← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 120

Sashe 32

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sallama ta shiga ɗakin,Hajiya Babba dake jera kayan guga A kwabarta, ta amsa fuskarta cike da mabayyanin farinciki tare da saurin A jiye kayan hannun ta ta janyo Bintu jikinta wadda take shirin duƙawa, cikin ƙaunar yarinyar Hajiya Babba tace"Bintu na ina kika ɓuya kwana biyu ina ta cigiyarki? Bintu tayi ɗan murmushi tana aiyana wa A ranta wato Rahima bata gayawa Hajiya Babba komai ba kenan, Hajiya Babba ta katse ta da cewa Bintu ki daina dogon tunani ke yarinyace mai ƙananan shekaru idan kika bari yawan tunani ya aure ki zai iya haifar miki da wata babbar matsalar dan haka ki manta da abinda ya faru Ni nasan bazaki taɓa aikatawa ba,tashi maza ki gaya min inno ta yadda da satar da aka laƙa miki? da sauri ta girgiza kanta yayin da ƙwallar ƙaunar bayin Allan nan take ƙoƙarin zubo mata, Hajiya Babba tace"a'a Bintu bana son kuka fa ai komai ya wuce,zan cigaba dayi miki addu'ar neman tsari daga sharrin dake cikin gidan nan insha Allah babu abinda zai sameki kema ki dage da addu'a kinji? Bintu ta rungume Hajiya Babba amma takasa furta komai a kan harshen ta,wani littafi Hajiya Babba ta janyo dake kusa da ita ta miƙawa Bintu tare da cewa, karɓi wannan Bintu zai tai makeki duniya da lahira,Bintu ta karɓi littafin tana duba sunansa DA HAKA NA GAGARA shine sunan littafin,Hajiya Babba tace"kije ki duba kiyi wata addu'a tana nan A shafi na goma sha tara sunan addu'ar GAYAWA JINI NA WUCE bazan gaya miki komai ba sai kinje kin gwada Allah Ubangiji ya taimaki rayuwar ki!'Bintu ta buɗe baki zatayi magana sai ga Rahima ta shigo da sauri tazo ta rungume Bintu, tana cewa dan Allah Bintu ki gafarceni nayi nadamar abinda da aikata miki saida Hajiya Babba ta fahimtar dani san nan hankalina ya dawo jikina dan Allah kiyi haƙuri!'Bintu tayi murmushin ta mai sanyi tanajin farin ciki har cikin ranta ta kuma samu salama cikin zuciyar ta, tace"Anty Rahima na fahimceki!'tura baki Rahima tayi ta harari Bintu tare da cewa, ai gashi nan kin rama tunda kince min Anty!'dariya suka saka gaba ɗaya kana suka fita suka nufi ɓangaren inno.

Duk da haka dai wannan abin yana zaune cikin ƙasan ranta,tanaji har yanzu A kwai wanda yayi saura ya fahimceta,tanajin rashin daɗi can ƙasan zuciyarta ɗan tura bakinta tayi cikin gunguni tace"shi wannan miskilin bazai yi maka alama ba kuma bazai fahimtar da kaiba,ji tayi kamar zatayi ƙwalla saboda bata sani ba ko kallon ɓarauniya yake mata,ko shima ya fahimceta oho,wata zuciyar tace da ita ya fahimceki kawai bazai nuna miki ba saboda karkiyi farin ciki,ɗan murguɗa ƙaramin bakinta tayi kamar yana ganinta,to ma meyene ta wani damu yaje can da halinsa tunda inno da Hajiya Babba da Rahima sun fahimceta to ai bata da wata sauran damuwa.

Duban samuyal Abdallah yayi kana ya nuna masa gidan da yake ɗan nesa dasu yace"inaso nasan wan can gidan na waye kuma suwaye suke zaune A cikin sa?samuwal yace"don sir!: kana ya kuma cewa daga yau zuwa gobe nake buƙatar komai!'daga nan Yahya yaja motar, ɗan juyowa yayi yace sir ina muka nufa asibiti ko gida? yace"office ɗin sirri!' ok sir"

