Sashe 125
Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
rayuwa me Kama data mafarki, Ina fatan hakan ya zama izina ga 'yan baya, kazalika Shi Sageer zamu daure shi na shekara biyar domin yaso lalata Rayuwar baiwar Allah Kuma bincike ya nuna Haka halinsa Yake tun ba yanzu ba sannan yyi kazafi ga Wanda beji ba be gani ba ya Bata Masa Suna akan wani buri nasa na daban Dan haka zai kawo tarar kudi naira dubu dari biyar, Faisal, Shafa'atu, Jamila ku da kuka assasa wajen faruwar lamarin zamu daureku na wata shida a gidan yari tare dacin tarar dubu dari kowa, ku Kuma bangaren karatun Omar masu hukunci ba bisa ka'ida ba hukumar makaranta tayi Zama na musamman a kanku duk Wanda yake dasa hannu yaje ya duba notice board an koreshi daga aiki Haka zalika takardun sa bazasu sake aiki a wata ma'aikata ba Ina fatan hakan yasa sauran lecturers su dauki darasi akanku" Nan fa Kotun ta sake rudewa kowa na tofah Albarkacin bakinsa, Saratu da nas ihu suke Suna zagin juna, su Anty shafa Banda kuka ba Abinda suke mom Fadi, "take Kun jamin asara da haihuwar ku gwara Babu Wlh Allah ya Isa" a tunzure Anty shafa Tace, "waike mom da kike fadar hakan duk waye silar fadawar mu Wannan Halin?" Anty Jamila Tace, "saidai mu muce bamu yafe ba Dan bamuyi sa'ar uwa ba" mom tace, "ni kuke gayawa Haka? Dana dauko ku daga kauye na kawo ku birni?" Anty shafa na share hawaye Tace, "na rokeki da girman Allah ki koma kauyen ki nemi babanmu ya taimaka Mana Dan da alama kema yanzu bakida shi. acan bangaren su Dr. Omar da Meera kuwa a sulale Yaja hannun sahibar sa suka fece daga ciki tun kafin a Gama shari'a ace za'ayi Hira dasu, su daddy da Mummy fuskar su cike da Annashuwa koba komai an rage musu radadin Abinda Saratu ta musu duniya ta shaida kowa yasan Abinda ake ciki, Alkali ya bada damar a Tisa keyar masu lefi, Saratu sunzo giftawa ta hango Abba da sauri ta Kira sunan sa tana fadin, "nasan rokona bazaiyi amfani ba Amma Dan Allah kaje gidan Nas Sahabatu nacan haihuwa yau Koh gobe kace ta yafemin" ta Fadi hakan tana kuka aka tura keyarta, Wannan shi ake Kira Ana wata ga wata tsabar bakin ciki ma Abba kasa Dagowa yyi yarinyar da beyi Mata aure ba Wai itace haihuwa yau ko gobe? Kai Gsky haduwa da Saratu bala'i ne, bayan Jan hankali da nasiha da Alkali yyi Nan ya buga guduma kowa ya watse Toh daga Nan fa 'yan jarida suka Fara tururuwar son daukar rahoto. Dr. Omar da Meera can gidan su daddy suka yini sbd daddy ya bukaci ganin Omar din, sun Dade a parlon daddy su biyu sunata lissafi da cike2 takardu karshe dai sai bayan magrib suka bar gidan, can wajen dad sukaje Yi Masa sallama yana kofar gida ya gansu, Omar ya sanar Masa garin zasu Bari dad ya tarbesu da murna kwarai ya Kuma Kara jajanta musu dayi musu nasiha me ratsa jiki, wajen Abba sukaje shima sun Dade sosai kafin daga Nan suka wuce gidansu Sadeeq Hajian Sadeeq tayi murna da ganinsu kwarai, anan yabar Ameeran shi Kuma ya tafi wajen Sadeeq, Sun dade Suna tattaunawa tsakaninsu, kafin sukayiwa gidan sallama akan da safe Sadeeq din zaizo musu sallama, dake yau din duk sun gaji gashi karfe 8am zasu bar gari shiyasa basu jima ba bcci ya dauke su, Wannan zaman da sukayi da daddy ragamar aiyukan daddy na kasashen waje Omar ya karba shikuma daddy ya karbi na cikin gida saidai kafin ya fara gudanar da aikinsa sai sunyi yawon shakatawa wato honeymoon. Washe gari kuwa kafin 8am Sadeeq yazo daukar su shi da Safna, Omar na ganinsu tare yyi murmushi Sadeeq daya lura da hakan yadan jashi gefe kafin yace, "Wannan munafikin murmushin fa na miye?" Dr. Omar yace, "ko ban fada ba ai ka sani yaushe aka jame?" Sadeeq yyi 'yar dariya yace, "lkcn da kke angoncewa Nima na yada manufa" dariya Omar yyi yace, "Allah ya shirya" Sadeeq yace, "Ameen" fitowa Ameera da Safna sukayi Nan suka shige motar su, a mota ma sai Hira suke a Haka har suka Isa airport Suna zuwa kuwa Basu Dade da zuwa ba aka Kira sunan su, Safna rungume Meera tayi tana fadin zatayi kewar su, Dr. Sadeeq da Dr. Omar ma suka rungume juna jikinsu a sanyaye Basu taba yin Wannan nisan ba abota tun yarinta, abota da aka ginata akan tubalin gsky, cike da kewar junansu sukayi wa juna sallama kafin suka juya zuwa inda aka kirasu, Suna waiwayen su har suka shige cikin jirgi su Sadeeq na daga musu hannu, Saida kowa ya Gama shiga kafin jirgi yyi sama dasu Nan suka nufi Paris kasar da zasu fara zuwa honeymoon. 8/27/20, 5:26 PM - Ummi Tandama: *kanki tsaye Zaki iya tuntubar Wannan Number 09039118754 domin Samun cmplt littafin nan�*