Sashe 106
Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inna fure tayi tana duban dad daya Shiga damuwa tace, "da alama sakin wulakanci ya mata shiyasa ta kasa furta komai" cikin sanyin jiki dad yace, "Nima Abinda nake tunani kenan tun jiya naso Jin ta bakinta dake a firgice tazo min saima kin ganta duk ta lalace Wlh" wani kululun takaicin ne ya sake Kama Inna fure Tace, "ina number marar mutuncin Nan yake na Kira yanzun Nan na Tabbatar Masa da cewa Meera da gatan ta?" Girgiza Kai dad yyi yace, "Banda ita" kwafa Inna fure Tayi ba Haka taso ba Amma a fili tace, "matukar Bata da hakki a kansa sai Allah ya saka mata" dad yace, "gskyne." Tashi yyi yabar gidan ita Kuma Inna fure ta nufi wajen Meera. Tun da asubar fari Dr. Omar ya jawo jakarsa zuwa parlo, abin har yaso bawa Sadeeq dariya Amma ganin yadda ya hade girar sama data kasa yasan yyi hakan ne Dan kada ya sake tsokanar shi, shigewa daki kawai yyi abinsa ya koma gado ya kwanta, Dr. Omar kuwa na Gama fito da jakar sa ya koma dakin ya dauko wayarsa da agogon sa Yana jawo kofar ya fito parlo, kokarin sa agogon sa yake Yana ganin lkci 5:40am a kalla su tafi da wuri yadda zai samu yyi tozali da sanyin idaniyar sa sai yanzu ya fahimci yyi sabo da Ameera Wanda Ada besan da hakan ba, ya Saba kullum dai a kallah zai hadu da ita Koda kuwa mgn me Dadi Bata hadasu ba, sai yanzu ya fahimci kallon kallo da suke Yana Kara Masa kwarin ido sabanin yanzu da yakejin Kamar idon ba a jikinsa yake ba burinsa kawai ya samu tozali Amma tozalin idon Meera, bayan ya Gama Shirin sa ne yadan kishingida Dan a tunanin sa Sadeeq shiryawa yake Yana Wanka, Dan kuwa shi tun kafin yaje masallaci yyi wankan sa especially Daren jiya daya Dade Yana tunanin Meera sai bcci barawo ya sace shi hakan ya jawo yyi mafarkinta, a cikin dream din nasa yyi feshin Madara shiyasa Yana tashi ya hade wankan sa, lumshe Ido yyi dake ba ishashen bcci ya samu jiyan ba sai kuwa ya sake yin awon gaba dashi Wai a hakan jira yake. Dakyar dai Inna fure ta samu ta shawo Kan Meera ta daina kuka har bcci ne ma ya dauketa tanata Jan zuciya tamkar karamar yarinya, wajajen karfe goma kuwa saiga Ahmad yyi sallama a gidan, Inna fure ce kadai a parlo tana tunanin Meera duk tasauyin yarinyar take a gidan ubanta Bata samu hutu ba gashi a gidan mijin ma Babu sauki Oh Allah dai ya sayaya Mata...., Sallamar Ahmad dince ta katse mata tunani, da fara'a ta Amsa sallamar tasa karasowa yyi ya zauna Yana diban gaisuwa, amsawa tayi tana tmbyr mutanen gida yace, "ai tun jiya suke tmbyr 'yarsu Ameera nace kece Nan Kika Hana da tuni tare mukaje" Dan murmushi Inna tayi Tace, "ai yau Insha Allahu zata Zo yanzu ma so nake Ana azahar mu fara zaga dangi na kusa kasan mahaifinta ma Yanason kaita can Gombe wajen 'yan uwansa" Ahmad ne yace, "dama ba Dan kano bane?" Inna fure Tace, "Toh kusan dai Dan kanon za'ace tunda acan aka haife shi saidai iyayen sa shi kadai suka Haifa su Kuma usulun su 'yan Gombe ne kasuwanci ya maidasu kano, Toh kasan zumunci idan ba anyi dgske ba da zarar ance ba ran Wanda ake ganin girmansa