Baba nura ya dubi Alhaji Salisu kana cikin tashin hankali yace,me mutanen nan suke nufi ne Salisu? kaga fa yaron nan ashe jami in sirrine, Alhaji sama ila ya ɗan ciza yatsa kana yace kun san abinda nayi tunani?gaba ɗaya suka zuba masa ido suna sauraren sa, ya ɗan ja ajiyar numfashi kana yace" inaga fa leƙen asiri yaron nan yazo yi!"Alhaji rufa'i (Babban yaron Alhaji Balarabe dake zaune akano yana auren sakina ƴar wajen Hajjah)takanas yazo har A buja saboda wannan zaman da zasuyi,gyara zaman sa yayi kana cikin nutsuwa ya fara magana,Ni ina ganin ba wannan dalilin ne ya kawoshi ba akwai dai babban dalili ta can ɓangaren Alhaji jafar!' wannan karon Alhaji Salisu ne yayi magana yace"duk abinda muke bibiya har yanzu bamu kai gacin nasarar tafiyarmu ba Ni dai aganina kama ta yayi mu maida hankali kan abinda ke gabanmu!'Alhaji Sama'ila yace tabbas maganarka haka take yanzu munajiran baya nai ne daga gurin Baffa Hashir daga nan zan bawa su ligidi aikin zasu yi shi batare da matsala ba!'

Dady jafar, ya kalli Abdallah tare da cewa yanzu wa kake gani acikin ma aikatanka mata zaka danƙawa ragamar shiga rayuwar Alhaji salisu? Abdallah yace" Dady Anty Samira zan dan ƙawa aikin nan saboda kaga ita bazawarace kuma tana da hikimar aiki zamu tura ta wajen Alhaji Salisu,nasan zata ɗauko mana dukkan bayanan da muke buƙata!' yauwa Alhamdulillah masha Allah,sai kuma batun Dadinku Mansur!' A hankali Abdallah ya ɗan kwantar da jikinsa,kana cikin nutsuwa,yace" Dady wannan bana ta tashi,Dady yace" ya kamata kasaka yariyar nan cikin tafiyar nan zata iya yi mana amfani!' runtse idanunsa yayi yana hango rigimammiyar fuskarta,can ya ɗan nisa kana yace"rabu da ita rigimammiya ce!'murmushi Dady yayi batare da ya kuma tankawa ba.

Wani irin shaƙurar ran kallo momy abigirl take bin Ayoyah dashi, tanason cewa wani abu amma ta kasa saboda maganar ta maƙale mata,can dai ta samu ta haɗiyi wani kakkauran miyau kana cikin tashin hankali tace"Ayoyah me kike nufi da wannan zan can naki? Ni kike sanarwar cewa ba gidan tiraning David ya kai Fatash ba? Ayoyah cikin tabbatar da zancanta tace"Abigirl banzo miki da maganar nan ba sai da na gama bincike, na kuma tabbatar da abinda naji kuma na gani, tabbas Abdallah yana ESTATE ɗin ALHAJI BALARABE,yana can yana rayuwa cikin musul mai yana kuma addininsa na Musulunci,hannu Abigirl ta ɗora aka ta kurma wani uban ihu, wayyo shikenan tawa taƙare asirina yana gab da to nuwa!'tashi tayi da gudu kamar mahaukaciya sabon kamu, sama ta haye bata tsaya ko ina ba sai tsakiyar ɗakinta zubewa tayi tana faman juya kanta ta rasa inda zata saka kanta saboda tsananin tashin hankali lallai idan batayi wani abuba, watan tonuwar asirinta yayi gashi nan garin neman gira zata rasa ido har da hanci da baki,zuface take keto mata ta ko ina, Abigirl tana cikin tsaka mai wuya me yasa David zai mata haka me yasa zai ci amanarta? ƙirjinta ta dafe da ƙarfi A yayin da wani tunani ya shige ta kaddai David ya gano sirrin da saninsa yake dai dai fansar rayuwar ta ?kai bai gano ba tabbas da ya gano da tuni sun daɗe da aikata lahira shi da Abdallah,to yanzu me zatayi dan cigaban rufuwar wannan mur ɗaɗɗen sirri? wani ɓangaren na zuciyarta yace mutuwar Fatash (Abdallah)runtse idanunta tayi ta na mai juyayin wannan shawara,idan kuma batayi hakan ba tabbas reshe zai juye da mujiya mutuwa biyu ce zata tabbata akanta,miƙewa tayi har zata fita sai kuma ta dakata ta ɗauki wayarta da mukullin mota ta fita.

