← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 120

Sashe 86

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Numfashin Bintu kaɗan ne bai zuƙe gaba ɗaya ba dan dai Allah yayi da sauran shan ruwan ta agaba amma mugun tsoro da firgicin da tashiga tsaf zai iya sawa ta haɗiyi zuciya,shi kan sa Abdallah ya shiga cikin firgici amma fa shi ba dan Bintu ba tabbas sai ya ga fuskar wan nan baƙin azzzlumin, cikin rawar baki da jiki Bintu tace"ga..g..gashi nan zai shigo!'ta faɗa tana wani irin jan numfashi kamar ta shiɗe,kamar daga sama taji Muryar matar da take zuwan mata amafarki wadda a yanzu ta gane ba Aljana ce kuma ba mafarki take ba, gani kawai take kamar amafarkin, tana mata magana, kin kakkausar murya tace"Bintu ki kwantar da hankalin ki insha Allah nasara na garemu ki nutsu kiji abinda zan gaya miki!'cikin sauri ta gyada kai duk da cewa ita bata ganin matar,matar ko nace aljanar taci gaba da cewa zan riƙe shi a bakin ƙofar nan amma na wasu ƴan daƙiƙa ne,kuyi gaggawar fita da mutumin nan ku kai shi wani ke ɓan taccen guri!' cikin tashin hankali Bintu tace"kina zan cen fita ta yaya zamu fita bayan yana bakin ƙofar,aljanar tace"zan riƙe ƙofar ne ta yadda zai ja lokaci bai buɗe ta ba,kuma dama ayanzu sihirin sa ba zaiyi tasiri ba tunda kun riga kunga sirrin sa,ɗan abinda yake dashi kuma bazai masa amfani yanzu ba,Bintu ta kuma cewa har yanzu dai baki gaya min abinda nake son ji ba,shin ta ina zamu fita?shi dai Abdallah sake da baki da hanci yake kallon abin al'ajabi agurin matar tasa dan shi kawai gani yayi tana magana amma bai san da waye take yi ba,ci gaba yayi da zubawa sarautar Allah ido,gani yayi Bintu ta bi wani ɓangare daga can lokon ɗakin da kallo tana cewa naga wajen!'aljanar tace"yauwa to a wajen ki duba akwai ƙofar da zata fitar daku har farfajiyar da ake ajiye dukan motocin gidan!'cikin sauri Bintu taja hannun Abdallah har zuwa gaban wannan mutumin da bashi da maraba da ice ta wani bangaren, tana cewa muyi sauri mu fita bamu da ishashshen lokaci!' ba tare da ya tsaya yi mata wasu tambayoyi ba kawai yayi abinda ta umarce shi bai sha wahalar ɗauke mutumin ba saboda babu wani nauyi atare da shi,sai dai kuma wani tashin hankalin da suka kuma riska har yafi na baya,saboda wata irin wuta ce ta fara ci a cikin dakin kamar wadda take jira a taɓa mutumin,kuma da sauri da sauri take ci,cikin wani sabon tashin hankalin Bintu ta nufi ƙofar daniyar buɗewa amma abin ya gagara kuka ta farayi tana jijjiga ƙofar da ko motsi batayi,yayin da wutar take tunkaro su ga kuma Abdallah saɓe da mutumin a kafaɗar sa,wutar na daɗa tun karo su Bintu na ƙara azamar da ɗa buga ƙofar,ji tayi matar ta kuma cewa da ita Bintu kiyi sauri ga can karfen dake jikin bangon gabas shi zaki ɗauka da Bismillah San nan ki buga ƙofar dashi kina ambatan sunan Allah insha Allah ƙofar zata buɗe!'cikin zafin nama Bintu ta tunkari wajen da ƙarfen yake wanda kuma wutar tana gab da isa wajen ƙarfan, Abdallah ne yayi ƙarfin halin cewa Bintu kina da hankali kuwa kina ganin wuta na tunkarar wajen amma kina ƙoƙarin kai kanki!'ba tare da ta saurari abinda yake cewa ba ta isa gurin tana daukar karfen, wutar na kamawa awajen cikin sauri ta matsa daga gurin ta koma bakin ƙofar tare da yin Bismillah ta daki ƙofar da ƙarfi tana ambatar sunan Allah cikin ƙudura ta Ubangiji ƙofar ta buɗe, tamkar walƙiya haka suka bar wajen wanda kuma suna fita ƙofar ta koma yadda take tamkar ba ataɓa taɓa ta ba,hakan ke da wuya kuma baƙin azzzlumin ya antayo cikin ɗakin tare da fara zazzare idanun sa yana bin wutar dake daɗa ruruwa da kallo,wanda hakan yake tabbatar masa da cewa mai faruwa ta gama faruwa, zubewa yayi a ƙasan wajen daɓas baiƙi alokacin nan wutar ta haɗa dashi ta cinye ba, tashin hankalin da yake ciki ba zai misaltu ba a wan nan lokacin,ya kasa yin komai banda zubawa wajen da ya ajiye ABUBAKAR da yayi da idanu ko ƙiftawa ba yayi,maƙoshin sa kuwa ya kasa haɗiye koda miyau ne.

