← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 120

Sashe 11

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da akayi shekara hudu da bacewar laila nima na fara fuskantar tawa matsalar,ni dakaina nayi tunanin mubar rugar baffa jauro, ko muna kusa dasune bamu sani ba, baffa shine yabani kudin da nazo na sai wannan dan gidan da muke zaune ya kuma bani kudi yace nayi wata yar sana ar kuma nasakaki amakaranta shi yabani shawara da muyi nisa da yola ko zamu samu nutsuwa, haka kuwa akayi baffa yasa nayi shigar da zan badda kama saboda samun akasi yakuma samo mana babur wanda zai kaimu har babbar tasha,munyi kuka sosai na rabuwa karma ke kiji labari dan har numfashin kine yake daukewa, dan alokacin shekarunki goma sha uku dan haka baki taba mantawa da baffa jauro ba kusan kullum sai kince na kaiki gurinsa da kyar nasamu kika daina yi min zancansa amma nasan badan kin manta dashi bane

Bauchi shine garin da muka kuma Allah yasa na hadu da mutum me amana me suna gali, shiya kaimu gidansa har yasamo mana wannan gidan ya kuma bani shawarar abinda zanyi da dan jarin da baffa jauro ya bani yace na siyo kayan gwari kamar su mango data goba duk dai abinda yake lokaci, haka kuwa akayi, lokacin gobane da data dan haka su nake sai dawa, na kuma sami makaranta mai kyau nasakaki lokacin kina da shekara goma sha uku kasan cewar mun riga munyi miki kyakykyawan paundation kai tsaye aka kaiki aji uku na secondary nan dinma kawai an barkine dan ilminki yafi karfin aji uku.

Ahaka muka dinga gungura rayuwar mu har kikayi candy wato ssce, ta bangarena wadannan mutanen suna ta bibiyata sai dai bantaba gaya miki ba saboda banasan damuwarki,
alokaci daya kuma rayuwar ta tsaya mana cak dan jarin da nake tattalawa ya kare sai yawan rashin lafiya da nake Wanda duk baya rasa nasaba da irin ukubar da nakesha agun wadan can azzaluman kuma Nima sun sha alwashin sai sun rabani dake tunda na zame Miki katanga bayan su so suke su ga rayuwarki ta lalace shi yasa duk wanda take baki kariya sai sun ga bayansa dansu abatan basirarsu da duhun kansu indai babu wani garkuwa atare dake to hakkun zasu ci galaba akanki anasu karatun kenan anamu kuma basu san cewa Allah shine garkuwar bawansa kuma majibancin al'amuran sa lokacin da nake ta tunanin zuwansa bintu Ina ganin yakusa zuwa na dade da rubuta wannan sakon naki bintu dan nasan watakil alokacin da nakeso na sanar miki hakan bazai samu ba.

Abu na biyu shine bintu Ina yawan sanar dake akwai wanda zai zamar miki jagora to tabbas naji ajikina zaku hadu kince na sanar miki waye? akuma ina yake? to ni kam duk bansan wannan ba!' hasali ma bantaba ganin fuskarsa ba andai nuna min shi amafarki na kuma inasa ran haduwarku insha Allah danshima yana bukatarki dan hada karfi da karfe ku tai maki junanku!'

Abu na uku shine inda zaki nufa, to daga nan, ki wuce abuja duk yanda zaki ki samu koda aikine a estate din Alhji balarabe, Ina da tabbacin cewa duk wani abu yana cikin gidan nasan da wannan ki nutsu bintu karki sake ki nunawa wani ke din ahlin gidance, duk yanda zaki shaku da mutum karki yarda ki bashi yaddarki duk wanda kika gani ko shiga gidan yayi saka masa ido harsai kintabbatar da gaskiyarsa sannan ki barshi kuma kiyi hakuri da duk abinda zaki gani kibi ko mai asannu harki tadda gaci,akwai rudadden al'amari awannan ahlin dan haka kiyi taka tsantsan dan sai kin nutsu kinbi hanyo masu bullewa kafin ki fahimci komai mutanen gidan suna da ruda mutum, kuma ina da tabbacin mafarautanmu suna hade da alhlin gidannan.

Bintu tana kawowa karshen bayanin fafi ta saki wata sassanyar ajiyar zuciya,tare da wani kuka me cike da shauki bege da kuma kewa data mamayeta, wani irin kewar fafi da mamanta ne suka hadu suka da baibaye zuciya da ruhinta, tanaji dolene ta shiga koma inane dan nemo fafinta da mamanta, kowane hadarine zata iya fuskantar sa indai akan wadannan mutanen guda biyune, ashe fafi bashi ya haifeta ba amma ya sadaukar da rayuwarsa ya bar iyalansa da mahaifiyarsa da dukiyarsa da abokansa yan'uwansa da komai nasa, kawai dan ya tserar da rayuwarsu ita da mamanta, shiko fafi wane irin mutumne haka da irin wannan babbar sadaukarwa?me zatayi arayuwarta dan saka masa da dinbin alkhairin da yaiwa rayuwarta? wani shashen na zuciyarta yace"fatima baki da abinda zaki iya sakawa fafi dashi arayuwarki sai dai ki bishi da addu'a da kuma binciko inda aka kaisu aka boyesu, da kuma rusa magautanku kamar yadda ya gaya miki, hannu tasa tashare hawayen da suka ki daina zuba daga cikin idanunta, kana ahankali ta bude wani page, dan taga kamar da wani sauran rubutu, aiko hasashenta ya zama gaskiya, ga abinda yace mata, bintu ki duba cikin kayana zaki ga kudi dubu biyarne na dade ina tarasu domin irin wannan ranar ki dauka kiyi kudin mota duk da nasan da.wuya zai isheki Amma dai nasan zai kaiki Abuja kuma kisamu ki danci abinci, Allah yabaki sa'a ya kuma kareki daga duk wani sharri ya kuma hadaki da mai taimakonki cikin sauki, Allah ya yiwa rayuwar ki albarka.

