Sashe 69
Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fuska ya hade sosai yace, "ke a gidanku ba'a koya Miki sallama bane?" A firgice Meera Tace, "Yi hakuri" ta furta hakan bakinta na rawa tayi kokarin juyawa da sauri, Tsaki Dr. Omar yyi kawai shima ya shige toilet. Kallon kansa Sageer yyi a madubi wayewar yau yaga duk ta kumbura ransa ne ya baci sosai gashi Ayau dinnan za'a fara duk wani event da za'ayi na bikinsa, Yana tsayen ne yaji an fara Masa knocking ta waje kin mgn yyi Dan tun jiya daya fice sassafe be Kara waiwayar gidan ba sbd kamasa da Dr. Omar yyi, Koda yake har lkcn ma basu fahimci Dr. Omar dinne yyi musu hakan ba, ci gaba da buga Masa kofar akai a tunzure yaje ya bude Yana fadin, "Wai uban waye me nacin bugun Nan?" Ya karasa mgnr Yana bude kofar tasa, wani irin mugun tsaki Yaja ya harari na bakin kofar kafin ya juya, Saratu da tun jiya ta lura da Rashin shigowar sa gida shiyasa Sam ta kasa nutsuwa sai dubansa take tanaso tazo ta dubashi sbd a jiyan taji alamun shigowar sa gidan Babu damar hakan sai yanzu da Hajia Aisha ta nemi a tura wata ta Kira mata shi tace zataje da kanta, ganin yadda idonsa da bakinsa suka kumbura ne yasa hankalin ta ya tashi da sauri ta fada dakin bakinta na rawa tace, "sageeru waye ya maka Wannan mugun abin?" Ta Fadi hakan tana nuna fuskar sa da yatsa, ji tayi an buge yatsan nata Kamar zai lankwashe da sauri taja hannun nata Dan azaba, cikin Jin haushi yace, "ke wacece da Zaki dinga nuna ni da hannu? Bayan Haka ma wanne iya shege ne ya kawo ki dakina Banda bakar jaraba da Wannan safiyar ki isheni?" A rude Saratu Tace, "kayi hakuri dama Hajia ce Tace nazo na kiraka" tsaki me sauti Sageer yyi yace, "Dallah ni ficemin daga waje" a hanzarce kuwa Saratu ta juya da sauri tana waiwayen fuskar sa data kumbura sosai, kayansa daya dauko ya saka kafin ya wuce part din Mummy, suna zaune da Daddy yyi sallama ya shiga, Zama yyi kasa Yana dukar da kanshi Dukansu biyun kallon sa suke da mmki, Hajia Aisha ce Tace, "Sageer Wannan kumburin fuskar taka a Ina ka samo shi?" Sake dukar da kansa yyi kafin yace, "bugewa nayi" daddy yace, "bugewa kuma? Dame ka buge?" Sageer ya Rasa amsar dazai Basu kawai yyi shiru, ganin Haka yasa daddy yaci gaba da mgn Yana fadin, "Sageer tunda har auren ka ya matso a kalla befi saura kwana uku ba inason kafin lkcn ace ka tattaro min duk wani results dinka nacan school" a firgice Sageer ya dago Yana duban daddy kirjinsa na bugawa da karfi, daddy ya girgiza Kai yace, "inason na baka wani company din da zaka juyashi Dan kaima ka rike kanka but saina ga takardun ka" wata irin zufa ce ta fara karyo wa Sageer take ya fara zundumawa prof Aliyu zagi har cikin ransa yake Jin takaicin canjin department din da akai Masa yanzu ta Ina zai samarwa daddy Wannan takardu? Daddy ne ya katse Masa tunanin da fadin, "nasan irin karatun ka Sageer inaso Naga irin point din da kke ja a school anan ne zan San Matsayin dazan Dora ka" Dagowa Sageer yyi Yana Dan Bata Rai yace, "haba daddy wasu ma can daban ka Basu Matsayin me girma a