Sashe 99
Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
baki Saratu tayi cikin azaba tana dukar dakai, wani dukan ta kaiwa Nas tana fadin, "marar Imani da tausayi iliminki be amfanar dake komai ba Wlh jahilin Kare ma yafiki" ta karasa mgnr tana bugunta a baya, officer ne ya riko Hajjaju data fara haukace musu sai dimar su take a baya Kamar ta samu jakkai yace, "kiyi hakuri Hajia a Gama Abinda ya kawo mu daga Nan sai adau hukuncin daya dace" Hajjaju na huci tace, "daka Barni na huce takaicina Akan wa'annan mugayen" hakuri ya sake Bata badan taso ba kuwa ta koma ta zauna, zamanta keda wuya H.o.d ya shigo Yana tmbyr wacece matar a ciki? Nan aka sake nuna Masa Saratu, gabanta ya Isa dakyar ya samu nasarar diban jininta Dan gaba1 jikin Saratu ba Abinda yake sai rawa ko kadan ta kasa hada Ido dasu sai kyarma take, Hajjaju Tace, "ahaff ai daga yadda take Wannan kyarmar kowa yasan cewa Wannan bakin Dan nata ta aje Mana a Matsayin namu saikace Aljana masu musayar Dan ruwa" Sageer da yake bin Saratu da wani matsiyacin kallo cikin tsawa yace, "ke dallah mlm ki daina yiwa mutane Wannan kyarmar jikin Nasan Wannan duk acikin tsarin kune nason hada baki a cuceni Kuma Wlh..." "Shut up...Sageer" daddy ya Fadi hakan da Dan tsawa take Sageer ya tsuke bakinsa Yana Harare Harare, Saida aka dauki lkci me tsawo kafin h.o.d ya nufo office dinsa shi da Dr. Sadeeq dake manne dashi har yanzu yaki barin sa Dan Yana tsaye akai komai akan idonsa yyinda can cikin zuciyar sa yake Addu'a da fatan zancen Abba ya tabbata, suna shiga kuwa daddy ya Mike kirjinsa na harbawa, shi kuwa Abba murna ce ta Kama shi yanzu dai za'ayi me kankat, bangaren su mummy kuwa Suma kirjinsu be daina harbawa ba sai zabga Addu'o'i suke, Safna Kamar tayi kuka sbd shiga rudani. Kallon takardar hannun sa h.o.d Bala yyi Yana Kara gyarasu, Dr. Omar dayaga Haka shima mikewa yyi Yana me harde hannayen sa ta baya yyinda Sageer ya shiga ci gaba da kada kafa Yana 'yar dariya Dan yasan shine a sama, Saida h.o.d Bala ya Gama gyarasu kafin ya dubi babban cikin officer din yace,"ni zan fada musu result ko Kaine?" Officer yace, "no Kai keda Alhakin hakan muna jinka" sake gyara tsayuwar sa h.o.d yyi Yana bin duka Ahalin da kallo kafin ya dire shi Kan Sageer dayake ta girgiza kafa cikin gadara Dan sauke numfashi yyi kadan kafin ya dubi Alhaji Abdullahi cike da girmamawa yace, "Alhaji saidai kuyi hakuri" Alhji Abdullahi yace, "hakuri kamar Yaya?" H.o.d yace, "a bisa Wannan binciken Dana gano gsky kafin nace komai Ina me bawa dukkanin ku hakuri ciki harda Kai Omar" a rude Abba yace, "Kai Likita me kke nufi?" Alhji Abdullahi kuwa kasa motsi yyi, Mummy kuwa cewa take, "meyasa zakace shi? Me kke nufi?" Ta Fadi hakan itama bakinta na rawa, Omar da yaji zancen kuwa tuni yaji wata irin zufa ta ketso Masa ta goshi hakan yasa shi nufin ficewa a office din da sauri...shima h.o.d da sauri ya damko hannun sa, kafin yyi mgn Sageer ya fashe da wata irin dariyar keta Fadi yake haba, "waya Gaya maka barno gabas take? Ai Wlh duk makircinka Omar a bayana kke karyane da Raina kazo kace daddy ubanka ne hhhh....Amma dai anji kunya" ya Fadi hakan Yana Kara