← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 120

Sashe 84

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Recording ɗin yana zuwa ƙarshe Abdallah ya kashe wayar tare da miƙewa tsaye goya hannayen sa yayi yana ɗan zaga filin ɗakin,a fili yace"hakan yana nufin ke nan su Fafi suna waje ɗaya da Abbana,mutum ɗaya ne duk ya sace su?idan hakane meye hurumin su acikin wannan al,amarin?munji manufar Nafisa sai kuma manufar baƙin azzzlumin!'sanadin juya bayan da yayi ne yasa baiji fitar Bintu ba sai rufe ƙofar ta,cikin zafin nama yabi bayanta wanda tana gab da fita daga falon ne ya cimma ta,cikin zafin naman da bai san yana dashi ba ya kamota, cikin wani irin yanayin damuwa yace"Bint Ina zakije?me kike Shirin aikatawa ba tare da kin sanar dani ba?cikin wani irin azababban fushi da ƙwarin gwiwar da take ji,tace"t wan can ɗakin zani kuma a yau zan fiddo abinda aka ɓoye acikin sa ko akeyi aciki,tun tuni mafarki na ya nuna min cewa wan nan ranar itace ranar da zan baiyana abinda ke cikin ɗakin nan,kuma Allah ya bani ikon ganowa wan nan ɗakin shine zai kawo mana ƙarshen wannan mugun mutumin,Yahh Abdallah dan Allah kabarni naje inaji ajiki na cewa a kwai Babban Al'amarin dake ƙunshe cikin ɗakin nan!'kallon agogo tayi cikin tashin hankali tace"lokacin zai wuce,sha biyu ta kusa ƙara sawa bayan kuma shine lokacin da jikina da zuciya ta suke bani cewa Allah zai bani nasara,a mafarkina angaya min cewa da zarar biyu tayi banyi abinda ya dace ba komai zai iya faruwa saboda a wannan lokaci ne mai dakin yake fitowa dan aikata mugun nufin sa!'tana kawowa nan a maganar ta ta fita da wani irin sauri, Abdallah bashi da zaɓin da ya wuce yabi ta tunda taƙi sauraren sa ma balle yasamu abin cewa,addu a ce dai bata yankewa daga bakin sa da zuciyar sa.

A cikin wannan daren kuma tuni ƴan aiken Abdallah sun cika aiki sun sanƙamo masa Abigirl wadda take ta ihun neman dauki,duk da cewa Muryarta bata fita saboda manne bakinta da sukayi da salatif,tun tana iyawa har ƙarfin ta ya ƙare ta haƙura, kasan cewar basu taho da wuri bane yasa suka kai har wannan lokaci na shabiyu da min tuna na daren ranar,samuyal ne ya dubi Safwan cikin gurɓatacciyar Hausar sa yace"Safwan baka lura da moto ɗin dake binmu tun fitowar mu daga cikin gari ba?ya faɗa yana mai leƙa bayan sa,Safwan dake gaba kusa da drever shima saita madubi yayi dan san gasgata maganar samuyal ɗin,sani dake tuƙi yace"tabbas maganar samuyal haka take ashe bani kaɗai na luraba, kawai nayi shuru ne saboda nayi tunanin ko hanya ce ta haɗamu!'Samuyar yace"nima daga farko abinda nayi tunani ke nan amma yanzu na fara zargin wani abu saboda da hanya ce ta haɗa mu to tabbas zasu iya wuce mu ko kuma mu muyi musu nisa!'shuru su kayi gaba ɗayan su kowa da abinda yake rayawa a zuciyar sa,sai daga can Safwan yace"ko Oga Abdallah zamu kira mu sanar dashi?sani yayi saurin cewa a'a ba haka za ayi ba bai kamata mu katse masa baccin sa ba,dabara zamuyi yadda zamu gane idan ma mu ɗin suke bi tunda kunga yanzu bamu tabbatar ba!'Samuwar yace"good i dea,hakan ne yasa suka ɗauke hanya suka canja daga hanyar da suke kai dama sun zo dai dai titin da zasu hau su shigo Abuja.

Yanzu kam sun tabbatar da abinda suke zargi dan kuwa motar su ta kuma biyowa tare da ƙara gudu daga dukkanin alamu dai yanzu so suke su cimmasu, Safwan yace"sani ƙara gudu so suke su tare mu da alama dai wan nan abar dake tare damu suke son karɓa!' yana nufin Abigirl wai,cikin wani irin gudu motar ta ci gaba da biyo su wanda ga dukkanin alamu ma kamar so suke su bige motar su Safwan ɗin,ganin haka yasa hankalin Samuyal ya tashi,cewa yake kashemu suke sonyi!' sani yace ku kwantar da hankalin ku insha Allah muna tare da Allah kuma zai fidda mu ƙarshen sune yazo, ga dukkanin alamu Abigirl ta san sirrin su shi yasa suke son kasheta ganin bazasu sameta bane yasa zasu kashemu baki ɗaya!'

