Sashe 33
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Cikin mutuwar jiki ta gama haɗa masa karin kumallo,sai da ta gama komai ta jera,kana ta samu guri ta raɓe kamar munafuka,bata motsa daga inda take ba har ya dawo daga motsa jiki ya shiga ya shirya ya fito tsaf dashi tamkar wani fure sai ƙamshi yake zabgawa,sumar nan ta kwanta tayi luf sai ƙyalli takeyi, nan ma dai yayi mamakin ganinta amma sai ya share ta ya nufi dining,har ya gama karyawa bata tashi ba sai dai ido datake binsa dashi,ɗaki ya koma ya ɗauko jakarsa ya fito,zuwa yayi ta gabanta zai wuce, tayi saurin tashi tasha gabansa,idanunta cike taf da hawaye,tsayawa yayi yana kallonta cike da mamaki,har zai kuma wucewa sai kuma ya dakata jin ta biyoshi cikin ƙosawa da ganin yanayin da take ciki yace"lafiyarki kuwa? cikin kuka tace"karka fita zasu kasheka wallahi naji da kunnena suna faɗa jiya ta bayan ɗakina!'wani kallo yabita dashi kana A hankali ya taka ya koma ya zauna cikin kujera dubanta yayi da lumsassun idanunsa kana cikin taushin murya yace"zonan!'cikin sanyin jiki ta ƙara so inda yake ta durƙusa,A gabansa cikin nutsuwa sai dai fuskar nan a haɗe take ka tamau babu alamun ya taɓa sanin yadda ake murmushi,yace" ina jinki ki nutsu kiyi min bayani banason bana son hawayen Nan!'
Samu tayi ta dai dai ta nutsuwar ta da ƙyar kana tace"jinayi suna cewa za'a sace tayar motarka da zaka fita da ita kuma ina tunanin sun sace"saboda alokacin umarni ake badawa da aje a sace!'cikin san tabbatar wa, yace" zaki iya shaida muryoyinsu?girgiza kanta tayi tare da cewa Ni ban taɓa jin muryoyin ba!'jin jina kansa yayi tare da cewa tashi ki tafi!'ɗan kallonsa tayi amarairaice,kamar zata fashe da kuka,bai ce mata komai ba ya ɗauki wayarsa saboda ya fahimci abinda take nufi,wayar yakara A kunnensa,jim kaɗan yayi magana,kakawo mota yanzu ina jiranka!' daga haka ya kashe wayar tare da maida idanunsa ya lumshe,ganin haka yasa ta miƙe A hankali ta fita daga falon ta ƙasan ido yabita da kallo har ta fice,
Duban samuyal yayi bayan sun shiga office ɗinsa,yayi masa alamun yana sauraren sa, samuyal ya ɗan gyara zamansa kana yace sir wannan gida na Alhaji Nasir ne kuma an ta nade shine saboda zaman mitin da sukeyi idan hakan ta taso!'ya miƙa masa wata doguwar paper yana cewa ga bayanan waɗanda suke mitin ɗin da jerin sunayensu!'karɓa yayi tare da jinjina wa samuyal,daga nan kuma ya bashi umarnin tafiya da cewar sai ya neme shi.....
Comment.....
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœðŸ¼*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ðŸ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 24 ```
Babbar mace ce, wadda baza ta gaza talatin da hudu ba,kyakykyawa ce bata da wata makusa,tana da kyawun jiki shiyasa idan ka kalleta zakayi tunanin bata kai shekarunta ba,A hankali ta zauna kan kujerar dake fuskantar sa,kana cikin girmamawa A matsayinsa na oganta,ta gaida sa,dubanta yayi cikin nutsuwa yace"Anty Samira ga wannan fayal ɗin kije ki duba shi ,A nutse,banaso A samu kuskure,saboda wannan aikin da zamu fara yana da ban banci da sauran aiyukan da muka saba fuskanta dole yana buƙatar shiri da kuma addu'a aikin yana da haɗari Anty Samira sai mun kula gaba ɗayan mu!'Samira ta ɗan ja dogon numfashi kana cikin nuna sadaukarwa tace"karkadamu sir,kafin na fara aikin nan nayi alƙawarin babu abinda zai tsoratani naji na karaya na sadaukar da rayuwata wajen kare rayuwar al umma dan haka zan je na duba insha Allah baza asami matsala ba!jinjina kansa yayi cike da gamsuwa,kana yace" shike nan zaki iya tafiya!' sallama tayi masa gami da fita daga office ɗin,shima kiran Yahya yayi,dan yana son shiga asibiti.
