← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 128

Sashe 57

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fara tare Mata fada ne tun kafin ayi nisa? Toh Bari kaji ka daina wani rawar Kai kana kwala Kai a faranti Dan Babu mmki kaje ka sameta fanko wani ya Gama da ita sai saura" cikin bacin Rai sosai Dr. Omar ya bude baki zaiyi mgn yaji an jawo shi, Abba ne yyi Masa Alama da yyi shiru, cije lips dinsa yyi cikin takaici ya juya Da niyyar tafiya, sai tausar zuciyar sa yake sbd yadda yake tunawa duk fa Abinda zaiyi mahaifiyar sa ce Babu yadda ya iya da ita be kamata Yana barin zuciya nafin karfin sa ba Dole ya lallaba da kalar uwar daya samu a rabu lfy, daidai zasu fita sukaji Saratu tace, "aikin kenan Kaima Haka zaka Kare da gulmar ka dadinta ma dai Babu bakin mgn bare ayi gulmata" Saratu ta furtawa Abba hakan, Ko kallon ta Abba beyi ba Dan bayason Dr. Omar din yace komai akai, Haka ya rakashi har bakin mota Saida yaga tashin sa kafin ya juyo zuwa gidan, Ashe suna fita kuwa Saratu ta jawo Sahabatu cikin masifa tana surfa Mata bala'i dama duk so take Omar yabar gidan Dan ta samu damar tmbyr ta, Sahabatu da aka jawo ta fisge jikinta cikin Rashin kunya tace, "Wai meye hakan ne ummah? Haba duk kinbi kin takura min tun jiya" "Kinci malafar ubanki kinji Koh?" Saratu ta fada ranta a bace, Zumburo baki Sahabatu tayi tana juya Mata keya, a zuciye Saratu tace, "bazaki gayamin Dan iskan daya Miki ciki ba ko saina zubar Miki da hakora?" Sahabatu tace, "Toh ni nasan Wanda yyi min?" zaro Ido sosai Saratu tayi tana Kara juyo d fuskar Sahabatu tace, "Dan ubanki me kike nufi?" Sahabatu ta sake fisgewa daga rikon da Saratu tayi Mata tace, "gsky fa na fada Miki bazan tantance waye uban cikin Nan ba" wani irin wawan Mari Saratu ta dauke Sahabatu dashi murya na rawa cikin tsantsar tashin hankali tace, "talle na tura ki kiyi Koh yawon akuyanci?" Share hawayenta Sahabatu tayi tace, "sai yanzu zaki tmbyi talle nake ko yawon akuyanci? Lkcin da nake kawo Miki kudi dayawa kin taba tsayawa ne ki duba yanayin yawansu da jarin Abinda na siyar? Na tabbata duk kudin da nake kawowa sun ninka jarinmu sau goma" tafa hannu Saratu tayi tace, "Shikenan kun cuceni yaran Nan, kun Gama Dani, duk kun watse" ta karasa mgnr tana Dora hannu akai, hararar ta Sahabatu tayi tace, "duk lefinki ne Kuma meyasa kike hadawa da jam'i? Nasan dai ya Maru yanada nutsuwa" a firgice Saratu ta kalleta Ashe taso tayi subutar baki Dan ita yanzu Sageer take tunowa lkcn dayace taja kofa Yana Shirin lalata 'yar mutane, cikin kawar da zancen tace, "ke tashi bamuga ta zama ba dama a unguwar Nan an sa Mana Ido sosai Dan Haka dole musan abinyi, dole yanzun Nan muje a zubar da cikin Nan Dan bazan rike Dan Kato ba Wlh" tayi mgnr Yana jawo hannun Sahabatu, Fisge hannunta Sahabatu tayi tace, "Wlh bazanje ba" Saratu tace, "ashe bakida wayo ban sani ba?" Sahabatu tace, "nifa nace bazanje ba* cikin takaici tace, "ke wacce irin mahaukaciyar yarinya ce Kam? Kinsan Abinda nake hango Mana kuwa? Toh Wlh bazaki sani Jin kunyar mutane ba Dole muje a zubar da