manyan company dinka bare ni da nake jinin ka? Ai kamata yyi kawai kace nabar B.U.K dinnan nazo ka damka min Wannan katon company din naka na Nan" kallon sa sosai daddy yyi a takaice yace, "sai yanzu ka Kara Tabbatar min da ba karatun kke a school ba shiyasa Sam you don't know the meaning of company bare Abubuwan dake cikin at all" kawar da Kai gefe Sageer yyi Yana muzurai, daddy yaci gaba da fadin, "idan har kanason kaci gaba da rike matarka da mutunci da Kuma daraja tabbas saika kawo min takardun school dinka Naga a wanne matsayi kke ciki idan ba Haka ba..." Sai Kuma daddy yyi shiru, Dagowa Sageer yyi Yana kallon daddy Yana jiran yaji me zaice, daddy yace, "Abinda yafi maka sauki shine Naga Abinda kke a school" tashi Sageer yyi ko sallama be musu ba ya fice a tunzure gaba1 hankalin sa a tashe yake yanzu ta wacce hanyar zai bullowa lamarin Nan? Saratu dake labe daga can kofar kitchen taji nata hankalin itama ya tashi Ada tana burin Sageer din yyi aure ko za'a damka Masa wata dukiyar dazai juya sai Kuma taji wani sabon salo Wai takardu? Ashe dai su daddy da take kallo Haka da wayon su, Nan ta fara tunanin ya za'ai Wannan takardu su samu take a karon farko taji haushin Sageer din matuka da Rashin Kwakwalwar sa Dan tanaji dazu suna mgnr shekara biyu data wuce ya kamata ace ya Gama karatu Amma har yanzu jiya iyau ba lbri. Meera na Gama rufe jarkar ruwan data Gama yiwa Abba Addu'o'i ta dauka a hannu bayan ta gyara hijab dinta ta fito, yau kusan kwana biyar kenan Ana bashi mgnin Yana Amfani dashi, tun kafin Tasha kwana take jiyo kakarin Aman mlm sale da sauri ta kara saurin tafiyar ta tana daga nesa dashi ta hango ashe amai yake, da sauri ta Isa gareshi taga Yana wani irin amai na bakin Abu kamar ruwa Yana fita a bakinsa da sauri Meera ta juya wajen mlm habu me gadi da nufin sanar Masa sukaci Karo da Dr. Omar daya dawo gidan, binta da kallon mmki yyi d sauri Tace, "yauwa Dan Allah ya Omar taho muje Abba ba lpy" ta Fadi hakan a rikice, a rude dukansu suka Isa gaban Abba daya rike makogwaron sa dake Masa zafi sosai, riko shi Dr. Omar yyi Yana fadin, "sannu Abba Bari muje hospital" rike hannun sa Abba yyi ya girgiza Masa Kai Yana Nishi a hankali, daidai lkcin Meera ta Mika Masa ruwan data Debo danya wanke bakinsa, Wankewa Abba yyi kafin suka matsa a wajen, kallon shi Dr. Omar yyi yace, "Amma meyasa baza muje hospital ba?" Abba ya girgiza Masa Kai Yana bude baki domin jinsa yake Kamar zaiyi mgn sai yaji wani Abu ya tokare shi, shiyasa yake ta Wannan kakalen Aman sbd yanajin kamar abin zai fita, Miko Masa jarkar Meera tayi Tace, "Abba ga sauran mgnin sai kaci gaba da Amfani dashi" karba yyi da murna domin tabbas yanajin dadin mgnin, Meera Tace, "Da fatan kanajin dadin shi?" Girgiza Kai Abba yyi da fara'a sosai Yana washe baki, Dr. Omar ya taimaka Masa ya koma cikin daki Saida ya kwanta sbd makogwaron nasa dake zafi kafin suka futo, a tare suka Shiga parlon su Dr. Omar ya zaro wayarsa dake ringing tun dazu, dauka yyi sbd ya gane me Kiran zama yyi Kan kujera ya fara Amsa wayar