← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 120

Sashe 44

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda ya farka bai cewa kowa uffan ba sai zuwa duba shi suke yi, amma A cikin su bazai tan tance wanda yazo dan Allah ba,sallolin sa yayi yayi wanka ya kimtsa tsaf dashi kai bakace mara lafiya bane,tun lokacin yaso su barshi ya tafi sai kuma sukace da A kwai buƙatar ya ƙara samun hutu koda na awa ɗaya ne Dady jafar ne kawai ya samu ya lallaɓashi ya haƙura,dole likitoci suka dakatar da shiga inda yake sai Dady jafar kawai da yake tare dashi,Dady jafar ya ɗan zubawa Abdallah ido na ƴan wasu daƙiƙa,kana a hankali yace"wai Abdallah me kasani game da wannan batun ne?shiru yayi batare da ya amsa masa tambayar sa ba,idanunsa A lumshe tamkar mai bacci,Dady jafar bai daddara ba ya kuma cewa, kasan cewa tunda abin nan ya faru Bintu tana hannun ƴan sanda babu wanda ya leƙa bare asan hali...ganin Abdallah kawai yayi batara da yasan lokacin da ya yun ƙura ba,sai tsintar sa yayi yana ƙoƙarin fita daga ɗakin, cikin sauri Dady jafar ya riƙo shi,amma yadda yaga fuskar Abdallah lokacin da ya juyo shi kansa sai da ya razana matukar razana tunda yake da Abdallah bai taɓa ganin mummunan ɓacin rai tare dashi da kuma tashin hankali ba sai yau,wani irin kallo ya shiga watsawa Dady jafar wanda bai san ya a kai ya sake masa hannu ba,fita yayi cikin wata irin gaggawa kana ganin sa zakasan cewa a kwai gagarumar damuwa, me napep ya tare yace" kaini duk wata station da kasani,daga haka ya faɗa Napep ɗin me Napep yaja suka fara kewaya station,

Saboda tsabar zuciya bai san station ɗin da aka kaita ba amma ba zai iya tambaya ba,a wannan lokaci bazan iya misalta muku zaɓaɓɓakar da zuciyar Abdallah take yi ba,tun shida suke abu ɗaya sune har takwas sallah ce kawai take tsaida su,yanzu ma sallar isha sukayi daga nan ne me Napep yace" da Abdallah to Oga Ni fa yanzu station ɗaya ta rage da nasani!'wata irin tsawa Abdallah ya buga masa tare da cewa to yanzu me kake jira ne?ai da wani irin gudu me Napep yaja jikin sa na rawa bai ƙara gangancin yiwa Abdallah magana ba,har suka isa station ɗin.

