← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 120

Sashe 100

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tun bakwai take zuba ido ko zataga daya daga cikin su yazo mata da maganar Abubakar,amma shuru take ji,gashi ta ƙagu taje tayi abinda yake gabanta,har daga baya ta yanke shawarar fara tafiya ta gabatar da babban ƙudurin ta,sai kuma ga sallamar Dady jafar a kofar falonta,duk da cewa ta riga ta shiryawa fuskantar kowanne daga cikin su amma sai da taji faduwar gaba,(Hajja kenan to ina batun kwanciyar hankali akan abinda babu Allah acikin sa)sauri tayi ta ƙara burkita yanayin ta tare da gaiyato tashin hankali kan fuskar ta,idanun ta kuwa ta shirya musu tun adaren jiya gasu nan sunyi jawur kamar gaske,zama yayi bayan ta amsa sallamarsa cikin wani irin yanayi da kukan da take ta san ƙirƙirowa kanta,Dady jafar yace"Hajja lafiya dai ko?cikin kukan da ta gama shirya zuwan sa tace"jafar ina fa lafiya,tun bayan dawowata gidan nan bayan rabuwar mu da Mansur yaran da na bawa ajiyar Abubakar da kuma likitan da na kai masa dan ya duba lafiyar sa,suka kirani suke sanar dani cewa Habibu ya tura abokan nan sa matsafa sun tafi da Abubakar ɗin!'ta ƙara sa maganar tana fyace hanci da haɓar zaninta,idanunta kuwa kai kace kukan tun daga ƙasan zuciyarta yake fitowa,da sauri Dady jafar ya mike cikin nuna mata tsananin tashin hankalin sa yace"innalillahi'wa'inna'ilaihi taji'un yasa hannu ya share zufar da ta tsatstsafo masa kana yace"shi kenan Hajja karki damu ai shi Habibun yana wajen su Abdallah dan haka zamu sa ya fito da Abubakar ko ta halin yaya fatana dai kar yasa sukasheshi!'Hajja ma mikewa tayi tana ɗan share hawayen fuskarta tare da cewa shikenan Jafaru amma kar wanda yasan da wannan maganar har sai mun sami nasarar kuɓutar da Abubakar daga hannun waɗan nan azzalumai!'yace"insha Allah Hajja karki damu komai zai tafi daidai!'daga haka sukayi sallama ya fita yana sakin wani ƙayataccen murmushi,yanzu ne ya kuma yadda da shu'umancin wannan mata,saboda shima yasan itace wannan matar me niƙaf tun ajiya Abdallah ya kirashi ya sanar dashi,ji yadda take yi tamkar wata ƴar wasan kwaikwayo,cikin ƙwarin gwiwa ya faɗa motar sa ya bar estate din ba tare da ya shiga ko ina ba.

Tana tabbatar da tafiyar sa,ta sheƙe da wata muguwar dariya,cikin jinjinawa kanta tace"saini Hajiya yagana mai buga gangar shaiɗan A bayan gida!'cikin takun ta na ƙaisa da alfahari ta shiga ɗakin ta,shiryawa tayi ta fito dan kaiwa ga inda zata cimma burinta.

Wayar sa ce ta tasheshi daga nannauyan baccin da ya kwashe su,kamar ba zai daga ba,sai kuma ya daga ganin Safwan ne akan layi,baiyi magana ba,sai daga can ɓangaren ne Safwan yace"sorry sir Abune ya taso na gaggawa,dama wannan Abigirl ɗin ce ta farka!'cikin sauri Abdallah ya ɗan zame Bintu daga jikin sa tare da miƙewa zaune,yace"Safwan kuyi mata duk abinda ya kamata kar kubarta cikin mummunan yanayin da zata kasa amsamin ɗinbin tambayoyin da nake son yi mata!'cikin girmamawa Safwan ya amsa kana suka katse wayar.

Cikin kanƙanin lokaci ta isa gidan saboda uban gudun da take sheƙawa,kai wannan tsohuwa akwai ƙarfin hali,ko da ike matan Alhaji Baba suna da matukar kyanjikin da bazaka iya tan-tance shekarunsu kai tsaye ba,shi yasa Hajja take jin kanta har yanzu da sauran ƙuruciyar ta,tana shiga suka shiga miƙa mata gaisuwa,yadda take amsawa ma kaɗai ya isa ya baka tabbacin yadda ta dauki KANTA,kujera aka dasa mata gaban Dady Abubakar wanda yake zaune hankali kwance,kai bakace saceshi akayi ba, murmushi tayi kana tace"da kyau yarona,da ganin alamu dai zaka iya bani haɗin kai cikin sauki ba tare da ka wahalar da hajjan ka ba!"ta faɗa tana wani shu umin murmushi,shima murmushin yayi tare da cewa,Hajja kar ki manta fa Ni ɗan ki ne ko nayi gaddama wa Habibu aike bazanyi miki ba,dan haka tambayeni duk abinda kekeson tambayata!'dariya tayi wadda ke cike da farin ciki kana tace"yauwa my son, shi yasa tun farko ka shiga raina ban taɓa kuma tunanin cutar da kaiba,inda dimon ɗin nan yake kawai nakeso ka faɗa min sai na mayadda dakai gida gaban iyayenka da ƴaƴan ka!'wata irin dariya ya sheƙe da ita, sai da yayi mai isarsa kana cikin muryar sa ta ainahi yace"kai wannan tsoho akwai shashasha!'sororo sukayi gaba ɗaya suna kallonsa cike da ɗin bin mamakin yadda akayi muryarsa ta canja lokaci guda,kafin ta gama fita daga mamakin da ya sakata ya kuma jefa ta cikin wani irin firgici da tashin hankali,sakamakon yaye fuskarsa da yayi,yacire fuskar ABUBAKAR da aka saka masa,fuskarsa ta cikakken bayerabe ta bayyana.