A can ɓangaren su Bintu kuwa lokacin da Abdallah ya biyota har tayi masa nisa hakan ne yasa ya haɗa da gudu ya cimmata, ESTATE ɗin yayi shuru bakajin motsin komai saina iskar damunar da take kaɗawa A hankali,atare suka shiga wajen da taimakon addu'a A bakunan su,har suka je bakin ƙofar basu daina ambaton Allah ba,cikin ƙarfin gwiwa Bintu tasa hannu akan ƙofar tana ɗan turawa,cikin raɗa Abdallah yace"Bint ya zamuyi mu buɗe ƙofar nan duba ko wajen ɗan mukulli babu!'Yahh Abdallah angaya min yadda zamuyi ƙofar ta buɗu,ta tsafi ce ƙofar dan haka karya tasirin ta addu'a!'ta faɗa tana ƙara ɗora ɗaya hannun nata akan ƙofar,matsowa yayi shima tare da yin yadda tayi rufe idanun ta tayi shima sai yayi hakan, addu'oi suka fara karantawa a fili,cikin ƙudurar Allah saiga ƙofar na yin ƙasa tamkar wadda ake janye ta ta cikin ƙasa,bin ta sukayi da ido har ta nutse cikin ƙasan gurin,kallon juna sukayi alamu yayi mata da su shiga, cikin tsananta addu'a da miƙa lamura ga Ubangijin talikai suka afka ɗakin wanda yake dun ɗum da duhu baka iya ganin ko tafin hannun ka,da sauri Abdallah ya riƙo Bintu bakin su ya kasa daina ambaton Allah.

Sosai fa mutanen ke son tura motar su Samuyal cikin rami,amma hakan ya gagara dan dukkan su addu'oi ne ɗauke abakin su, idan kacire Samuyal da ba Musulmi ba,shi kam amatuƙar ruɗe yake dan baya son mutuwa ko kaɗan,ji yayi kawai bakin sa ya kama innalihin da su Safwan suke ta ambata cikin ɗan ɗaga sauti yake ƙara nanata ta akan harshen sa,tun yana faɗa ba daidai ba har ya dawo yana faɗa dai dai,sai ya zamana duk addu'oin da suka kama marasa tsauri shima yana iya kamawa kamar allahumma ajirni filmusi bati wakalifni khairan minha, da la ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalumin,lahaula da A uzu bikalimatullahittammati min sharril ma kalaƙa,cikin ƙudura ta ubangi da kiyaye bayin sa da suka tsaya gareshi suka nemi taimakon sa,a maimakon mutanen su sami na sarar jefa su Safwan sai kawai burki ya ƙwace wa drevern waccan motar kafin ƙiftawar ido sun afka dogon ramin da suke san jefa su Samuyal,ji kake bam motar ta tashi da wuta.

Wata irin doguwar ajiyar zuciya suka sauke tare da faɗin Alhamdulillah!' a fili sai shima Samuyal ya kuma faɗa, sai lokacin suka samu nutsuwar tunawa da abinda Samuyal yayi, shi kuwa Samuyal tuni ya tafi duniyar tunanin ƙarfin mulki irin na Ubangijin sammai da ƙassai,ganin abun yake tamkar sihiri wato waɗan nan addu'oin da sukayi sune suka tseratar dasu daga hannun waɗan nan mugayen,suma dai su Safwan basu ce masa komai ba amma suna fata da buri wan nan abin da ya faru yanzu ya zama izina da kuma sanadin da Samuyal zai gane gaskiya,ita kuwa Abigirl saboda abin da suka shaƙa mata bata san duk wan nan abin ya faru ba,

Wayyo Yahh Abdallah duhu babu haske ya zamuyi yanzu ta ina zamuga makunnin fitila?Bint ki nutsu Mana Ina ƙwarin gwiwar taki ya tafi?bakiga Allah yabamu nasarar shigowa ɗakin ba?kuma kina gani saboda Allah yana tare damu bamu sami wata matsala ba,kuma kin san abinda yake faruwa dake duk lokacin da kika zo wajen amma a wannan lokaci dake nasarar tana garemu babu abinda ya faru, kuma zamu fita lafiya insha Allah!'jikin sa ya shiga lalubawa,cikin ikon Allah kuwa sai gashi ya zaro karamar wayar Bintu,cikin farin ciki yace"Alhamdulillah,tare da kunna toch ɗin wayar.
Chapter 84 · 0% Book details