Sashe 49
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Hannun tane ya fara rawa saboda tsabar ruɗanin da maganar Alhaji Baba ta saukar mata, ji tayi tamkar an ɗora mata wani gungume man dutse akanta,wai dama da gaske Alhaji Baba yake ita zai ɗaurawa Oga Abdallah?anya kuwa wannan haɗin yayi?ya zatayi da farmakin Taufiƙa? Sannan taya zatayi ta cimma burin ta alhalin da igiyar Aure akanta?shin Abdallah zai tallafa mata kamar yadda fafi yasanar da ita?idan kuwa har zai tallafa mata to kuwa dole ta haƙura da Auren sa domin shima wata babbar dama ce agareta, wannan muskilalliyar Muryar tashi me tsananin daɗi ce ta katse mata tunaninta, Alhaji Baba mun gode Allah ya ƙara girma da lafiya,in Sha Allah zamuyi maka biyayyar da zakayi alfahari damu!'kut kaji wai zamuyi wannan ai aran baki ne,wato yau darar Alhaji Baba zaiyi dan tasan wannan muskilin ba abinda ya iya banda nunƙufurci da tsirawa mutane allura,duk gungunin da take da zunɓura baki akan idanun sa dan salon kallon Abdallah abin burgewa ne amma ga Bintu wanda shi kansa bai san yanayi ba,(amma koni alƙur an kallon na bani citta)Alhaji Baba yace"to masha Allah Ubangiji ya yiwa rayuwarku albarka ya baku zuri'a me albarka, Allah yasa wannan Aure ya kasance fitila ga rayuwar ku! da Amin suka amsa kana Bintu ta miƙawa Alhaji Baba kuɗi tare da cewa, Alhaji Baba kabar kuɗin nan Ni ban san me zanyi dasu ba!'yace"a'a Bintu wannan haƙƙin kine dole ki amsa idan yaso ga mijinki nan sai kibashi ya ajiye miki!'gyaɗa kai tayi kawai batare da ta kuma cewa komai ba,har zasu miƙe Alhaji Baba yace"au na manta ban tambayeka ba zaka zauna a gidan nan ne ko zaka tafi da matarka wani gidan daban? Abdallah ya ɗan rusuna yace"zamu cigaba da zama a ɓangare na har muga abinda Allah zaiyi!'hakan yayi kyau kuje Allah Ubangiji yayi muku albarka!'suka amsa da Amin kana suka fita daga falon, murmushin farin ciki Alhaji Baba ya saki tare da binsu da kyawawan addu'oi.
Tarbar da Inno tayi mata ita tasaka kuka wanda dama a kusa yake,rungume ta tayi sosai tana ɗan bubbuga bayanta,cikin kalaman lallashi take cewa haba Batula to kuma meye na kukan bayan kina kusa dani, dan ban shiryawa rabuwa dake yanzu ba sai nayi miki biki irin na yargata amma ba yanzu ba akwai lokacin yana nan zuwa,idan kuma zan haɗa da suna ne shike nan!' Abdallah harara ya watsawa inno kana ya shigewarsa ɓangaren sa ya barta ita da sakalalliyar Bintun ta,hannun Bintun ta kama ta isa da ita har ɗakin ta da kanta ta haɗa mata ruwan wanka wanda sai da Bintu ta shiga taga kamar ba zallar ruwa bane dan sosai yake wani irin fitinan nan ƙamshi mai kama jiki da zuciyar wanda aka raɓa,sosai taji daɗin jikin ta, kwanciyar ta tayi saman tattausan gadon ta,ko minti biyu batayi ba wani nannauyan Bacci yayi awan gaba da ita.
Tunda ya shiga ya gabatar da abubuwan da suka zama farilla agareshi, har ya kwanta saboda gajiyar dake tare dashi sai kuma wata gagarumar yunwa ta motsa masa, dan sai yanzu ya tuna rabon sa da abinci me nauyi tun kan wannan abin ya faru sai ƴan kame kame da yake dan bayajin zai iya cin kowane irin abinci idan ba na Bintu ba,ɗan tsaki yayi tare da tashi zaune ya dafe kansa dake ɗan sara masa,wayarsa ya ɗauka ya danna lambar inno bata jima ba kuwa ta ɗauka tare da yin sallama,amsawa yayi kana cikin takurawa kansa da magana yace"inno kisa yarinyar nan ta dafo ko noodles ne ta kawo min yunwa nakeji sosai!'inno tace"ai inaga sai dai Ni nayi maka dan Bintu tayi bacci!'ki tasheta inno yanzun nan!' saurin dafe kansa yayi saboda shikan sa bai san ya akayi ya faɗi hakan ba cikin san kawar da waccen maganar yace"inno bana son ki wahalar da kanki kawai ki tasheta bata da magagi!'murmushi inno tayi tare da cewa to gaskiya bazan sa ta girki daga farkawar ta ba sai dai idan na dafa maka in yaso na tasheta ta kawo maka, hakan yayi maka?shike nan inno yayi!'daga haka ya kashe wayar batare da yasan irin mamakin da yabar inno dashi ba,duk wanda yaga Abdallah ko yaji kalamansa dole zai gane halin da yake ciki amma a yadda ta lura sam shi bai san yanayin duk wannan ba,bai san yadda al'amuran sa suke tona asirin zuciyarsa ba,wani ƙawataccen murmushi ta saki gami da yunƙurawa dan zuwa kiching ɗin.