Dan iskan cikin Nan tun kafin yyi kwari" Sahabatu tace, "Ashe kuwa matukar Kika matsa sai an zubar Toh kuwa Zaki iya rasani Dan kafin kiyi tunanin a zubar na rigaki yin Wannan tunanin Dan Wannan ba shine farau ba" a gigice Saratu tace, "me kike nufi?" Sahabatu tace, "na zubar da ciki kusan sau biyar Wannan shine na shida matukar na matsa saidai na Rasa rayuwa ta" zubewa Saratu tayi a wajen cikin mugun tashin hankali tace, "shikenan Sahabatu kin kashe mu" ta Furta hakan tana Dora hannu akai, mlm sale dake jinsu kuwa goge hawayen bakin ciki yyi a ransa Fadi yake Allah ya Isa tsakina dake Saratu kin cuceni, kin tarwatsa min farinciki na, Ban yafe Miki ba, da Wannan tunanin nasa shima ya shige daki. Acan bangaren Ameera kuwa zaune tayi gaban gas tana juya miyar da take Shirin gamuwa, sai sauri take tana duba agogo Dan bataso ta haura time din da yace, dake duk wani Abinda ya shafi kitchen gwanace hakan yasa duk Abubuwan da tayi be Bata wahala ba sbd dama can ta Saba domin ita keyin girkin gidansu, a gurguje taje jikin dining table ta jera Masa kulolin Abincin nasa, Saida ta Gama tsaf ta dawo kitchen ta gyara shima, Kai kace ba'ayi amfani da wajen ba dake ma lkcn da take aikin tanayi tana sawa a Dan karamin kwandon shara ne shiyasa kitchen din be wani harsgitse ba, lkcn da take shafa Addu'ar ta na sallar Isha ne taji Alamar shigowar sa Dan dazu ma saijin karar motar sa tayi lkcn dazai fita, sanin zai iya bukatar abincin sa yasa ta fada toilet a gurguje dan zafi takeji musamman data Gama girki yanzu, kafin wani lkci harta gama wankan ta Sharp kafin ta samo riga da skirt ta saka, Bayan ta tufke gashinta ne ta dauko hijab dinta shima ta saka Dan bazata iya zuwa gabansa a Haka ba sbd kunyar sa da takeji musamman idan ta tuna lkcn daya taimaka Mata da rigar sa sai taji kamar ta nutse a kasa Dan kunya, Tana fitowa kuwa taga Yana sakkowa daga sama harya Kai kayansa ya aje, Da Dan hanzarin ta ta Isa gareshi murya na rawa Tace, "am,..Ya Omar" Dan tsayawa yyi Jim Yana tuno inda aka fara kiransa da hakan, a ransa yace kaji wani sabon sanabe, a fili kuwa tabe baki yyi ya juyo ya kalleta ya watsar beyi mgn ba yaci gaba da tafiya har izuwa Kan kujera ya zauna, Dan binsa tayi a darare daga Dan nesa ta tsaya tana Wasa da hannunta takasa mgn sbd yadda taga Yasha kunu, kamar daga sama taji yace, "kin hadiyi sanda ne kika tsaye min akai?" Yyi mgnr Yana juyowa gefen ta hade da wurga Mata Harara, durkusawa tayi cikin rawar murya tace, "kayi hakuri dama zance ne ga abincin can na aje Kan dining table ko Kuma a kawo maka Nan ne?" Kawar da kansa yyi be Mata mgn ba Yana kokarin canja channel Saida Yaja wasu seconds Dan har ta debe tsammanin bazaiyi mgn ba taji yace, "kawo Nan na gani" tashi Meera tayi da saurinta da nufin dauko Masa kular, hakan yasa ya bita da kallo kasa2 Yana Jan tsaki a hankali a fili kuwa Fadi yake, "village girl ji yadda take tafiya kamar zata kifa Wai a hakan mace?" Mtwss ya sake Jan tsaki, acan gun Ameera kuwa batasan kushen da ake Mata ba duk tanayin komai da hanzari ne Dan kartayi lefi Dan Haka