← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 128

Sashe 97

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar sabuwar kamu?" Cije lips dinsa Omar yyi yanajin zuciyar sa na tafarfasa dakyar ya samu damar furta kalmar, "mun rabu" ya Fadi hakan a takaice, saura kadan Sadeeq ya saki steering motar da yake ja bakinsa na rawa yake fadin, "Innalillahi....." Ya furta hakan hankali tashe yace, "Omar Wai yau wacce irin ranace Kam? Daga aure jiya sai aji Kuma kun rabu? Dukda dama can bana supporting dinka a auren Salma Amma be kamata ace ka yanke Wannan danyen hukuncin ba" Kawar da kansa gefe Omar yyi Yana ganin kamar Sam Sadeeq be fahimci komai ba, Sadeeq ya katse shirun da Fadin, "Gsky ya kamata kafin kumai ya sake baci daga Nan mu wuce gidansu Salma kar mutunci ya zube" Juyowa Omar yyi Yana binsa da wani irin mugun kallo yace, "tabarya da zanin zanbi? Kai bakaga wucewar ta bane?" Ya Fadi hakan a zafafe, shiru Sadeeq yyi sai yanzu yake tuna a yanayin daya ganta tabbas badan mlm habu ya Tabbatar Masa da ita bace bazai gaskata hakan ba, Juyowa yyi da sauri yace, "Kamar ta rage kiba a Daren jiya ko idona ne?" Cije lips dinsa Dr. Omar yyi bece Masa komai ba saima zubawa gabansu danjar data tsayar su Ido, Sunkuyar da kansa Sadeeq yyi Yana Dan buga steering a hankali, sai yanzu ya fara fahimtar komai idan yyiwa abin fashin baki kenan fa Salma da ciko ta Shiga gidan tunda kowa ya ganta Saiya shaida manyan hips dinta Amma dazu ba komai saima zani da take ta tattarowa Yana zamewa, dukda shima Yana cike da Alhinin Abubuwan dake samun Omar tun Bayan wayewar garin yau hakan be Hana shi Jin wata irin dariyar Omar din b, wacce taso fitowa ya danne sbd yasan yanzu ba anutse yake ba karya sake kunna Masa wata gobarar takaicin Kuma, damar wucewa aka Basu Nan ya ci gaba da tuki kowa na tunani a ransa shi kadai, gaba1 Omar ya manta da batun daddy yace aje da surukar tasu dukda be banbance ba Dan yasan Abba ya Gama masu bayanin Mata biyu gareshi, a Haka suka Isa cikin gidan Bayan sun fito a mota ne sukaga tahowar Safna da sauri, dama tun dazu sai leka bakin gate take tana jiran zuwanshi, da murna ta Isa gareshi tana Kama hannun sa tace, "ya Ameer ka barmu munata missing dinka" ta Furta hakan cikin shagwaba abinka da Auta, Saida yyi ta maza kwarai da gske kafin ya samu ya tattaro duk wani kalen murmushin sa ya sakar mata yna dubanta Yace, "da alama d ban iso ba biyoni zakiyi" Safna tana 'yar dariya Tace, "sosai ma kuwa muje ciki duk fa mun hallara only my one and only big bro ake jira" ta Fadi hakan tana kamo hannun sa, juyawa Omar yyi da nufin yiwa Sadeeq mgn sai yaga gaba1 hankalin Sadeeq din Yana Kan Safna, Dan murmushi yyi yace, "frnd muje" sai a lkcn Safna ta juya gefenta da sauri karaff kuwa suka hada Ido da Sadeeq din take taji wata irin kunyar sa ta Kama ta, cikin hanzari Tace, "sannu Ina wuni? Yauwa ku shigo" ta Fadi hakan da sauri tana juyawa ko hannun Omar din Bata sake rikewa ba, still Sadeeq nabin bayanta da kallo harta bacewa ganinsu kafin yyi firgigit Yana dawo da kallon sa Kan Omar daya nade hannun sa a kirji Yana kallon sa, Dan shafa keya Sadeeq yyi Kamar Wanda yaji kunya yace, "tsayuwar me muke muje Mana" yyi mgnr cikin basarwa, Dan murmushin gefen baki Omar yyi yace, "tunda ka Gama kallon ta dole kace muje" Sadeeq yace, "banson sharri yaushe kaga na kalleta?" Omar na tabe baki yace, "idan ka Gama gulmar saina fada maka" yyi mgnr Yana yin gaba, Dan murmushi Omar yyi shima yabi bayansa, suna shiga parlon kuwa duk suka tarar da Ahalin gidan a parlo har Hajjaju ga Abba shima cikinsu ya ware sunata Hira Ana bada lbri suka karasa garesu Bayan sunyi sallama, Hajjaju dake zaune Tace, "maza taho Nan angona ai yau nice Nan matar" ta Fadi hakan da sigar tsokana, Dan murmushi Omar yyi duk yanajin sa wani iri sbd be Saba da hakan ba, daddy ne yace, "Toh muje daga Kan dining Koh" yyi mgnr Yana mikewa, Nan kowa ya Mike suka nufi dogon table din da aka gyara me dauke da kujeru dayawa, Sadeeq Kam tunda ya shigo parlon hankalin sa ke Kan Safna ya kasa daukewa sai kallon ta yake a sace, duk Omar na lura dashi ta Wutsiyar Ido jira yake su fita ya Masa tsiya, mummy ma dai Dan satar kallon Dan nata take duk tausayin irin Rayuwar daya taso take abun tausayi. Bayan dukkansu sun zauna ne Daddy yace, "Omar Ina surukan namu?" Daraaaamm..., Kirjin Omar ya buga da karfi dannewar tashin