wayarsa a kunne bugu daya Faisal ya dauka Sageer yace, "ku futo daga inda kuka boye Dan yanzun Nan za'a fara show..." Gaba1 mutanen office din hankalin su a tashe yake hardai Abba daya kasa nutsuwa, a zuciye Sadeeq ya cakumo wuyan H.o.d cikin matukar bacin Rai yace, "kada ka rainawa mutane hankali ka sanar damu direct Abinda ake ciki bawai ka tsaya Mana indirectly ba," hannun h.o.d na bisa hannun Omar daya damke gefe guda na kokawa da rikon da Sadeeq ya Masa yace, "Dan Allah kuyi hakuri nifa har yanzu bakuji nace ga Abinda Yake a rubuce ba hakuri fa kawai nace kuyi" officer ne yazo ya janye Sadeeq din Yana duban h.o.d yace, "kasan Wannan case din babbane Amma kana ja musu Rai ka fada Mana me result ya nuna idan yaso daga baya ka bawa Wanda kaso hakuri..." Gyara kwalar labcoat dinsa h.o.d yyi kafin yace, "ku gafarceni" Nan ya dubi takardar hannun sa zai fara mgn kenan masu daukar rahoto na gidan radio da TV har sun hallara a wajen kowa da abun daukar sa sai fadowa office din ake, Sam hankalin su daddy bekai kansu ba shi kansa h.o.d be kula dasu ba Dan ya tsorata da reaction din Ahalin Dan Haka a gurguje ya fara fadin, "a bisa duba da kwayoyin halittar ku da mukayi a duka bangarori biyun cikin hukuncin Allah ya Tabbatar Mana da cewar Dr. Omar Wanda aka Fi sani da Dr. Omar salees shine Nan asalin jinin Alhaji Abdullahi Omar Mai fata, yyinda shi Kuma Sageer Wanda Ada ake ganin shine Sageer Abdullahi Omar mai fata asalin iyayensa sune Saratu 'yar aikin gidan Alhaji Abdullahi da mlm sale......" murnace ta karade mutanen office din, sai hamdala suke shi kansa Omar besan meyasa yaji zuciyar sa tayi Sanyi ba, oga Sageer fa? Tun daga ambaton Omar na farko ya Shiga shock, yyi suman zaune bakinsa a hangame gaba1 baya iya fahimtar Abinda ke faruwa Kuma, Faisal da yaji Abinda ya girgiza Masa tunani kokarin dakatar da 'yan jaridar da suke ta dauka suke Amma Ina sun samu new topic of discussion kowa Allah Allah yake ya zanta da daya daga cikin mutanen wajen, sai a lkcn hankalin daddy ya koma kansu da mmki yake tunanin waya turosu Kuma? Sadeeq kuwa rungume Omar yyi bakinsa yaki rufuwa sbd murna Fadi yake, "Alhamdulillah" Dan murmushi Omar yyi shima ya rungume shi ta baya, kowa fara'ace fal a fuskar sa duk 'yan jaridun sun cikasu da tmby Hajjaju da murna ta isheta tayi gaba tana Basu Amsa wani Dan jarida yace, "baaba koh Zaki iya fada Mana yadda abinnan ya faru?" Hajjaju bakinta a washe tana goge busassun hawayenta Tace, "kaidai Bari dannan Wlh duniya ta lalace kaga waccar munafukar matar?" Ta nuna Saratu da kanta ke kasa jikinta ya jike jalab da gumi, Nan kuwa aka hasko ta ita da Nas, Hajjaju taci gaba da fadin, "itace Nan 'yar aikin gidan Dana, munafukar mata muna tare da ita shekara fiye da talatin Ashe cin dunduniyar mu take tana Mana zagon kasa Allah ya Isa bamu yafe Mata ba" ta karasa mgnr tana matse kwallar takaici Tace, "yaron Nan umaru ta reneshi cikin azabar rayuwa da kunci har gaba da abadan abada bazamu taba yafe mata ba muguwa marar tausayi" Nan fa dayawan mutanen wajen suka cika da Alhini anaci gaba da daukar su, masu damarar wajen ne suka tiso keyar Saratu da Nas