Sashe 40
Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
****Rana Bata karya saidai uwar Diya taji kunya, Yau take Friday inda mutane da dama suka halarci daurin auren Dr. Omar salees da amaryar sa Hafsat Ibrahim, dukda duka bangaren basuyi wani gayyata ba hakan be Hana samun mutane sosai ba, Acan cikin gida kuwa Ameera tana cikin daki tun kwana biyu saura biki ta gama shirya kayanta a akwatin da Su Aunty Shafa suka Bata kuncen sa ta wanke 'yan kayanta tsaff ta shirya su a ciki ko Dan lalle Nan na amare batayi ba, Haka zalika Babu wani gyaran jiki abin dai gashi Nan Salam, Kamar yadda Dad yace kafin magrib akazo daukar amarya da mota daya motar ma Sadeeq ne a ciki yazo daukar ta Dan Dr. Omar kekasa kasa yyi yace bazai zo ba Dan Wannan Bata lkci ne. Meera na sama taji ance tazo suyi sallama da dad kafin su wuce, Tasowa tayi a sanyaye tabi Bayan mom data kirata dukda tasan yanayin auren nata yadda yazo Amma batayi tsammanin zata kasa samun Koda 'yan uwan dad ne bare nata dake can Adamawa, matan dake gidan daga su mom sai su Surry da sukazo Suma gulma ce ta kawo su dandai kawai suga inane gidan amarya? Da Wannan tunanin nata suka Isa parlon dad, Yana zaune ya kunna Tashar CNN Yana kallo, Fita mom tayi Dan Basu waje, Saida aka dauki seconds masu yawa kafin Dad Yyi gyaran murya yace, "Ameera" "Na'am Dad" Ta Amsa Masa muryar ta na rawa, Duban ta yyi yace, "inaso ki bude kunnuwan ki sosai sbd Jan kunnen da Zan Miki" girgiza Kai Meera tayi tana me Dan share siririn hawayen daya sakko Kan kumatun ta, Dad yace, "ni bansan yaushe Kika canja ba Ameera, kin bani mmki kina 'yar Karama dake Amma kinsan kibi maza" Dagowa kanta tayi da mmki tana kallon sa, Rai ya hade sosai yace, "karya aka Miki? Inace sbd abun kunyar da Kika jawowa kanki aka koreki a skul?" Tsananin mmki ne ya Kama Meera au Dama sharrin dasu mom sukayi Mata kenan? Ita yaushe aka koreta? Dad ne yaci gaba da fadin, "Dan haka Wannan auren shine hukuncin ki, idan mijinki ya barki sai kici gaba da karatu a gidan sa domin yanzu shi yake da iko da ke, Kuma Ina Kara gargadin ki ki rungumi auren Nan naki dakyau duk rintsi kada Naga kafarki anan kin kawo korafi, Bana bukatar Jin komai daga gareki, matukar kikayi sake auren ki ya mutu da wuri sbd shashanci ki sainayi sadakar ki acan kauye, kauyen ma irin Wanda mota Bata iya Shiga" Share wasu zafafan hawaye Meera tayi zuciyar ta na zafi kiri-kiri take ganin ikon Allah game da dad dinta, Kai kace bashi bane me matukar son natan Nan, kamar bashi bane me kulawa da ita ba, Allah sarki rayuwa kenan Sihiri gskyr meshi, A fili kuwa bakinta na rawa Tace, "shikenan Dad Insha Allahu bazan taba baka kunya ba zanyi kokari na rike aurena kamar yadda ummana tayi har izuwa karshen rayuwa na Nima" ta karasa mgnr hade da fashewa da kuka sbd tunowa da umman nata da tayi, Dan dam dad yyi yanajin wani iri a ransa, Dan tausayin tane yaji ya darsu a ransa, sosai ya fara jiyo kamar an danne zuciyar sa d wani katon Abu kasa Furta Mata komai yyi Dan Haka ya mika Mata wasu kudi hade da fadin, "sadakin ki ne" ya Furta hakan yana me nuna Mata kofa da hannu, tashi Meera tayi Bayan ta karbi kudin ta share hawayen ta kafin tayi Masa sallama daidai zata fita kuwa suka hadu da mom Nan taja hannun ta suka fito waje, su Anty shafa duk sun Gama shiryawa kowa so yake Meera ta fito aje aga gidanta, kilama gidan haya ne irin gida masu yawa toilet dayan Nan, Haka dai sukayi ta lissafi har sukaje bakin gate inda Dr. Sadeeq ke jiran a kawo Masa amarya su tafi, Yana daga cikin mota Amma mmkin su yake yadda yaga sun nufo gurin motar a ransa yace badai hardasu za'aje ba? Lalle da sun hadu da fushin Dr. Omar Dan yadda yake Jin haushin su zai iya babbala su, Suna isowa suka buga masa mota, Meera na gefe tana Dan share hawayen ta, zuge glass Dr. Sadeeq yyi Yana dubansu sama da kasa kowacce taci kwalliya Ana taunar chewing gum kamar zasuje party, Dan kasa yyi da glass dinsa fuskar sa a daure yace, "Ina amaryar?" Anty Jamila tace, "saurin me kuke? Bayan Gata can gefe jira muke ka bude kofa mu shigo da ita" zare gaba1 glass din Dr. Sadeeq yyi Yana binta da mugun kallo Babu fara'a Sam a fuskar sa yace, "me kuke nufi?" Shan jinin jikinsu sukayi Dan sun gane Dr. Sadeeq din frnd din Omar ne zani ne ta tadda muje Dan dukkansu ba kanwar lasa bane na Dr. Omar dinne yafi zafi, Hakan yasa Anty shafa tadan daure tace, "rakiya zamuyi ka bude kofar kada dare yyi" Mtwss Dr. Sadeeq Yaja tsuka Yana me maida glass din idonsa yace, "No need" Afra ce tace, "haba bawan Allah an taba Kai amarya ne ba 'yan rakiya? Kasan ko Dan zuwa gaba sai muga gidan nata basai munyi tmby ba" kunna motar Dr. Sadeeq yyi Yana me fadin, "ganin gida ko ganin gulma? I know Abinda zai kaiku kenan shiyasa nace no need domin Abinda kuke hasashe ne gidan hayane me dauke da mutane 15 a ciki" dafe kirji sukayi har suna hada baki wajen Furta, "Sha biyar?" Ko kallon su Dr. Sadeeq beyi ba ya fara matsawa da motar a hankali zuwa baya, be tsaya ba har Saida ya dangana da inda Ameera ke rakube tana goge hawaye, Lekowa yyi inda take yace, "Amarya bude Bayan mu tafi dare nayi" ya Furta hakan Yana duba agogon hannun sa, kamar jira kuwa take haka tabi umarnin sa ta Shiga tana rufe kofa kuwa saigasu Anty shafa sun karaso wajen da sauri hakan yasa Dr. Sadeeq ya sawa motar lock Babu damar budewa, "Yau munga Tsiya" suka Furta hakan suna dariya, badesu da kura Dr. Sadeeq yyi kafin ya fisgi motar a guje Kai kace wasan tsere zaiyi, Habawa tuni suka fara tari suna Kade kurar jikin su Duk kasa ta shige musu Ido da hanci hakan yasa garin fitar da kasar ya jawo duk kwalliyar da sukayi ta cabe sai kace dodanni, "Allah ya Isa shege me Kan kwakwa" Anty shafa ta Furta cikin jin haushi tana tari, Atishawa sauran suka farayi Dan har wani yaji2 sukeji a hancinan su da Ido ba shiri suka bazama cikin gidan a guje kowa na haki kamar Wanda sukaje yaki.