Sashe 70
Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gaba kenan, matukar Abba ya koma gida Toh a satin Zaki bar gidan Nan domin ci gaba da zama dake baida amfani" yyi mgnr Yana zube mata idonsa a nata, rintse ido Meera tayi jikinta sai rawa yake sbd tashin hankali tace, "akan lefin da ba nawa ba kke fatan kaga tozarci na Ya Omar?" Ta karasa mgnr tana bude idonta a kansa, taci gaba da fadin, "Ko halin da Abba yake ciki baka gani kaidai tunanin ka kaga zubewar mutuncina akan auren da ko shekara beyi ba?" Dr. Omar na Shirin tashi yace, "idan ta Abba ne ki rubuta duk wani kudin aikin da kikayi Masa na samun sauki da zarar ya fara mgn ni Kuma zan biyaki shi dama nasan tun da Kika fara rawar jiki a kansa nasan cewa badan Allah kike ba kinayi ne Dan ki samu kusanci a gareni Wanda hakan Kuma bazai taba yiyuwa ba Dan kar nake kallon komai, lkci kawai nake jira na samo matar data dace Dani" ya karasa mgnr Yana tafiya kafin ya fara taka stairs ko waiwayen ta ba yyi, Bin bayansa tayi da kallo harya kule ya shige daki Bata daina kallon hanyar stairs din ba, zuwa yanzu gaba1 kukan da take ya daina zubowa samun kanta tayi da tashi ta wuce dakinta tana Shiga ta fara jawo tsohuwar Trolley dinta da tazo da ita, sai yanzu ta fara tunanin irin auren cin mutunci da Dr. Omar din yyi da ita, auren da Babu sutura bare kayan kwalliya, zuciyar ta ce take zugata akan kawai ta tafi, gwara tabar Masa gidan yaje ya auri wacce yake so din, zuciyar ta Banda zafi ba Abinda take, harta fara zuba kaya a Trolley dinta tunanin Abba ya fado Mata, wani irin tausayin sane ya sake Kama ta harga Allah take tausayin bawan Allah Nan Amma tsabar wulakanci Dr. Omar ya dubi kwayar idonta yace Wai Dan neman kusanci take Yi, ranta ya baci sosai saidai tana so taga samun saukin Abba domin ta fara ganin Alamar hakan, a hankali ta sulale kasa wasu irin zafafan hawaye na kwarara a Kan kumatun ta, ta Rasa wacce irin rayuwa take ciki, gidan ubanta bataji Dadi ba yanzun ma gidan mijin Bata more ba a maimakon aga tayi kyau tayi haske saima sake ramewa da tayi da baki danma jikinta ba me nuna Rama bane shiyasa ake ganin ta Kamar a cike, sbd yadda take kwana da tashi cikin razana da firgici. Rana Bata karya saidai uwar Diya taji kunya Yau ta kasance Saturday inda dubban manyan kusoshin masu kudin Nigeria da wasu na mutanen ketare suka halarci daurin auren Sageer Abdullahi Omar me fata da Amaryar sa Shafa'atu Ibrahim Usman dake sun boye sunan mahaifin su na Asali shiyasa sukayi amfani da sunan dad bikin da ko Dangin ubansu Basu San dashi ba mom tayi hakan ne sbd tana tsoron kada a samu cikas a auren itadai burinta kawai ayi a daura, fadin irin watsewa da shagulgulan da akayi a Wannan bikin ba'a mgn domin a Wannan ranar ma Faisal ya angwance da Amaryar sa Jamila. Saratu ce ta fito daga bangaren da take zaune na masu aiki taci ado za'aje mother's Eve kalar lace din da su mom suka fitar me mugun tsada da kudi kusan dubu 100k shine a jikinta itama ta saka, tun daga wajen masu aikin ake