Fatima ta kuma rushewa da wani rikitaccen kuka mai taba zuciya,duk wanda yaga halin da bintu take ciki awannan lokacin indai yana da imani da tausaiyi dole ya zubda mata da hawaye,tayi kuka tayi kuka har ta gaji sai wani irin masifaffan ciwo da kanta keyi mata tamkar zai tsage gida biyu,ahaka ta hakura ta lallashi kanta da mika dukkan lamuranta ga sarki Allah buwayi mai iko da komai,tare da fara kokarin shirin fuskantar gagarumin yakin dake gabanta.

......Abuja......

Kwanaki uku yayi cir yana istihara dan neman zabin Allah akan akan yakin da yake kokarin fuskanta,kuma alhdulillah yaji hankalinsa ya kwanta tare da samun kwarin gwiwa na shiga cikin ahlin Alhaji balarabe.

Acikon kwana ukunne yagama shirinsa tsaf dan komawa estate din, dama dady ya kaimasa duk kayansa da kuma duk wani abu nasa mai muhimmanci tun kafin yau din tazo,dan haka yana tashi daga aiki ya nufi gida dan yiwa mom sallamar da taci albarkacin dady, da farko baiyi niyar yi mata sallamar ba, amma da yayi wani tunani saiya ga bai kyautatawa dady ba amatsayinsa na wanda yake ta kokarin dai-dai ta rayuwarshi da tarin kyautatawa da neman mafitawa rayuwarshi.
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

```Page 10 ```

Koda ya shiga falon mom din zama kawai yayi batare da ya iya cewa da ita komaiba,sam shi baisaba da yin magana anyhow ba, shiyasa take matukar yi masa wahala har ga Allah sautari rasa abin cewane yake hanashi magana, kamar misali dady awasu lokutan yanaso yayi mishi magana kodan nuna masa irin jin dadin da yake shiga duk lokacin da yaga yana kokarin kawar da damuwar dake dankare azuciyarsa, sai dai kuma yana rasa tayaya zai iya hakan.

Zuba masa ido tayi tana mamakin hali irin nasa, wai ace mutum da ransa da lafiyar sa amma sai yay awa biyu cur batare da ya bude baki yay magana ba, idan ma zaiyi bata wuce kalma biyu zuwa uku anya kuwa fatash zai iya rayuwa da mace?shin wace irin macece zata iya zama da fatash da wadannan halaye nasa?to shi tayaya ma zai iya wata soyayya?ita tana ganin ma bazai taba yin aure arayuwarsa ba tunda babu wanda ya ke shakka ko tsoro da zai tursasashi yayi auren, sai dai yay tazama ahaka tunda ya riga ya auri aiki, mom ita kadai da zuciyarta take mitar nan tare da cin alwashin bazata tanka masaba ko zasu kwana ahaka har sai taga iya gudun ruwansa.

Banza tabawa ajiyarsa kamar yadda ta kudurta aranta,sai dai kuma abun neman fin karfinta yake, dan bata ga alamun yana da niyar tanka mataba, saima kokari yake ya bar falon saboda yasan dady ayanzu shi yake jira, saurin dakatar dashi tayi da cewa"haba fatash sai kace wadanda suke zaman gaba me yay zafi haka!' kake tsaurara tsanarka agareni?kai kana ganin ya kamata ka tafi wani guri zama na tsawon wani lokaci batare da munyi sallama wa juna ba?ya kamata ka sassauta min nasan ni mai tarin kuskurece agareka amma ai na nemi yafiyarka kuma kace kaimun afuwa!' to meye kuma acikin ranka game dani haka fatash?
ta fada tana mai sakin wani dan marayan kuka gwanin tausayi.

Ahankali ya koma ya zauna yana mai hada hannayensa biyu tare da lan kwasasu cikin kwarewa da sabo, suka bada wani sauti kakasss!' kana ya dubeta cikin dauriya yace" mom sorry and please forgive me, ni zan wuce Allah kaddara saduwarmu!'daga haka bai iya kara koda harafi daya ba yasa kai ya fice batare ya waigo ba.

Sake da baki da Ido ta bishi, to meye amfanin neman yafiyarta ta?batare da ya saurari abinda zatace ba yai ficewarsa, ga tarin tambayoyin da tayi masa duk ya hada ya share tamkar ma batayi masa suba, ita dai tanaso taga ranar da za aiwa fatash tambaya ya amsa kai tsaye,wani lokacin idan kanasan amsar tambayarka agunshi sai dai kakula da aiyukanshi' a kanka ta nan ne kawai zaka gane amsarka amma ga wanda yasan hali.

Acikin mota ya sami dady shi kadai, dan basa bukatar driver awannan gabar,yana shiga dady ya tayar da motar yaja me gadi ya wangale musu wawakekiyar kofar get din suka fita.
Chapter 11 · 0% Book details