Cikin bacci taji kamar ana tashin ta, cikin nutsuwa ta buɗe manyan idanunta da a yanzu suka bada wata kala ta musamman saboda baccin dake cikinsu,inno tace"yi haƙuri Bintu ta shi ki kaiwa Abdallah abinci, waya ya yimin yana jin yunwa!'tura baki tayi gami da gyara kwanciyar ta zata cigaba da baccin ta,inno tayi saurin ruƙota cikin lallami tace"haba Bintoton inno kinga fa cewa yayi na tasheki ki dafa masa amma saboda kar na tasheki sai ni nashiga kiching ɗin,kuma kin san dai halinsa tsaf zai biyoki har nan idan baki tashi ba!miƙewa tayi tana gunguni,ga bacci fal idonta amma saboda mugunta ance tana bacci wai atasheta,karɓar tiren da Inno ta zuba abincin tayi ta zura silifas saboda ba dai dai take ba sam ta manta da kayan da ke jikinta,ita kuma inno batace ta canja ba saboda taga cikin bacci take.
Wani irin kuka ne ya kufcewa Taufiƙa lokacin da taga shigarta falon Abdallah daɗin abin baƙin cikin kuma kayan baccin da suke jikin Bintu wanda ko ita mace idan tacire hassada da kishi tabbas sai ta burgeta,gashi dai kayan ba wani nuna tsiraici sukayi ba amma yadda doguwar rigar mai shegen sulɓi da wani irin shep tabi lafiyayyan dirarran jikin Bintun shine abin kallo da burgewa, Siddiqa ce tayi saurin janye ta tare da toshe mata baki suka koma cikin ɗakinsu, Siddiqa tace"sai kin kawowa kanki maganar inno wadda itace zata iya fasa ƙahon zuciyarki!'cikin kukan fitar haiyaci Taufiƙa tace"wallahi bazan iya ba bazan iya kallon wannan macijiyar tana yawo tare da abinda nafi ƙauna arayuwata ba, tabbas Bintu kin janyowa kanki rigima da tashin hankali mara karshe dan sauna salwantar da rayuwarki!'
Bintu baiwar Allah bata san ma tanayi ba, ita haushin ankatse mata baccin ta a yanzu shi yafi damunta,dan haka da haushin ta faɗa falon bata ganshi anan ba,dan haka cikin sauri ta ajiye tare da juyawa dan barin falon,cikin ƙasaitacciyar muryar sa yace"nan zaki kawo min!' ashe har yaji shigowarta kuma yana da yaƙinin abinda take shirin yi, Ai kuwa buɗe ƙofar ɗakin da yayi yaga tana sanɗar ajiyewa,da sauri ta ɗago ta ɗan dubesa kana ta duƙa ta kuma ɗauka ta biyo shi ɗakin babu abinda takeyi azuciyarta sai mita,tana shiga ta ajiye zata kuma fita nan ma dakatar da ita yayi da cewa ki tsaya ki tafi da kayan dan bazan kwana da ƙazanta ba!'ƙazanta kuma lallaima wannan mutumin wato kwanikan ne ma ƙazanta?kallonsa take cike da takaici saboda yadda ya basar kai bakace shiyayi maganarba, A hankali ta samu guri ta rakuɓe tana jira ya gama yangar cin abincin nasa.
Wucewar mintuna huɗu zuwa biyar ya ɗan saci kallon ta sai yaga ta sheme ta cigaba da baccin ta hankali kwance,samun kansa yayi da zuba mata rikitattun idanun sa wanda har baisan iya tsawon lokacin da ya ɗauka yana binta da kallon ƙurilla ba,ɗan ƙaramin bakinta ya tsirawa ido haka nan yadinga jin wani abu na ratsa zuciyarshi wani irin mutuwa jikin sa yayi har wani sanyi-sanyi ne ke ratsa cikin jikinsa, lumshe idonsa yayi daga kallonta yayin da yarasa abinda ke damunsa wanda shi dai yasan bai taɓa jin Irin wannan yanayin tare dashiba,ɗan tsuka yayi tare da tashi ya shige toilet sabon brush yayi kana ya fito ya ɗauke kayan ya fita dasu kan dining table ya ajiye,