binta da kallon mmki, zata shiga part din Hajia Aisha kenan Hajjaju ta jawota da sauri Tace, "Saratu, ko ba Saratu bace?" Tayi mgnr tana kallon kayan dake jikinta Saratu na washe baki Tace, "nice Hajjaju wani Abu kike bukata?" Ja baya Hajjaju tayi tana tafa hannu tace, "ke kuwa Saratu a Ina Kika samu uban kudin da Kika dinka kayan da iyayen yaro zasu saka?" Fara'ar Saratu ce ta fara raguwa zuwa bacin Rai waigawa baya tayi taga har an fara taruwa a wajen abinka da Taron biki, Saratu tace, "haba Hajjaju yanzu Dan nayi ankon iyaye shine abin aibi a ciki?" Daidai lkcn su Mummy da frnds dinta suka fito hajiyoyi dasu Wanda Suma ake damawa dasu a duniyar naira wata daga cikinsu tace, "Hajjaju wacece Wannan din?" Hajjaju tace, "wacece kuwa idan ba 'yar aiki ba?" Fuska a hade wata kosasshiyar Hajia a ciki tace, "Kan uban Nan ankon dake jikin mu shine Wannan jemammiyar me aikin tasa itama a jikinta?" A rude Saratu ta dubesu tace, "Dan Allah kuyi hakuri Nima Sageer Kamar da ne a guna Koh Hajia?" Ta Kare zancen nata Kan Hajia Aisha da ranta yyi mugun baci sbd kunyar data Bata gaban frnds dinta wasu ma matan Alhazai ne abokan daddy dake Hulda dasu, a tunzure Hajia Aisha Tace, "sbd Yana Kamar da a wajen ki sai akace danki ne? Meyasa Kika fiye Shiga sabgar da ba'a saki a ciki ba?" Sakin baki Saratu tayi tana kallon Hajia Aisha data rufe Ido ta fara zabga mata fada, a tsorace tace, "Dan Allah kiyi hakuri hajiya ni duk bansan hakan zai Bata muku Rai ba" Rai bace Hajia Aisha tace, "yanzun Nan basai Anjima ba nakeson kiyi maza ki cire kayan dake jikin ki idan ba so kike ki fuskanci mummunan hukunci daga gareni ba" gaba1 Saratu ta rude Bata taba zaton Hajia Aisha ta iya fada bare masifa ba sbd rikicewa tun daga wajen ta fara cire dankwalin kanta da taci gwaggwaro tana tafiya da sauri takalmin data sa Medan tudu shima ta gurde garin sauri saura kadan ta Fadi zanin dake jikinta duk ya harde ta hakan yasa ta figse zanin ya rage Mata daga ita sai fatari tana tafe tsingil-tsingil cikin Taron biki, ai kuwa me mutane zasuyi mata idan ba dariya ba sai gulmar ta ake wata na cewa ni da farko ma Dana Zo bikin na dauka itace uwar ango yanda Naga duk Abinda akace Ina uwar da indai Hajia Aisha Bata wajen zaka ga tayi tsugul Tace Gata Ashe 'yar aiki ce gsky ta zaqe dayawa, Nan mutanen wajen suka Amsa da cewa tabbas hakane anan dai akaci gaba da mgnr Saratu masu dariya nayi, Hajjaju ma tuni ta koma part dinta tun bayan data Gama Shan dariyar tafiyar Saratu, Hajia Aisha dai a kunyace ta bawa frnds din nata hakuri kafin suka fara shigewa manyan motocin da zai kaisu hall din da aka Kama na Iyaye, Saratu na komawa inda 'yan aiki ke zama taci sa'a ba kowa a dakin da suke, cire kayan tayi tana share kwallar takaici data fito Mata, kallon kayan tayi tana tunano yadda akai ta samu kudin data dinka su, duk kudin da take karbewa a wajen Omar dana aikinta da Wannan bikin da aka fara ta zama itace Kan gaba wajen siyo abubuwa anan ta samu damar Tara kudi me yawan gske, da munafurci