Sashe 45
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna tafiya ya dubi Dady jafar da ya tsaya kawai yana kallon su, inspector lawan yace"bai kamata ka tsaya kana kallon mu haka ba kamata yayi ka da Katar dashi tunda kaima kasan abinda yayi bai kyauta ba!'Dady jafar ya ɗan ɗage kafadar sa tare da cewa hakan da yayi shine dai dai matsayin sa na wanda aka yiwa wannan laifin yazo ya fitar da wadda akace ta aikata laifin to kuma kai meye naka aciki,ko bakasan cewa matar da zai aura bace? cikin tsananin mamaki inspector lawan ya maimai ta kalmomin, matar da zai aura kuma!' Dady jafar yace"ƙwarai kuwa ko kana mamaki ne? girgiza kansa yayi yace" ai dole nayi mamaki matar da zaka aura kuma ta nemi kashe ka? gaskiya abin da kwai rikitarwa,da matuƙar al'ajabi!'Dady jafar yace"shi yasa nace maka ka rabu da wannan case ɗin, na cikin gida ne saboda Bintu ba itace tayi wannan laifin ba kasan dai matsayi na amma banyi amfani da hakan ba a matsayina na uban Abdallah,dan haka ina baka shawara ka fita daga wannan sabgar dan kar kazo kayi nadama!'daga haka bai sake cewa komai ba shima ya wuce ya bar station ɗin.
Har cikin gidan sa na area 1 me Napep ya kaisu,kuma har lokacin Bintu bata farfaɗo ba ɗaukar ta ya kumayi a kafaɗa ba tare da ya tsaya ba yace" da me napep ɗin ya biyo shi, jiki na rawa yabi bayansa ko tsoro bayaji ko ɗan yankan kaine,suna shiga tangameman falon da ya kusa zautar da me Napep, Abdallah ya kuma cewa da shi ka dakata A nan ina fitowa!' amsawa yayi jikin sa na ɓari,shi kuwa Abdallah kai tsaye saman haɗaɗɗen benan da aka ƙawata shi a tsakiyar falon ya hau Bintu shimfiɗe A kan kafaɗar sa,kai masha Allah abinda nace kenan lokacin da naga ya kwantar da ita cikin wani lafiyayyan gado mai rai da lafiya tabbas idan kashiga ɗakin nan idan bakayi sa a ba sai kamanta a duniyar da kake,komawa yayi ya sallami me Napep da ɗaurin dubu hamsin bai tsaya sauraran doguwar godiyar da yake masa ba cikin gaggawa ya koma ɗakin tare da fara bata taimakon gaggawa,duk da shima har yanzu bajin daɗin cikin sa yake yiba amma saida ya tabbatar Bintu ta dawo hayyacin ta duk da dai bata farka ba,saboda allurar baccin da yayi mata bata cikin hayyacinta,dan da a dai dai take yasan sai yasha daru,gyara mata kwanciya yayi bayan yasa mata ruwa,
Sai lokacin hankalin sa ya dawo jikin sa fita yayi ya koma É—aya É—akin shima ya É—an watsa ruwa kana ya zura doguwar jallabiya me ruwan toka,san nan ya nufi wajen daya killace shi dan yin ibadarsa cikin nutsuwa.