hankalin sa da yake ta boyewa tun dazu ya fara kokarin bayyana karara Kan fuskar sa, yyinda kuma na wajen duk suka zuba Masa ido suna jiran Jin ta bakinsa, shi kansa Sadeeq yanzu a tsorace yake da tmbyr da aka yiwa frnd din nasa take ya fara tunanin ya za'ai su samu Mafita, Dr. Omar kuwa daya Gama yanke shawarar abinda zai fada kawai ya dago kansa dadan murmushin yake zaiyi mgn kenan Sukaji an banko kofa, dukansu juyawa sukayi suna bin bakin kofar parlon da kallo, mutanen da suketa shigowa ne yasa fuskar su ta bayyanar da madaukakin mmki, cikin bacin Rai daddy ya Mike Yana duban masu damarar da suka Gama shigowa parlon gidan yace, "Kai wa'anne irin marasa hankaline ku da zaku shigomin gida tun daga bakin gate har izuwa parlo?" Maimakon masu damarar su amsawa daddy sai Jin muryar Sageer sukayi Yana shigowa hade d mgn da karfi yace, "ninenan na daukosu domin su Kama wa'ancan matalautan mutanen da suke ikrarin Kaine mahaifin sa" A zuciye daddy ya Isa gareshi batare da tunanin komai ba yahau kikkifawa Sageer Mari wani daga cikin masu damarar ne ya riko shi Yana fadin, "ayi hakuri Alhaji" Alhji Abdullahi ransa na zafi yace, "ko kunyar kanka da kanka Bakaji ba Sageer? Bayan wulakanci da cin mutunci da kuka Gama yiwa gudan jinina Kai da uwarka shine yanzu zaka sake zuwa ka tozarta shi??" Hannun Sageer na kumatu ya saki dariyar shakiyanci yace, "Wallahi karyane a Rasa Wanda za'a hadani da ita sai Wannan jemammiyar? Kai daji karya suke maka daddy nine Nan danka gudan jininka, Kai daddy baka ga tarin dukiyar da kke da ita bane? Kana tunanin da ace baka da ita akwai Wanda zaizo ya maka karyar jinin ka ne?? Sbd tsabar ka tsaneni shikenan daga zuwa sunyi maka tatsuniya saika amince Kamar baka da Yara haba daddy Kamar baka Shiga aji ba? Mayaudara nawa suke a duniya??" cikin zafin Rai daddy yace, "ni kke gayawa Haka Sageer? Rashin hankalin naka haryakai ka zageni?" Ya Fadi hakan Yana Shirin dukansa Dr. Omar dake bayansa zuciyar sa na tafasa ya riko hannun daddy ta baya, kallon sa daddy yyi bacin Rai karara a fuskar sa yace, "Dana Omar kada zancen wanna yaron ya Shiga ranka, tun kafin nasan kaidin dana ne muka aminta da junan mu a Matsayin uba da 'Da bare yanzu da haske ya bayyana." Sageer ne ya tsoma baki da fadin, "ahaff Kun gani Koh? Wannan mutumin abokin adawata ne tun muna skul nasan zafin korar Dana sa akai Masa ta jawo yimin gugar zana da alama wajen wani kasurgumin bokan sukaje aka juyar min da hankalin mahaifi" "Malafar ubanka Sageer" Hajjaju da ranta itama ya baci sosai ta Fadi hakan tana nuna Sageer tace, "kaci Bantan ubanka shege gantalalle marar mutunci ka kallesu Tass dukkanmu farare ne Babu baki a cikinmu Kai tun iyaye da kakanni kowa ya shaida Dangin farare ake kiranmu Babu baki mummunan me donono hanci kamar malmalon tuwo irinka, Banda raini da Rashin kunya Meka iya?" Sageer yace, "dole ki Fadi hakan man tunda ya juyar muku da tunani" a tunzure Dr. Omar ya riko hannun Abba da tun dazu yake share kwallar bakinciki Yana kallon Sadeeq da shima ransa ke bace yace, "muje" tirjiewa Abba yyi Yana fadin, "ya za'ai da girmana da mutunci na nazo na shirgawa manyan mutane karya? Me akai akayi dukiya abinda zamu barta a duniya?" Kai Dallah malam ware kana Nan Dan kyamurmur yunwa ta Gama kodar dakai ai komai ma zaka iya Yi Dan kusamu ku..." Zancen dabai karasa ba kenan Dr. Omar ya daukeshi da wani irin mahaukacin Mari zuciyar sa na turiri, a gigice Sageer ya dafe kumatun nasa har tafin kafarsa yake Jin sautin azabar da kumatun sa yake bare kunnuwan sa da suka dauke na wani lkci, Kokarin kifa Masa wani Marin yazo Yi babban cikin mutanen da suka Zo yyi azamar rike Omar kadan ya rage kuwa Marin ya samesa ya zame a tsorace kwarai ya girgiza da zafin Naman Omar Kai kace shugaban sojane a gabansu, ganin abin na neman lalacewa ne yasa shi saurin Shiga tsakiyar su Fadi yake, "Dan Allah kuyi hakuri muyi mgn" Sageer da yake share jinin bakinsa yace, "Wallahi Allah Saiya biyani jinin daya zubar min Haka kawai Dan tsabar bakin talauci na cinsa zaizo har gidan ubana yace nasa ne?" Rintse ido Omar yyi da karfi yanajin Kamar ya kaiwa Sageer naushi yaji babban masu damarar yace, "Alhaji Wannan mgn fa ba karamin case bane Abinda nake gani shine zamu je hospital dukanku ayi muku DNA kowa a Tabbatar da gskyr sa duk Wanda ya zama shine jininka sai daya yyi hakuri.
Chapter 97 · 0% Book details