da gulma Haka ta samu damar sanin kalar ankon dasu Hajia Aisha zasuyi, ta girgiza dajin kudin lace din Amma data tuna auren danta ne bana uban kowa ba sai taji itama dole tayi ankon tunda itace uwarsa ta Asali, wani irin hucin takaici tayi tana Muzurai, gaba1 ba Wanda tafi Jin haushi irin Hajjaju duk ta Bata mata shirinta Dan Ada niyyar ta tayi sauri ta saje cikin manyan Mata batare da an fahimci tana wajen ba, Tsaki ta Kara ja a Karo na Babu adadi tanajin Kamar taje ta shake Hajjaju ta huta. Bangaren su Anty shafa ma abin ba'a mgn domin wani irin uban bashi Mom taci Dan ganin kawai sun fita kunya a idon surukai, dukda Dad ya Basu kudi hakan be ishesu ba domin komai karya suke zubawa a ciki Suna ganin kamar sun kusa kamowa su Sageer komai da komai, Adan kwanakin Nan ne ma Dad yake Dan rike Aljihun sa idan Mom tayi Masa mgn Saiya Musa mata yace su Ina nasu uban da bazaiyi musu ba? Ranar daya fara Furta mata hakan hankalin ta ba karamin tashi yyi ba domin tasan baya Mata mgnr ubnsu kwata2 sbd tasa an kawar Masa da Wannan tunanin, sannu a hankali ta fara fahimtar canjawar Dad Abu kadan zai zugeta da fada batare da abun yakai ayi fadan a kansa ba, Wannan sabon canjin na dad ba karamin sake hargitsa tunanin Mom yyi ba ga biki ya shigo gadan2 hakan yasa take lallabawa a samu a Gama bikin duka kafin tasan bakin inda zata Kama bakin zaren Fitowar dad daga Wanka kenan Mom ta shigo dakin nasa, kallon ta yyi ya watsar Mom tace, "Haba Alhaji kwana biyun Nan sai Naga kamar kana fushi damu" be kulata ba yaci gaba da shafa man da yake, matsowa tayi tana cire wani ganye daya makale Masa a baya daidai lkcn ya jiyo da sauri zaiyi mgn ta aje Masa ganyen Kan mirror dake gabansa Tace, ,"cire maka nayi gashi Nan" ta furta hakan tana nuna Masa ganyen, kallon ganyen yyi ya fahimci na miye Saiya dauka yaje can windows sa ya jefar, Yana dawowa ya fara saka kayansa Saida ya Gama still Mom na bakin gado tayi tagumi tana jiransa ya Gama, Yana gamawa kuwa yayi hanyar fita batare da yyi mata mgn ba, da sauri Mom ta Mike cikin kasa da murya Tace, "Alhaji tun dazu fa Kai nake jira?" A tunzure yace, "meye Wai?" Ya karasa mgnr Yana kallon ta Haka kawai 2days dinnan yakejin haushin duk mutanen gidan gaba1 mom ta Dan risinar da kanta kasa Tace, "Dan Allah idan ma lefi nayi maka kayi hakuri dama yaran Nan ne zasu Zo kuyi sallama ka tsaya ka saurare su kamar yadda ka Saba a baya Dan Allah" tsaki Yaja Yana Kama handle din kofa yace, "idan har sai sunyi min sallama ne zasu bar gidan Nan Toh karsu tafi suyita zama" yyi mgnr Yana bangaje rikon da tayi Masa kafin ya fice daga dakin, dukda Ana Taron biki hakan be Hana dad zuwa parking space ya dauki motar sa hade da barin gidan gaba1 ba, Mom ba karamin rudewa tayi da Wannan abun daya auki tsakanin ta da dad ba, Tasowa tayi hankalin ta a mugun tashe har zata fito daga parlon nasa ta tuna jama'a nacan suna jiranta akai Masa su Anty shafa, da hanzari ta dakata tana me rike kirjinta dakyar ta samu ta danne duk wani tashin hankalin da