A can ESTATE kuwa Anty Nafisa ce zaune cikin ɗakinta tagumi hannuwa biyu,babu abinda take sai tunanin hanyar da zatabi tacika burinta, yanzu idan akace Bintu gidan kaso za a kaita wa zata samu ta maye mata gurbin ta?san nan taya zatayi tasan wanda yasa ta wannan aikin meye kuma dalilin da yasa ita batayi mata irin wannan aikin ba taje tayiwa wani?tabbas dolene ta samu waɗan nan amsoshin daga bakinta,domin taga haɗamammun gidan kullum ƙaruwa suke dole tayi hanzarin cika burin ta,to amma yanzu fatan da take yi Allah ya dawo da Bintu saboda A yanzu ne zata fiyi mata amfani dan tasan tabbas Bintu zata iya karɓar aikin ta yanzu,to kuma idan taji tsorofa?duk yanda zatayi dole sai tayi dan rufin asirin ta da kuma samun burinta,ɗan kashingiɗa tayi tare da tsurawa hotan mijin nata ido haƙiƙa tana matsanancin son mijin ta, A baya tayi tunanin bazata iya wata rayuwa ba idan babushi har tana tsoron ranar da asirinta zai tonu saboda gudun samun tangarɗa A cikin zamansu, sai kuma gashi katsam Hajiyarta ta nusar da ita tare da ɗorata A hanya wanda har ma ji take A yanzu tafi Hajiyartata sanin matakan aikin,kawar da kanta tayi daga kallon hotan dan bata so taji tausayi ko ɗugon imani A cikin dukan niyarta ta samun duniyar ta.
Farida ta zubawa Taufiƙa ido tana sauraran ta cikin azalzalar da zuciyarta take mata take cewa, Wallahi Farida da zan samu dama saina bita har cikin station ɗin na kashe rayuwar ta ɗan bata da wani amfani!'Farida tace"Ni kuma ai atunanina an wuce gurin yanzu dan na tabbatar yanzu shi kansa Alhaji Baba bazai yadda da wannan auren ba, balle kuma uban gayyar bazai taɓa yadda ya auri matar datake son raba shi da rayuwarsa ba, Farida ta ɗan kalli ƙofar ɗakinsu sai da ta tabbatar babu wanda yake ƙoƙarin shigowa kana tayi ƙasa da muryar ta tare da cewa,dan Allah niko Taufiƙa na yi maki wata tambaya mana!'Taufiƙa tace"inajin ki"yauwa Dan Allah Taufiƙa bake kika haɗa wannan tuggun ba saboda kar Bintu ta auri Ya Abdallah?wani kallo Taufiƙa tayiwa Farida amma batace komai ba, saida Farida ta dafa ta tare da cewa kiyi haƙuri idan tambayar ta ɓata miki rai kawai dai abin da na sanine zaki iya aikata komai akan cikar burinki,shi yasa nayi miki wannan tambayar!'miƙewa tayi zata fita daga ɗakin cikin sauri Taufiƙa ta ruƙo hannun ta tare da cewa Wallahi Farida ban sani ba ban san waya aikata ba kuma banji haushin tambayar ki ba, kawai dai nayi mamaki ne duk wannan shedun da suka bayyana amma keda Siddiqa kuke san sawa zuciyar ku yadda da Bintu bayan kuma duk irin cika bakin da kika gamayi na ɗaukar fansa akanta,abu na biyu kuma banyi zatan zakiyi tunanin zan iya kashe abinda nake ƙauna da hannu na ba, koda kisan ne sai dai na kashe Bintu dan wannan alƙawarina ne indai Bintu ta auri Abdallah sai na hana rayuwar ta zama lafiya sai ta gwammaci mutuwar ta akan rayuwa,dan haka ki dai na tunanin Ni nayi wannan haɗin babu ruwana wannan macijiyar da take son mamaye dangin mu da salon ta na yaudara to itace ta haɗa komai,dan haka ki cire zargina da kika fara sawa A ranki!'tana gama faɗa ta saki hannun Farida tare da kwanciya saman gadon ta, Farida ta jin jina kanta tare da cewa na yadda da maganar ki Farida saboda nasan bazaki ɓoye min duk wani al'amarin da ya shafe kiba.