gaba, daidai lkcn Sageer yyi firgigit daga dogon suman zaunen da yyi dalilin girgizashi da Faisal yyi, a zabure ya Mike Sam be lura da 'yan jaridar ba ya nufi gaban h.o.d Bala zai cakumar Masa wuya officer ya riko shi, sai kwacewa yake Yana tirjewa Fadi yake, "kur'ani ban yadda ba, idan na yadda da Wannan batun shege nake, Kai karyane ma Wlh biyansa sukayi" officer daya rike shi yace, kana gani fa a gabanka aka Debi jini kowa Yana Nan har result ya fito Toh Kuma wanne irin shaida kkeso bayan Wannan?" Sageer yace, "dalla sakeni kaima biyanka akai" baki hangame officer yabi Sageer da kallo yace, "tsakanin Kai da Omar waye yaje har ma'aikatar mu ya kawo mu Nan?" Sageer da ya zama kamar zararre sbd dunbin takaici yace, "dama can Kun shirya hakan shiyasa ma kuka biyoni Dan Haka wallhi bazan lamunta ba saina hada musu jini da majina" ya Fadi hakan yanayin wajen h.o.d, da sauri officer yasa sauran mutanen nasa suka Kama Sageer take suka maka Masa ankwa shima suna turoshi waje, Abba dake can gefe ba Abinda fuskar sa take sai ambaliyar hawaye, idonsa na dama na kwararar da hawayen farincikin shahadar da yyi ya bayyanar da gsky, yyinda dayan idon nasa na hagu ke malalar zafafan hawayen bakincikin halin dayaga gudan jininsa ya Shiga a dalilin bakar ashana Saratu, dukansu tasa keyarsu akayi gaba har izuwa waje Nan suka tarad da mutane jingim gaba1 hospital din ya rude dajin Al'ajabi shiyasa Kota Ina bullowa ake Ana ganewa Ido hatta majinyatan da sukejin kwarin jikinsu ba'a barsu a baya ba Nan aka fara cincirindon ganewa ido, har daga waje ma shigowa ake lbri harya fara bazawa ko'ina especially gidan TV da suke watsa abin a daidai lkcin, Kan Saratu na kasa Amma sbd zungurinta da ake Saida yasa ta dago kowa Nan ya shaida fuskar Azzalumar matar datayi Wannan danyen aikin da ita kanta nurse, Sageer kuwa Banda harbe2 ba Abinda yake sai dura ashar yake Yana surfa zagi hatta daddy ma cewa yyi biyansa akai lol# Abu dai ya baci yyinda a bangaren su Omar ya kasance duhu ya yaye haske ya bayyana, camera kuwa tayi aiki domin duk Inda ka juya flash kke gani hatta masu manyan wayoyi ba'a barsu a baya ba take wasu suka fara uploading Ana dorawa a kafafen sada zumunta labari da dumi-duminsa. Acan bangaren Meera kuwa tun bayan da suka Gama mgn d dad ta lumshe Ido take bcci yyi awon gaba da ita abinka da dama tun Daren jiya batayi bcci ba, Koda suka Isa Adamawa lkcn la'asar tayi suna sauka dad ya hango Ahmad wato jikan inna fure kanwar kakar Meera kenan ta wajen ummah, da fara'ar sa dad yayi nuni da Ahmad din da ko kadan be hango su ba yace, "Yauwa Ameera Kinga Ahmad can ya Zo daukar mu" kallon inda dad yake nuna mata tayi daidai lkcn kuwa Ahmad ya dago kansa, Yana ganin dad ya taho da sauri da murnar sa shima, musabaha sukayi da dad cikin fara'a Ahmad ya kalli Meera yace, "sister barka da zuwa Adamawa" Dan murmushi Meera tayi kafin Tace, "Ina wuni" "lpy Alhamdulillah" Ahmad ya furta hakan Yana karbar trolley din wajenta, sun Fara tafiya kenan Ahmad yaci gaba da fadin, "Amma dai dad Bata taba zuwa Adamawa ba Koh?" Dad Yana Dan murmushi yace, "tazo Mana Amma lkcn tana Karama" Ahmad yace, "yauwa Koda