Wata irin zabura Hajjah tayi tare da dafe ƙirjinta da yake wani irin bugu,cikin rawar hannu da na baki ta shiga nunashi da yatsa,yayin da bakinta ya kasa furta abinda take son furtawa,da ƙyar ta iya fuzgo maganar tace"kai kaiwaye? ID ɗin shi ya curo ya nuna mata yana mai ɗage mata gira,yace"wannan duk lissafin yaro mai ƙwazone, Abdallah yayi nisa babu mai iya taradda dashi,tunanin sa yana tafiya daidai kuma aikin sa na tafiya daidai da abinda yazo tunanin shi,ku da kuna nufin a jakar kwaƙwalwar ku ke da ɗanki Abdallah zai dauko mahaifin sa ya kuma mayar da shi inda ya kubuta da ƙyar? girgiza kanshi yayi yana wata dariyar tura haushi,Hajja kuwa tsugunawa tayi tare da dafe kanta ta rasa abinda yake mata daɗi, wannan shine taga samu taga rashi,yanzu ya zatayi ke nan,kashe mutumin nan zatayi ko zata rabu dashi ne in yaso ta rokeshi ya rufa mata asiri ta hada masa da manyan kuɗaɗen da zai jima yana amfanarsu?kai anya kuwa hakan zata yuwu?Gara kawai tasa sukashe shi hakan shine zai zama rufin asirinta,to amma ya zatayi da ƙaryar data zubawa Jafar?meye manufar sa da bai gaya mata cewa ba ABUBAKAR ne suka zo dashi ba?tunawa da wannan yasa takuma shiga tashin hankali,sosai ƙirjinta ke bugawa tamkar wanda ake kiɗan ganga acikin sa,miƙewa tayi tare da yanke shawarar kawai ta cigaba da rike mutumin nan anan har sai ta tabbatar da cewa ba ganota Dady jafar yayi ba da har ya ɓoye mata,abinda suka aikata akan Abubakar,fita tayi tana cewa ku ci gaba da riƙe shi anan,koda ta zauna cikin motar ma kasa ja tayi jikin ta duk yayi sanyi,amma gaskiya yaron nan ya shammace ta da yawa,ko ina Abubakar ɗin yake oho?ita yanzu da zata samu tasan inda dimon ɗin nan yake ai da komai ma zata iya ɗauka,A hankali take jan motar tunani fal cikin ƙwaƙwalwar ta...

FATIMAH Y ADAM✍🏽
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

```Page 56 ```

Yana gama waya da Safwan ya tashi ya faɗa toilet,wanka yayi ya shirya tsaf,kana yazo ya tsaya akan Bintu da har yanzu take ta shaƙar baccin ta hankali kwance,a hankali ya sunkuya ya kai bakinsa kan ɗan ƙaramin bakinta ya sumbata,wanda hakan ya farkar da ita, zuba masa ido tayi kana kuma ta ɗan tura baki tare da cewa nifa bacci nake ka tasheni!'ɗage mata gira yayi,ba tare da yace"mata komai ba yaja hannunta ya miƙar da ita tsaye, sannan a hankali ya kuma janta har zuwa cikin toilet duk bata ce mashi komai ba,sai da taga yana ƙoƙarin cire mata kaya,kana tayi saurin riƙe hannun damansa cikin tura baki tace"wai mi zakayi ne? cikin haɗe fuska yace"wanka zanyi miki!'zaro manyan idanunta dake matuƙar burgeshi tayi,kana cikin san ya tausaya mata,tace"dan Allah kabari zanyi da kaina!'ba tare da ya tanka mata ba,ya rabu da ita tare da ficewa daga toilet ɗin,wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke kana tashiga tsaftace kanta.

Bata sameshi a dakin ba sai kayanta da ta tarar har da mayafi da alamu dai yanzun ma fita yakeso suyi,a nutse ta shirya duk da yunwar dake sakaɗar ƴan hanjinta,tsaf ta fito da ita cikin doguwar rigar atamfa mai kalar kore da baƙi, sai hakan ya kuma haska kyawunta da ƙuruciyar ta suka kuma bayyana,takalmin ta ta zura bayan ta feshe jikinta da sassanyan turarukan sa,fita tayi cikin wani irin taku tamkar wata ɗawisu.
Chapter 100 · 0% Book details