Tunda asuba Bintu ta farka sai dai babu ƙarfi sosai a tare da ita, kasan cewar har yanzu bata ci ko mai a cikin ta ba yanzu ma da taimakon ruwan da yasa mata samu ɗan ƙarfin jiki,tana idar da salla ya shigo ɗakin hannun sa ɗauke da wani ɗan madai daicin cop sai madai daicin kwalanda,ajiyewa yayi A gabanta batare da yace"mata komai ba yayi mata nuni da takarya yanzu,miƙewa yayi ya fita yayin da Bintu ta ɗauki cop din nan da yake shaƙe da kakkauran shayi wanda yaji haɗi,tunda ta kafa shi abakinta ba ita ta ajiye ba saida ta shanye shi tas kana ta janyo kwalandar da take ɗauke da soyayya dankali da uban ƙwai sai zabga ƙamshi yake ta hau ci so sai taci tayi ƙat,daga nan kuma ta fara tunanin wanka dan har wani ƙayƙayi taji jikinta nayi saboda rashin wanka,tashi tayi ta shiga haɗaɗɗen banɗakin da sai da taja wasu mintuna wajen ƙauyanci da kalle kalle kafin ta fara gabatar da wankan ta sai da taji fatar jikinta har zafi take saboda gurza haka gashin kanta kana ta haƙura ta fito,kamar wancan lokacin yauma doguwar A baya ta samu saman gadon murmushi tayi tare da cewa,yau dai bazan ce wataran ne kake da kirki ba kana da kirki, kullum kai mai kirki ne mai tausayawa rayuwata Oga Abdallah kai na musamman ne gaskiyar fafina ne da yace" kai zaka zama jagora kuma garkuwa a gareni tabbas na haɗu da mai sharen hawayena,inayin ka ogana over!' tayi waɗi ɗan juyi mai cike da nishadin dake tattare da farinciki.
Shi kuwa Abdallah bayan gama shirin sa Yahya ya kira yace"masa zasuje can office ɗin sirri saboda akwai buƙatar zuwan sa A yau ɗin,bayan gama wayar tasa ne ya koma ɗakin da Bintun take ciki,sai da ya ɗan yi knoc ta bashi izinin shiga kana ya shiga ,cikin wannan yanayin nasa na kirnewa wanda ita a yanzu bai dame ta ba, ya nufi wata durowa kai tsaye taga ya ɗauko magunguna har da allurai cikin sauri ta tashi zata shiga banɗaki, wanda kanta kai ga buɗewa ya danƙo hannun ta cikin zafin nama irin nasa na ƙarfaffan namiji,waro manyan idanunta tayi saboda ita tsoro ma ya bata dan bata san lokacin da har ya ƙara so ba,kwaɓe fuska tayi tana shirin sakin mai kuka saurin ɗora yatsun sa yayi kan jajayen laɓɓansa yayi mata alamar tayi masa shuru,batayi kukan ba amma bata saki fuskar ba, jawo ta yayi ya zaunar da ita gefan gadon,kana ya nufi ɗan ƙaramin frige ɗin da yake ɗakin ya bude ya ɗauko gorar ruwa ya ɓalle maganin ya miƙa mata tare da ruwan,karɓa tayi ta shiga juya sa cikin hannun ta,tunda ya shigo sai yanzu bakinsa ya motsa,Malama kina ɓatan lokaci ina da abinyi!'cikin tura baki tace"to kayi tafiyar ka zan sha!'kawai gani tayi ya shiga haɗa allura, cikin rigimammiyar Muryar ta tace"Ni dai banason allura zansha maganin ko kallon ta baiyi ba ya cigaba da abinda yakeyi,da taga dai da gaske yakeyi allurar zaiyi mata kawai sai ta miƙe zata gudu daga ɗakin, cikin azama ya fizgota ta faɗa jikin sa dama ya gama haɗa allurar riƙe ta yayi sasai ya tsira mata allurar kuka takeyi sosai hadda su kai masa duka a ƙirji amma bai rabu da ita ba sai da ya tabbatar allurar ta gama samun mazauni cikin jininta kana ya saketa yana watsa mata harara,juyawa yayi ya fice yana aiyana rigima da sakalci irin na Bintu A ransa, A nan kan gadon ta gama birgimar ta daga ƙarshe kuma bacci yayi awan gaba da ita.