sai kaga Abu Yaja baya" Ahmad yace, "hakane Allah dai ya rufa Mana Asiri" "Ameen Amadu" Dan Bata Rai yyi yace, "meye Kuma Amadu Inna?" Inna Tace, "Kai kajimin yaro Toh ba sunan ka bane?" kawar dakai yyi cikin kawar da mgnr yace, "Wai Bata tashi bane?" Inna fure Tace, "anzo gurin.." Juyowa yyi Yana kallon ta yace, "gurin me?" Dariya take Masa Tace, "haba Amadu ni nasan zaryar Nan akan Ameera kke shiyasa nace anzo gurin tunda na ganka da wuri Haka nasan zancen gizo baya wuce na koki" cikin borin kunya ahmda yace, "yanzun Nan fa Kika Gama mgnr zancen zumunci idan taga duk bama kulata ai bazata sake marmarin dawowa ba Koh?" Gyada Kai Inna tayi Tace, "kanada gsky" Dan sauke ajiyar zuciya yyi yace, "Toh yanzu Bata tashin bane?" Girgiza Kai Inna tayi tace, "harta karya ma tadai koma bcci ne" cikin damuwa yace, "Wai har yanzu bataji saukin Kan nata bane?" Inna tayi murmushi Tace, "a'a gajiyar ce Bata Gama sakinta ba Kuma kaga Anjima zamu fita banaso ta takura dayawa" gyada Kai Ahmad yyi yace, "hakan yyi Nima zan koma Anjima zan dawo sai muje" "Toh madallah" Inna fure ta furta hakan shi Kuma ya fice. Dariyace sosai ta Kama Sadeeq daya fito cikin Shirin sa yaga Omar kishingide Kan kujera yanata bcci takalmi a kafarsa, dariyar tasa ce ta farkar da Omar a firgice ya tashi zumbur Yana kallon Sadeeq da yake cikin Shirin sa yace, "Yauwa ka fito Toh muje banaso ko takwas tayi Mana anan" wata dariyar Sadeeq ya sake Yi hakan yasa Omar Jan tsaki Yaja jakarsa yyi gaba, dake parlon duk an saki labulai shiyasa Sam bazakace lkci ya kure ba Dan akwai sauran duhu, Omar na bude parlon yaga Rana ta haske shi da sauri yayo baya Yana Kare fuskar sa, Juyowa yyi yaga Sadeeq ya rufe bakinsa da hannu Yana dariya, cikin takaici yace, "Wai Kai Abin dariya na koma maka ne da kke tamin dariya tunda na tashi?" Dage kafadun sa Sadeeq yyi yanzu Kam murmushi yake yace, "mutumin da yake sauri tun farkon Asuba shine na tarar a parlo Yana bcci" kallon agogon sa Omar yyi kusan 10:50am wani takaicin ne ya sake Kama shi yyi waje Sadeeq na Binshi a baya, Suna hanya sukaci Karo da Safna, tana isowa gabansu Tace, "yauwa ya Ameer Wlh Karo na uku kenan Ina zuwa tun 9am akace na Kira ku ni Kuma Naga Kuna bcci shiyasa ban tadaku ba" dafe goshinsa yyi Yana riko hannun ta yace, "why Safna? Meyasa baki tadani ba?" Yyi mgnr ransa a dagule, farfari tayi da Ido Dan Bata Saba yayanta ya mata hakan ba Tace, "Toh ai ba kowa keson a tada shi Yana bcci ba" "darn it.." Omar ya furta hakan Kamar yyi ihu Dan haushi, wuceta yyi kawai ya nufi part din Mummy, bin bayasan tayi da kallo taji ance, "Safna.." Juyowa tayi Sadeeq ne a tsaye bayanta, murmushi ya sakar mata hakan yasa itama ta saki murmushin da Bata shirya ba, matsowa yyi kusa da ita yace, "Saifa kinyi hakuri da sabon Yayan naki" Tana murmushi tace, ,"No ba wani Abu hakan yasa naji inada kwarin gwiwar shiga Ko Ina tunda inada jarumin Yaya" dage gira yyi Yana murmushi shima yace, "oh! Really?" "Yes" Safna ta Furta hakan, Fara tafiya sukayi kafin yace, "Ashe naki saurayin jarumi ne" yyi mgnr