Sashe 119
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Yau dai jirgin su Abdallah da sauran ƙannenshi ya tashi tare da rakiyar iyayensu da abokan arziƙi,tunda suka je Madina babu abinda suke sai bautar ubangiji,a cikin kwana goma sha biyar da sukayi a garin na Manzo s.w.a ba ƙaramin nutsuwar zuciya suka samu ba,gashi su Bintu kansu ya haɗe kula suke da junan su basa so ko kusa da a taɓa daya daga cikin su saboda tsananin zumuncin da suka riƙe,ga mazajensu da suke tattalinsu da kaffa kaffa dasu,dukaninsu suna cikin farin ciki da walwala,daga nan kuma kowa ya nufi ƙasar da ya zaɓa A matsayin cin amarci,shi Abdallah dake yana da wani bincike akan wani criminal da ya gudo daga can naija,ya dawo nan kasar Siriya,dan haka kawai sai suka wuce can da niyar Bintu zatayi karatun wucin gadi anan kafin su koma,hakan kuwa ba ƙaramin farinciki ya saka Bintu ba, dan haka ta nunawa Abdallah sha awarta na koyon nau ikan girkuna, saboda ko ta koma naija abinda zata karanta ke nan,yayi na am da buƙatar ta dan haka sukayi ban kwana da ƴan uwansu kowa ya nufi inda yafi wayo,
Rayuwar Abdallah da Bintu, rayuwa ce da kai tsaye zamu kirata da rayuwar farinciki da fahimtar juna,komai yayi farko haka yana da ƙarshe,Bintu bata taɓa tunanin zata kai irin wannan matsayin ba a rayuwarta, to amma dake abun ƙudurace ta Allah sai gata a inda batayi zato ko tsammani ba,ta fara karatunta na catering cikin nasara,shima Abdallah a gefe ɗaya yana gudanar da aiyukan sa wanda yake saka ran San n nasara insha Allah...
Bayan wata biyar,sai ga ciki ya baiyana a jikin Ummi Laila,waiyo zakuso kuga farincikin ABBA Umar,abin dai ba a cewa komai, Allah ya nufa Laila da Umar ɗan su yafi ɗaya a duniya,sai kuma wani abin al'ajabin, ko da yake kaɗan daga ƙudurar Allah ke nan,sai ga Anty Samira ma da cikin Dady jafar, Allahu Akbar bayan cire rai da samun wannan kyauta tsawon shekaru sai gashi Allah ya nuna masa ikonsa da buwayarsa,lallai bawa kar ya taba cire tsammani da rahamar Ubangiji, A hankali kuma sai ciki yay ta ɓullowa jikin jikokin Alhaji Baba,su Taufiƙa su Farida Hauwa'u, Rahima, kai abun dai masha Allah sai fatan duk Allah ya sauke su lafiya.
Lokacin da Bintu taji labarin cikin da ummin ta take dashi sai da tayi kuka tayi suddar shukurr,sai kuma na ƴan uwanta wanda hakan yasa ta farinciki da kuma jin kwadayin samun ciki, ,fafy ne yake faɗa mata lokacin da suke waya,ya kuma sanar da ita an saka ranar usainar sa,daɗi kan daɗi ke nan,ganin tana ƙoƙarin fasa masa dodon kunne kawai sai ya kashe wayar yana dariya,wato dan bata san shima ya kusa zama Baba akaro na biyu bane, da ji zatayi kamar tayi tsuntsuwa, kawai ta taho naija, Abdallah yana dawowa da zan cen da ta fara tararshi ke nan,sai da ta gama faɗa mashi kuma wai sai ta saka masa kuka itama sai yayi mata ciki tunda su Taufiƙa ma suna dashi, bayan kuma ta riga su yin aure amma suka zo suka rigata,a kullum wautar Bintu mamaki da dariya take bashi amma kuma da yayi wani tunani sai yaga ai shi gaba ta kaishi,dan haka sai ya matseta cikin jikinshi yana cewa yi shuru my ukty ciki kike so ba?ta daga kanta kamar wata ƙaramar yarinya,yace"to maza share hawayenki insha Allah yau zan miki ciki,bazan ƙyaleki ba har sai na tabbatar da cewa na dasa ƙwaina a nan!'ya faɗa yana shafa kan mararta,dariya tayi cike da farin ciki tana da ɗa rungumo shi jikita tace"yauwa my zauji!'