Wucin da ya rufe fatar jikin sa da wani irin zafi me shiga ɓargon jiki shine ya ankarar dashi halin da yake ciki,cikin sauri ya fita daga ɗakin zuciyar sa in banda balbala da wuta babu abinda take yi,yana fita daga gurin kuwa wata irin wuta ta mamaki ta mamaye dakin,wani abin al'ajabi kuma iya gurin ne kawai yake ci da wutar duk da cewa da akwai motoci ta bayan dakin, zubawa ɗakin ido yayi idanun sunyi wata irin kala tamkar garwashi,kamannin sa har sauyawa sukayi saboda tsananin ɓacin rai da tashin hankali, ƙoƙari yayi ya bar wajen tun kafin asirin sa ya ƙarasa tonuwa.

Wata irin ƙaƙƙar far ajiyar zuciya Bintu ta saki lokacin da taga sun fita daga cikin ESTATE din lafiya ba tare da sun hadu da wata tuhuma ba,shigewa tayi jikin sa tana fidda wani numfashi wanda kana jin sa kasan na wahala ne,runtse idanun ta tayi saboda zugin ƙonuwar da sai yanzu tasan tayi ta ta ratsa fatar ta,A hankali yasa hannun sa guda ya shafa kanta da duk ya hargitse saboda wahala,zuciyar sa kuwa cike take da tausayi da tarin tambayoyi,agame da wannan al'amarin da yafaru akan idanun sa,ɗan zamewa tayi daga jikin sa dan san bashi damar ci gaba da tuki cikin nutsuwa,sai dai duk sakan da sai ta duba bayan ta dan tabbatar da cewa yana nan,gani take kamar har yanzu basu tsira ba,kamar za a iya ƙara ɗauke shi ta hanyar tsafi,amma idan ta tuna da cewa Allah yana tare da su kuma nasarar tasuce sai hankalin ta ya ɗan kwanta,tafiya suka ɗanyi mai nisa kana taga sun ƙara so wani ɗan madaidaicin gida mai kyau mota ma batafi biyu ce zata iya shiga farfajiyar gidan ba,fita yayi ya buɗe get ɗin kana ya dawo yaja suka shiga,

Ga mamakin su sai kuma sukaji yanzu yayi nauyi bakamar da farko da Abdallah ya ɗauke shi ba,hakan yasa Abdallah ya ɗauke shi da nishi,a hankali suka shiga cikin madaidaicin falon da babu wasu kayan tarkace idan ka ɗauke tv da ec sai frige da kujeru, bai tsaya ba sai da ya dangana da can ƙuryar ɗakin dake cikin falon anan ya kwantar da mutumin da har yanzu bai san waye shi ba,tsayawa sukayi akan sa tare da zuba masa ido,tsuguna wa Bintu tayi agaban sa cikin fidda zafafan hawaye tasa hannun ta ta fara goge wan nan abun mai kamar yana ajikin sa da fuskar sa,cikin kukan da ya tsanan ta agareta tace"Allah sarki rayuwa ke nan yanzu ɗan uwanka ma sai ya zama abin farmaki agareka,ko kai ka farmake shi ko shi ya farmaki rayuwar ka,tabbas Dady kaga rayuwar da bantaɓa ji ko ganin irin ta a duniya ba,to amma hakan ba wani abune na mamaki ba duba da yadda duniyar ta koma duk abinda kake zaton ba zai yiwu ba yanzu shi yake yuwuwa, abubuwan al'ajabi da ɗaure kai su suke ta faruwa yanzu,sai dai muyi fatan Allah ya shiga tsakanin mu da shaidan ya kuma tsare zukatan mu da shiga mummunan rayuwa!'tana faɗa tana cigaba da yaye abin daga kan fuskar sa, Abdallah dama yaya lafiyar kura ai faruwar wannan lamari sai ya ƙara kurumtar dashi domin shi kansa so yake yaga yace wani abu amma hakan ya gagara,ga kuma tambayoyi fal aransa.

Zama ko makaman cin haka bai same shi ba,tabbas yasan babu waɗan da zasuyi masa irin wannan muguwar ɓar bar sai yaran nan,wai ma tun asali mai yasa shi kasa ɗaukar mataki akan su?me yasa baiyi ƙoƙarin ganin bayan su ba?bazan taɓa barin ku kutona min asiri acikin ESTATE ɗin nan ba,bazan baku wannan damar ba kunyi naku kun gama saura nawa wallahi babu wanda zan ƙyale acikin ku kaf sai na ƙarar daku,saboda tsabar baƙin ciki baisan sanda wani kuka ya kece masa ba mai tsananin karfi da fitar da wani amon sauti wanda yake cike da abubuwa na bakin ciki masu tarin yawa.
Chapter 86 · 0% Book details