kirjinsa na bugawa Dan besan amsar da zata bayar ba, shiru Safna tayi Kamar bazatayi mgn ba can Kuma Tace, "wa? Ni?" Sadeeq yace, "ehmana" Dan murmushin gefen baki tayi kafin Tace, "upto now ban hadu da wani jarumi ba" wata boyayyar ajiyar zuciya Sadeeq ya saki kafin yace, "but why?" Kallon sa tayi Tace, meyasa kke tmby? Shima Yana kallon nata yace, "nutsatsiyar budurwa irinki me cike da Kamala da kwarjini hankali da hangen nesa ace ta Rasa jarumin da take so ba" zuba Masa ido tayi sosai karon farko kenan da taji wani Namiji ya mata mgn ta hankali sabanin Wanda zasu fara furta yanayin kyanta da Kuma dukiyar mahaifin ta, waving hand dinsa yyi a face dinta hakan yasa ta Danyi firgigit a kunyace ta kawar da kanta batace komai ba tayi gaba da sauri, lumshe ido Sadeeq yyi yace, "my dream girl welcome to my heart." A gurguje Omar keta cusa breakfast din da aka jere musu da Sadeeq, Mummy data dawo wajensa yanzu tace, "ga ticket dinku Nan jirgin 12pm zaku bi" tea din da Omar ya kurba ne ya furzar da sauri hakan ya sashi Fara tari, ruwa Mummy ta Mika Masa yasha kadan kafin yace, "Mummy har Nan da 12pm?" Kallon mmki ta Masa Tace, "Abinda ya jawo Tarin kenan?" Dukar da kansa yyi a kunyace, Dan murmushi tayi Tace, "duka saura mintuna nawa Sha biyun tayi? Yanzu fa har 11:15 tayi kafin ku Gama ma lkci Yaja kaga saiku wuce" Sadeeq ne yace, "hakan ma Yyi Mummy ai saukin mu kenan" hararar sa Omar yyi a kaikaice Sadeeq ya Masa gwalo, Mummy kuwa Tace, "Abinda nakeso ya fahimta kenan idan kun Gama Hajjaju na part dinta sai ku gaisa Abba ma yana inda yake duk saiku gaisa kafin daddy ya fito Dan tare zaku tafi" zaro Ido Omar yyi yace, "Adamawan?" Mummy ta kada Kai Tace, "haba akwai babban case a gaban mu ai, tun safe aketa doka Masa waya game da case din matar Nan Saratu Haka zalika Sageer daya zama kamar zararre Yana kaiku airport zai wuce can" Shiru Omar yyi da ace Babu case din Meera a kansa tabbas da tare zasu je Dan bayajin zai iya yafewa Saratu bisa rabashi da iyayen sa da tayi idan ya tuna Wannan Abu yanajin takaici matuka, juyawa Mummy tayi tabar masu wajen, bayan sun Gama kuwa suka Mike Dan zuwa wajen Hajjaju, tana parlon ta Ana mata tausa ganin su yasa meyi mata tausar ta fice tana Dan waiwayen Dr. Omar, Dan duk ma'aikatan gidan sai kishin2 sukeji daga wajen securities da abun ya faru gabansu Amma basuji mgnr daga tushe ba Dan su daddy Basu fada musu komai game da Omar ba Amma sunada niyyar su Tara duka ma'aikatan su sanar dasu Abinda ke faruwa, securities din da suka yiwa Omar wulakanci kuwa cikinsu ne ya duri ruwa sun Shiga fargaba da tashin hankali. Zama sukayi da fara'ar su suka fara gaishe ta, Hajjaju ma da fara'ar ta take Amsa musu Tace, "duk Wannan Shirin na zuwa wajen kishiyar tawa ne?" Dan murmushi Omar yyi yace, "Hajjaju ai kece ta gaban goshi" Hajjaju Tace, "a'a ban yarda da dadin bakin maza ba Abinda tun jiya kkeso ka gudu?" Dariya Sadeeq ya saka yace, "ai Hajjaju tun duhun Asuba yaso gudu Allah ya Kama shi bcci ya sace shi" Hajjaju na Kama haba Tace, "ai kaji Koh? Lalle wannan Ameera da