Alhaji Hashir da Alhaji Nasir da dai duk sauran ƴan tafiyar su,

A can kuma su Abba Umar wani ɓoyayyen gidan sa ya kaisu su Hajjo,tare suka ɓoye kansu,dan gabatar da shirin da suka shirya,
Chapter 94 · 0% Book details