Salma, Salma dake dayan barin Tace, "Dr. Omar kwana biyu na jika shiru Kuma idan nazo office PA dinka baya Bari na Shiga Wai hakan meke faruwa ne?" Dan kallon Meera da take Shirin tafiya dakinta yyi kafin ya maida hankalin sa Kan Salma Yana Dan daga murya yadda Meera zata ji yyi Dan guntun murmushi yace, "karki damu tomorrow zanyi Masa mgn yadda zai fahimci su waye ya dace su Shiga office dina" ya karasa mgnr Yana satar kallon Meera data kasa tafiya saima Juyowa da tayi a tunzure ta rike qugunta duka biyun tanajin wani irin kishi na taso mata hakan yasa ya maida hankalin sa Kan wayar Yana sauraron Salma, da murna Salma Tace, "shikenan zanzo goben" Nan suka ci gaba da wayar Yana biye Maya badan komai ba sai domin Meera taji haushi, Saida ya gaji da Jin shirmen ta kafin ya kashe, Meera da tun dazu ta daskare a tsaye tana sauraron sa ta matso inda take ranta a bace tace, "Ya Omar" kallon ta yyi up and down yace, "Ya akai?" Dan kawar da kanta Meera tayi tana kokarin zama nesa dashi tace, "inason muyi mgn ne" aje wayar hannun sa yyi Yana me Bata attention dinsa yace, "meya matsalar?" Meera tadan ja Numfashi sosai tace, "kusan watanni kenan da auren mu Amma haryau bansan meye asalin matsayina a gidan Nan ba, auren da Kai da kanka ka nemi ayi shi, ko badan NI da nake mace yarinya ba ya kamata ace ka dubi girma da Matsayin aure ka saurareni ta wani Bangaren" Hade fuska Dr. Omar yyi yace, "yaushe Kika fara zama me saurin mantuwa ne?" Meera Tace, "Kamar ya?" Dr. Omar yace, "Kin manta tun lkcn da Kika shigo gidan Nan nace kada ki kuskura ki dauki kanki a Matsayin mata domin kedin baki da banbanci da wacce tazo Aikatau?" Meera na share hawayen da suke gangaro mata tace, "yanzu tsawon lkcn Nan ban cancanci ace ka manta da Abinda ya faru a baya ka rungumi auren ka ba?" 'yar dariyar takaici Omar yyi yace, "Na manta?" Sai Kuma yyi shiru Yana Kare mata kallo yace, "a jaririya na dauke ki wacce batasan me ake Kira da aure ba but Naga kamar kedin kin zaqe da yawa alamu ya nuna kinsan meye aure wato kina bukatar Namijin dazai debe Miki kewa" cikin mugun tashin hankali Meera Tace, "Ya Omar?" Dr. Omar cikin tsare gira yace, "ba hakan bane? A zaton ki nidin kowacce kucakar ce zata birgeni har naji Ina sha'awar daukar ta a Matsayin Mata? Look Meera idan ma ni kike tunanin zai zame Miki wani bangare na Rayuwar ki kinyiwa kanki gurguwar fahimta, domin kedin bakya cikin tsarin irin matar da nakeso, bakida class din daya dace na jera hanya dake a Matsayin Mata, bakida Kirar jikin da zan kalla ki birgeni a Matsayin Mata, Ban taba Jin Inajin sha'awar kasancewa dake ba Meera, Da zarar Abba ya koma gida zanyi kokari naga na baki sallama kin tafi gidanku domin amfanin ki ma ya kusa karewa a gidan Nan" a razane Meera Tace, "bayan cin mutunci da wa'annan mugayen kalaman daka furta a Kaina zaka tozartani da saki?" Kawar da kansa yyi yanajin wani irin Abu na tokare Masa kirji yace, "hakan dai nake tunani Kuma idan hakan zaisa Kiji Kamar na tozarta ki to kuwa ba shakka daukar fansar da nayi yazo akan