ma duka ta debo kular wata ta rungume, wata ta rike a hannu, yanzun ma cikin sauri ta iso wajensa, Omar sai ganin ta yyi ta aje Masa a gabansa saura kiris ma kular ta bude tayi saurin tarota tana rufeta da hannu, tsaki Omar Yaja da karfi hakan yasa Meera ta aje kulolin da sauri tana matsawa gefe, Kamar bazaiyi mgn ba can Kuma yace, "bude mu gani" budewa Meera tayi gashi Nan dai an mulmula sakwara ga miyar egusi Nan kamshi sai tashi yake, Amma a gurin Omar Kam tabe baki yyi yace, "waye zaici Wannan kwamacalar Taki?" Zaro balabalan idanunta tayi tana kallon sa da mmki, Tsare gira yyi sosai cikin dan daga murya yace, "bance banason yawan kallo ba?" Kawar da idon nata tayi da sauri bakinta na rawa Tace, "kayi hakuri" tsaki Yaja me sauti yace, "kwashe Wannan kwamacalar Taki daga gabana kije can ki cinye Dan zuciyata dab take da tashi sbd yanayin kamshin girkin ma ba Dadi saima kauri dake tashi" Yyi mgnr Yana maida bayansa jikin kujera, kallon sa tayi a sace ta dawo da kallon nata Kan abincin data bude mmki ne sosai ya kamata da yace Wai kauri suke, Toh kauri ta Ina? Tasan ko a gidansu dad dinta na son sakwara da miyar egusi Kuma ita takeyi Toh kodan tayi girkin ne da gaggawa? "Zaman me kike har yanzu?" Dr. Omar ya katse Mata tunanin da take, be karasa rufe bakinsa bama ta debe kulolin da hanzari tana bar masa gurin da sauri Tsaki ya sake ja ya maida hankalin sa Kan labaran da ake, Saida ya Gama Jin lbrn ya kashe kayan kallon ya nufi sama, Koda yaje dakima takeaway dinsa ya bude daya shigo dashi dama can bawai yanada niyyar cin abincin nata bane Dan gani yake jagwalgwalo ne bazai iya cin kazanta ba, Saida ya Gama yin da'amin kafin ya shige toilet ya sakar ma kansa ruwa Bayan ya Gama ne ya dawo daki ya shirya zuwa kayan bcci, kashe wutar dakinsa yyi lkcn 10pm ta kusa yyi mmkin saurin lkci Saiya tuna Ashe ya Dade da Abba dazu Bayan sunyi sallar Isha, Dauko wayarsa yyi ya kunna, hoton tane ya bayyana, kafe ta yyi da Ido Yana Ji a ransa kamar ya Santa ba kowa bace face hoton Mummy, tun lkcn daya gani a wayar Safna ya samu kansa da turawa da sauri batare da tasan yyi hakan ba, tun Yana gun aiki time to time yake yawan duban hoton brain dinsa na fadawa tunani kamar wacce ya santa, rufe wayar yyi Yana me lumshe idonsa, haduwarsu ta dazu yake tunawa sai yake jinsa kamar shima Dan cikinsu ne wato lkcn da Safna tazo, ga daddy a wajen, sai Kuma shi sai yake ganin kamar wani Ahali guda sun hadu, dafe goshin sa yyi a fili Yana Furta, "What's wrong with me?" Dan tsaki Yaja kadan kafin ya fara Addu'ar bcci ya shafa sannan ya lumshe idonsa gaba1. Acan bangaren Ameera kuwa Koda tabar wajen Bata tsaya ko'ina ba sai kitchen, aje kular tayi tana sake duba miyar Dan karawa tayi a hanci tanason Jin kaurin da yace yanayi Amma bataji komai ba, shima sakwarar Saida ta Kara a hanci Nan ma shiru, duk ta Shiga damuwa sbd batasan mezai biyo baya ba, Amma da cikinta ya murda Saida ta Kama saitin wajen tana tunanin tun guntun kazar dataci da safe Bata Kara cin komai ba gashi har Bayan Isha yyi, Haka
Chapter 57 · 0% Book details