← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 128

Sashe 121

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

hakan Yana Masa mugun kallo yace, "Allah ya sauwake ba Dani za'ai Wannan shirmen ba" Sadeeq yace, "Kai Al'adace fah" Omar yace, "Farilla ko Sunnah?" Sadeeq ya girgiza Kai yace, "ba ko daya" Omar yace, "fine, Dan Haka Kama zare mgnr rakiyar Nan" dariyar sa Sadeeq yyi yace, "mutumina Omar Allah ya Barni Naga har jikokin mu" Omar na murmushi yace, "Ameen." Bayan sallar magrib daddy da Mummy suka Tara Ameera da Ameer sukayi masu fada sosai me ratsa jiki da jijiya, Meera batayi mmkin su ba dama tun farko sbd kaf Inna fure ta labarta mata Abinda ya samu Omar din Ashe Abba ba shine asalin mahaifin sa ba gsky ta tausaya Masa matuka Dan har kukan tausayin sa Saida tayi, Bayan an gama Yi masu fadan ne Mummy ta kamo hannun ta zuwa wajen Hajjaju a parlo suka tarad da Safna na jiransu Dan tunda taga Meera ta manne mata tanayin Nan2 da ita, tare sukaje bangaren Hajjaju itama fadan dai ta musu me ratsa jiki da jijiya kafin Nan suka dawo gun Mummy, kaya Mummy ta Bata ta canja Bayan ta Sata sake wanka, Shigar da tayi ya matukar amsar ta kwarai, Safna ce ma me mata daurin zamanin Nan Dan Meera Zama dasu Anty shafa aka maida ta 'yar aikin dole yasa Sam abun kyale2 Nan be hau kanta ba, tayi kyau kwarai tana fitar da wani irin kamshi me ratsa zuciya, dake bawai Kai tsaye za'ace mata amaryar farko bace Haka yasa da kansa Omar din zaiyi driving dinsu zuwa can gidansu, har bakin mota su Mummy suka rakata Dr. Omar na kallon ta daga nesa harta shigo ciki kanta da lullubi sai kace ranar farkon Aurenta, leko kanta Mummy tayi Tace, "na rokeka Ameer ka rike amanar yarinyar Nan" Dan murmushi yyi mata kafin yace, "Insha Allahu" murmushi tayi tana duban Meera data dukar da kanta ta lura yarinyar tana da kunya sosai Tace, "Daughter Saida safe" Meera ta Dan dago a kunyace tana gyada Kai, matsawa Mummy tayi Safna dake bayanta Tace, "Anty Ameera saina Zo" murmushi Meera tayi mata Safna ta daga mata hannu Alamar bye, Suna tsaye kuwa Dr. Omar ya fara tuki a hankali harya fice daga gidan daddy na hangen su daga can sama badan aure ba yaushe zakayi nesa da yaronka? Saida suka bar bangaren area su Dr. Omar ya tsayar da motar sa Yana parking a gefe, har lkcn Meera Bata dago ta dubeshi ba shima Kuma bece komai ba Kawai ya nade hannun sa a kirjine idonsa a kanta, Jin Shirin yyi yawa yasa ta dago kanta taga ita yake kallo, da mmki murya na rawa tace, "ya Omar lpy ka tsaya?" Hmmm ya saki ajiyar zuciya Yana me dafa hannun nasa a steering yace, "haba yanzu na farajin daidai" Meera Tace, "kamar ya?" Dr. Omar yace, "tun da Kika shigo baki min mgn ba bayan kin sani Sarai ba Abinda nafi kaunar naji sautin muryar sa sama da Taki babe" dukar da kanta Meera tayi tana wasa da hannayen ta, itafa tun farko dama a tsorace take tunda akace ta fito su tafi hanjin cikinta yake kadawa ko farkon Aurenta Bata tsorata kamar yanzu d kome zatayi ba, Kashe motar yyi Yana kokarin maida kujerar baya yace, "da alama zamu kwana anan tunda mgn ma yau babe Taki min" Dagowa tayi da sauri tace, "No ya Omar muje gida pls" murmushi ya sakar mata yace, "you're right dear gwara muje gidan Kam" ya karasa mgnr Yana tada motar, kasa janye idonta tayi daga gareshi kamar daga sama taji yace, "kinyi kyau babe, kamshin ki ya sani kasala, kallon da kikemin ya jefani wani yanayi harnaji inason mu kasance a gidan" ya Kara mgnr Yana Juyowa hade da kashe mata Ido daya, Ya Salam! Anya Dr. Omar din data sani ne ko kuwa wani aka canja mata? Ta Fadi hakan a ranta tsoro na Kara Shigar ta, murmushi Omar yyi be Kara mgn ba har suka kaiga gidan nasu, mmki ne ya sake Kama Meera data lura ba gidansu nada sukaje ba, wani tamfatsetsen gidan na gaban kwatance dayafi Wanda suka baro sau biyar Omar ya Danna hancin motar sa ciki, Wow...wow..Nan Meera ta Wara Ido sosai tana kallon Aljannar duniya.
Chapter 121 · 0% Book details