Allah mai ƙudura da irada gagara iko gagara misali,sai ga shi maganar Abdallah ta tabbata dan kuwa tsakanin ranar da yau da ta zagayo wata ɗaya cif, Abdallah ya tabbatar da cewa ya dasa ɗan sa ko ƴarsa a marar Bintu,shuru yayi dan yana so sai ya tabbatar da hakan,yau tunda ta dawo daga makaranta take kwance ta kasa tashi ko da abinci taci,dan ma gurinta tsaf yake kamar babu halittar dake motsi acikin gidan,saboda tsananin tsaftarshi da ƙamshin da yake tashi,a gurin,a haka ya shigo ya same ta kamar ruwa,cikin sauri ya ɗauke ta yana dubata kamar wanda akace masa wani abu ya sameta,yace"my Bint meke damunki?langaɓar da kanta tayi akafadarshi tana cusa kanta a wuyanshi,ba tare da ta bashi amsar tambayara shi ba, tace"wayyo my zauji, inason wan nan ƙamshin naka dan Allah kabarni in kwana ina shakarshi!'ba tare da yace"mata komai ba ya ɗaga ta suka nufi bedroom kana yace"anya my zaujaty babu ajiyata acikin nan naki? bari dai na bin cike ki sai hankalina yafi kwanciya!"zaro manyan idanunta tayi tace"amma dai ba allura zaka mun ba ko? yace"haba my jewel ya kamata ace kin daina tsoran allura tunda kinga fa kin kusa girma!'bata gane abinda yake nufi ba dan haka sai tayi rau-rau kamar zatayi kuka,cikin sauri yace"nifa bance zanyi miki allura ba,duba ki kawai zanyi!'hakan da yafaɗa sai ta hakura yayi mata duk wani binciken da yakamata,bata ankara ba sai ji tayi yana juyi da ita a tsakar dakin tare da bin ko inan ta da wani zazzafan kiss,wanda har sai da ya ruɗa ya sauya mata yanayinta abinka da dama wadda take kusa saboda cikin da ke jikinta yana ɗan sata jin bukatar mijinta,ai kuwa dai biye masa tayi suka jika junansu da ƙauna mai tsayawa a zuciya da ruhi,bayan sun sami nutsuwa ne ya mamayeta da dukkan jikinsa yayi mata rumfa da faffaɗan ƙirjinsa, kana cikin so da kulawa yace"my ukty sai ki shirya dan kin kusa zama Ummu nan da wata takwas!' ya faɗa yana yi mata nuni da yatsunsa,ganin kamar bata fahimceshi ba sai ya kama kunnen ta yayi mata raɗa dariya ta saka tare da ƙanƙame shi tana mai jin farin ciki na mamaye duka nin ruhinta.
Wata sabuwar kulawa da soyayya Abdallah ke bawa Bintu yayin da duk gida ya ɗauka kowa murna da farin cikin ƙaruwar da suka samu yake,burin Alhaji Baba ya cika zuri'arsa ta kasance cikin walwala da jin daɗi,
Abdallah ya samu nasarar aikin da yaje yi, acikin wata takwas dan haka ya zauna Bintu ta ƙarasa karatunta kafin nan suka jiyo gida naija,
Taufiƙa ce ta fara sauka ta haifi dan ta namiji sai Rahima, daga nan kuma sai Ummi Laila,kamar layi abin sai ya zama abun burgewa saboda yadda suke ta haihuwa ajere,Anty Asma'u ma ta haifi ɗanta namiji,sai Anty Samira da ta haifi namiji itama,Bintu dai itace karshe dan da akwai tazara tsakanin su,
Alhamdulillah masha Allah bayan wata uku Bintu ta san kato yarinyar ta mai kama da Abdallah da Ammi,bazan iya fada muku irin farin cikin kin da bayin Allah nan suka shiga ba, sai dai kawai mutaya su da addu'a,an sakawa yariyar suna yusra,