A dai dai wannan lokacin kuwa Bintu tana cikin cell cikin wani irin yanayi me matuƙar ban tausayi, babu wanda ya dubeta da idon tausayi babu abinda taci ko tasha sai azabar kuka wanda shi ya zama ruwan shan ta, A halin yanzu ma tana zaune can loko ta haɗa kanta da gwiwa kuka takeyi me cike da tausayin Abdallah da kuma fargabar halin da yake ciki, wani ne ya taso ya daka mata tsawa, miƙe wa tayi a firgice,wata ƴar sanda mace ya kira tare da cewa dpo yace mu fara tuhumar yarinyar nan ta faɗi wanda yasa ta wannan mugun aikin!'to tace" tare da ɗauko wata sanda da suke dukan masu laifi....
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

```Page 30 ```

Wayyo Allah na dan Allah karku dake Ni bana son duka!'ɗan sandan yace"au dama wayake don duka ai sai dole, idan kika bamu haɗin kai ba wanda zai taɓa wannan lafiyayyar fatar taki idan kuma kikace gadda ma da taurin kai zakiyi yanzu zan farfasa lallausar fatar da kike tsoron kar ataɓa, cikin tsuke fuska yace"gaya min waya saka ki saka yin kisa?wani irin kuka ta fashe dashi tana wani irin girgiza kanta,tsawa ya daka mata tare da cewa ke nake jira ki bani amsa kuma ki faɗi gaskiya bazan ɗaga miki ƙafa ba idan kika yimin ƙarya!', numfashin ta har sarƙewa yake ta kuma kasa yin magana sai ruwan hawayen da da ace yana ƙare wa da yanzu na Bintu ya ƙare,kallon ƴar sandar yayi tare da yi mata alama Aikuwa ta dai daici kyakykyawar fuskar Bintu ta zabga mata mari wanda sai da taga giftawar wasu taurari,kamar zata shiɗe haka ta fixgo maganar daga bakinta,wal wal wal wallahi bani bace ban san komai ba kar ku dakeni bana son duka fafina kazo kabuge su kacire Ni anan gun ni ban san komai ba!'dalla Malama rufe mana baki duka kuwa kamar kin sameshi kin gama tunda baza ki gaya mana gaskiya ba!'cewar ƴar sandar nan,yace"rabu da ita yanzu zataci ubanta tunda bazata faɗa ba!'

Suna shiga cikin ainahin station ɗin ya dinga jin bugun zuciyar sa na ƙaruwa,da ƙyar ya iya sauraran ƴan san dan suka bin cika masa sunan Bintu, duk da sun san nan aka kawo ta amma sai suka farayiwa Abdallah ƴan kewaye kewaye na nuna alamun suna san wani abu daga hannun sa,ai tun da Abdallah ya tabbatar Bintu dai tana cikin wannan station ɗin ya wuce su cikin wani irin ƙaƙƙarfan taku irin na jaruman maza masu ji da da kuzari,da sauri wani yazo zai tare masa hanya amma kallon da Abdallah yai masa sai da yasa shi sakin acawi a wando,ci gaba yayi da tafiya batare da ya saurari ƙananan maganganun da suke ba,

Duka na farko da ya kaiwa Bintu akan idon Oga Abdallah, ya ɗaga zai kai mata na biyu,yaji anyi wata majaujawa dashi,wanda tashin farko yasamu karaya a hannun da yake dukan Bintu dashi,bai gama dawowa daga wannan azabar ba ya kuma jin wani uban naushi acikin sa wanda atake agurin ya zube,shi kuma Abdallah ya kuma samun damar take ƙafar sa itama atake tasamu karaya,kafin wani lokaci ƴan sandan sun gar zaya dan sanar da inspector lawan.

Da wani irin azama ta ƙara so duk da jikinta babu ƙarfi amma ita ba wannan ne damuwar taba, farin cikin ganin sa A raye yafi mata komai arayuwarta,saurin tarar ta yayi ganin tana shirin faɗuwa, wata irin runguma tayi masa mai cike da wani irin salo da ɗoki da wani irin gawur taccen farin cikin da baza ta iya musaltashi ba,tallafo ta yayi tamkar jaririya wani irin kallonta yakeyi kamar wanda yake bincikawa dan ya ga ko ancire wani abu ajikinta,cikin sa'a yaga shatin marin da ƴar sandar nan tayi mata,cikin wata irin murya mai cike da wani irin amo da ya gauraye da ɓacin rai yace"waye ya mareki tun yaushe suka fara dukanki?cikin ɓoye fuskar a ƙirjin sa tayi nuni da inda ƴar sandar take A tsaye tamkar wadda aka liƙa tun lokacin da taga an zubar da oganta cikin halin mutuwa ko rayuwa,bata gama shiga tashin hankali ba sai da taga Abdallah yayi mata alama da tazo batare dashi ya motsa daga inda yake ba,cikin rawar jiki ta ƙaraso kafin tasan abinyi taji ya ɗauke ta da wani zazzafan mari wanda lokaci guda ya ɗauke mata ji da ganin ta na wasu mintuna,duk da sun kasan ce ƴan sanda amma basu da ƙarfin gwiwar sa insa da Oga Abdallah, kwarjinin sa da ilhamarsa sun wuce ka tsaya yana faɗa kana faɗa, ƙoƙarin gyara mata zama ajikin sa yake ɗan yaji daɗin tafiya,amma sai ta saki kuka ta saka tana ƙara cukume shi,dan atunanin ta tafiya zaiyi ya barta,ƙara sautin kukan tayi tare da cewa Ni bazan zauna ba duka na sukeyi tsawa suke min na ce musu ban san komai ba sunƙi yadda,gashi kaima baka yadda ba tafiya zakayi kabarni, wallahi bani bace,idan katafi kasheni zasuyi,idan baka yadda dani ba ban san wa zai yadda dani ba,yunwa nake ji basu bani abinci ba basu bani ruwa ba mugaye ne basu da imani,katai maka koda baka yadda dani ba kafitar dani daga nan na maka alƙawarin bazan koma gidan kuba!' Abdallah ya ɗan rumtse idanun sa saboda yadda kalaman ta suke dukan zuciyar sa, A rayuwarsa ya daɗe bai cikaro da abinda ya bashi tausayi ba kamar Bintu ba,wani ɗan danshi yaji cikin idanun sa wanda ya tabbatar ƙwalla ce amma bai bari ta zubo ba,saurin ɗaga ta yayi kamar wata ƴar tsana haka ya sunkuceta,

Cirko cirko yagan su tsaye sun kasa yin ko tari da kyar ɗaya daga cikin su yace"yallaɓai yace kaji ra shi yataho!'ko kallo bai isheshi ba,sai da ya fita ya farfajiyar station ɗin kana ya tuna babu mota A hannun sa,babu waya.

Motar da ta faka a gabansa ita tasa ya maida hankalinsa kan wanda ya fito daga motar, inspector lawan ne sai Dady jafar,ɗauke kansa yayi yana ƙoƙarin barin gurin dan baya bukatar ganin su balle yayi magana da su, inspector lawan ne yace"ka dakata wannan ba hurumin ka bane ya kamata ka barmu muyi aikinmu,dole kabamu ita saboda ka karya mana doka ka daki ma alokacin mu,dan haka bazan baka koda belin ta ba!cikin tsanaki yake binsa da kallon mahaukaci mara imani,wata Napep ce ta shigo dan haka ya daga ƙafa zai ƙarasa inda take sai yaga ashe ma wanda yakawoshi ne ya dawo karɓar kuɗin sa,shiga yayi ya kwantar da ita A bayan Napep ɗin,cikin hanzari yake ƙoƙarin shiga saboda yadda yaga Bintu bata numfashi saboda yadda ta gala baita ga yunwa da ƙishi duk A tare da ita, inspector ne ya kuma yi masa magana, Abdallah kar kasake ka fita da yarinyar nan batare da ka cika ƙa idoji ba!' cikin wata irin ɓacin rai Abdallah ya nuna lawan da yatsa cikin muryar sa dake fita ɗaiɗai yace"kar ka sake kakuma da Katar dani idan kuma ba haka ba zakayi da nasanin tsayawa agabana kana yimin umarni!'daga haka ya faɗa Napep ɗin ya bar inspector lawan da baki sake cike da mamakin kwarjinin Abdallah,saboda shika kansa ƙarfin hali yake wajen kallon idanun sa.
Chapter 44 · 0% Book details