Yau tsawon kwanaki biyu kenan yana gwada zuwa wajen amma sai ya kasa shiga ɓangaren to wai meyasa hakane? hakan yana nuni da lallai an kewaye gurin da manyan sirrika,tunda ya auna ya gani kuma ya ankare tun da yazo gidan bai taɓa ganin wata halitta ta kusanci gurin ba,sai dai wannan inuwar da yake yawan gani lokaci lokaci,to ya akayi wannan matsoraciyar yarinyar take iya tun karar wajen? meye tare da yariyar nan ne? ko dai ta bakin Dady jafar ne dole sai sun sakata cikin wannan mugun haɗarin,anya baiyi ganganci ba idan yasaka Bintu cikin haɗarin gidan nan ba? to meyasa yake tsoron sakata bayan itama tana da burin tai makon ahlin gidan?to amma dai dole ya nutsu yayi tunani akan al'amarin.

Gaba ɗayan su yau suna cikin ƙungurmin dajin da ko tafin hannun su basa gani, sai dai dake shu'umai ne su wannan shine cigaba agurinsu cikin gidan kansa din ɗin yake babu abinda kai baƙo zaka gani amma su dake sun san kansu da sirrinsu basu da wata da muwa da hakan, wutace A tsakiyar su take ci tamkar za'a babbaka mutum, wannan wutar itace idon su, dukkanin su sunyi tsit dagani zaka san cewa wani muhimmin aiki sukeyi wanda da gani yana basu wuya,cikin wata kakkausar murya shugaban nasu yace"nanu Akwai babbar matsala tunda har muka kasa hana kifanyan nan tun karar ɗakin iko,munyi nasara a kan kifin babu yadda zaiyi ya iya tsallaka wurin nan,kai ko tsuntsu ne yazo giftawa ta saman ɗakin nan sai ya fado ƙasa matacce,yanzu tashin hankalin mu kawai wannan fitinanniyar kifanyar,mafita ta ƙarshe itace..banji me sukace ba saboda ba da Yaren da nakeji yayi magana ba,daga nan kowa ya ɓace da ɗamarar sa ta fara yaƙi.

Gudu take sheƙawa kamar zata tashi sama har ta kusa dan gana da inda zata, sai kuma taja wani uban burki wanda saura ƙiris ta angije wani me napep bata kula da zagin dayake antaya mata ba ta gangara gefe tayi fakin wayar ta dake ta neman ɗauki ta raruma,ta can ɓangaren cikin muryar ƴan daba akace mata Mr Devid ya akayine naga kiranki Ina cikin ɗaukar saiti!'ajiyar zuciya ta saki kana tace"

Fire kana inane yanzu ina kan hanyar zuwa tsangayar ka!' yasa wata shegiyar dariya mai ban haushi, kana cikin maganarsa ta maye yace"hajjaju kenan kin so dakar gurbi saboda Ni yanzu bana Abuja na tafi ƙaddamar da ɗan wani aiki amma ba zan jima ba ki bani sati biyu kawai on my way!'momy Abigirl taja dogon numfashi kana tace"shike nan Fire Amma naso kana kusa saboda aikin na gaggawa ne amma babu damuwa zan jarraba wasu hanyoyin kafin dawowarka!'yauwa hajjaju sai nadawo ɗin!'kifa kanta tayi jikin sitiyarin tana maida numfashi,sai da ta ɗauki wasu ƴan mintuna kana taja motar A hankali kamar ba ita ta gama sheƙa gudu ba,

Can cikin baccinta taji kamar motsi ta bayan ɗakinta har ma da sautin magana ƙasa ƙasa,cikin sanɗa da san cire tsoro ta tashi ta nufi jikin window A hankali ta manna kunnenta, abinda taji ana faɗa shiya matuƙar tayar da hankalin ta zama tayi daɓar aƙasan ɗakin yayin da zufa take yanko mata ta ko ina tamkar babu fanka A ɗakin,kafin kace meye idanunta sun jiƙe jagab da hawaye,yadda taga rana haka taga dare sai dai bata bari daren ya tafi abanza ba saida ta rayashi da kiyamul laili.
Chapter 32 · 0% Book details