Lokacin da ya dawo gidan A ɓangaren sa ya sameta duk da bai dawo da wuri ba yayi mamakin abin da ya hanata kammala girkin da wuri amma sai bai bawa kansa damuwa ba ya barshi kawai a yanayin yau da gobe,ita kuwa Bintu ba komai ne ya hana ta girkin da wuri ba sai ciwon marar da yake ɗan tsun kulinta Lokaci zuwa lokaci,A dai dai lokacin da take shirin fita daga falon mararta tai wani irin murɗawa da sauri ta durƙusa gami da riƙe cikinta yayin da gaba ɗaya ƙafarta ta riƙe katamau sai wani irin danƙa da marar take mata,abinka dama da wadda kuka baya mata wahala tuni fara rera abinta,yana fitowa yayi karo da sautin kukanta girgiza kansa kawai yayi yana mamakin yadda sam kuka baya mata wahala,zama yayi yaci haɗaɗɗen danbun shinkafar da yaji zogala da kayan haɗi sai zabga ƙamshi yake,sai da yaci yay ƙat kana ya kora da kunun ayarsa me shegen ɗaɗi goge bakinsa yayi da tishu,kana cikin yanayin takunsa na isassun maza masu kwarjini da haiba ya taka har zuwa kan luntsumemiyar kujerarsa,wani irin zama yayi mai cike da burgewa kai komai Abdallah yayi sai yayi masa kyau komai nasa abin burgewa ne, cikin wani irin salo mai cike da burgewa,ya zuba mata lulu eyes ɗinsa masu haske da sheƙi,jin idanunsa na yawo ajikinta yasa ta ƙara sautin kukan ta tana mai jin haushin yadda ya shareta,to ba sai ya tambaye ta abinda yasa ta kuka ba amma ya mata shuru sai kallon da ya ishe ta da shi kamar wani maye,jin ya ɗan lafa mata yasa ta miƙe A hankali zata lallaɓa ta bar masa falonsa inyaso sai yaci kansa,wani irin rawa ƙafarta ta shigayi yayin da marar ta kuma juya mata ai batasan lokacin da tasaki ƙara ba gami da zubewa ƙasa tana wani irin juyi wanda yake nuni da tsananin azabar da take sha, A hankali ya miƙe cikin takunsa na nutsuwa ya isa inda take kwance tana faman juyi,wani ɗan tsuguno yayi na burgewa A gabanta,kana cikin kamilalliyar muryarsa yace"me yasa ki kuka? duk da halin da take ciki amma hakan bai hana ta jin haushin tambayar tasa ba,har sai da ta ɗan yi musu-musu da bakinta tana ɗan murguɗa shi,sharewa yayi kamar baiga abinda tayi ba,idan bazaki magana ba ki tafi min A falo kin dameni da ihu!'ƙasa ƙasa ta wulla masa wani shu'umin kallo wanda ita aganinta hararace,ganin ya tashi zai bar gurin yasa ta kuma sakin ƙara wadda har sai da tasa ya runtse idanunsa,har ya rasa me Yakamata yayi,dawowa yayi tare da miƙa mata hannunsa batare da ya dubeta ba, cak kukan nata ya tsaya,yayinda ta ke bin hasken tafin hannun nasa da wani irin kallo,kusan sakanni ashirin kafin a hankali ta ɗaga hannunta ta ɗora bisa tafin nasa hannun,kamawa yayi ya miƙar da ita tsaye ,kana ya shiga takawa A hankali yana nufar ƙofar fita da ita,wani irin kallo take bin kwantaccen gashin da ya ƙawata ƙeyarsa dashi har bata san ya akayi ta shiga taka ƙafar data riƙe saboda ciwo ba,
Bashi ya tsayaba sai da ya dangana da ƙofar ɗakinta kana A hankali ya saki hannunta ya juya ya barta A tsaye,saida ta ga yashi ge falon sa kana ta ji ciwon ya dawo sabo, komawa cikin ɗakinta tayi ta waɗa kan gadonta tana juyi,tsit tayi lokacin da taji alamun an shigo ɗakin,ɗago kanta tayi cikin yanayin jin ciwo,ɗan lumshe idanunta tayi kana ta buɗe su A hankali ta zuba su kan kyakkyawar fuskar sa mai cike da kamala,ta kowa yayi har gaban gadon,kana ya miƙa mata robar ruwan dake riƙe A hannun sa,karɓa tayi ya kuma miƙa mata wasu magunguna, suma karɓar tayi sai juyasu take A hannunta ta kasa sha, dan tsakanin magani da allura bansan wanda Bintu tafi ƙi ba,ganin taƙi shane yasa ya ɗan zaro mata idanu wanda dole yasa ta runtse idanunta ta afasu A baki,da farko kamar zatayi amai sai kuma ta koma tana maida numfashi,atunaninta juyawa zaiyi sai taga yana haɗa allura,tofa anan akeyinta cikin rawar murya tace"Ni ba sai an yi min allura ba naji sauƙi!'bai kula ta ba ya gama haɗa allurar,yay mata alama da girarsa data gyara zaiyi mata,tura baki tayi tana magana ƙasa ƙasa,mutun duk abinda zaiyi sai ya haɗa da mugunta,ga kuma bazai yi magana ba sai dai komai yayi wa mutum alama kamar wani bebe shi ko gajiya bayayi da rashin magana,bata aune ba sai jitayi kawai ya riƙe hannayen ta duka biyu yana ƙoƙarin tsira mata allura,wani irin zillo tayi sai gata gaba ɗaya A cikin jikinshi hakan kuwa ya bashi damar riƙe ta gam ya tsira mata allurar,ƙanƙame shi tayi tana kuka wanda harga Allah kukan zafin allurane, yana gama yi mata ya tura ta saman gadonta,ya tashi ya bar ɗakin yana mai jin mamakin sangarta da tsoro irin nata,ko ta yaya zata iya taɓuka wani abu da wannan shegen tsoron,