← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 128

Sashe 94

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ka fahimtar Dani Abinda ke faruwa Wlh gaba1 Kaina ya kulle duk kasa na Shiga fargaba" kokarin mayar da kwallar sa Abba yyi yace, "ni Kaina Omar a cikin fargabar nake, dolece ta sani hakan kayi hakuri kaji?" Cije lips dinsa Dr. Omar yyi Yana matse yatsunsa, daidai lkcn daddy yyi sallama, Amsa Masa sukayi daga Nan Kuma sai ga Hajia Aisha ta iso itama bakinta dauke da sallama, wani irin bugawar zuciya ce ta kasance tsakanin ta da Dr. Omar a lkcn da sukayi Ido biyu da juna cikin azama tayi saurin kawar da idon nata zuciyar ta na harbawa da sauri2 bayanta Safna ce da Katon hijab tana kumbura fuska Dan bcci take aka tasota, tana ganin Dr. Omar ta washe fuska sosai da murna ta Isa gareshi Fadi take, "ya Omar? Yau Kaine a gidan namu? OMG! Mummy shine fa GM na company da muke baki lbri Koh daddy?" ta karashe mgnr da sigar tmby gaba1 ta karade falon da surutu sai kace aku, yyinda mummy da Dr. Omar suka cika da tsananin mmkin juna, shikuwa Abba kawai kallon ikon Allah yake idan ya kalli daddy, Saiya kalli Mummy ya dawo ya dire kallon nasa Kan Dr. Omar, Daddy ne ya katse surutun Safna da fadin ta zauna kafin ya dubi Abba yace, "gashi mun taru saidai ba duka b Hajjaju tana bangaren ta kasan Sha'anin tsoffi tafiya tana wahala, babban Dana Kuma Yana zuwa" girgiza Kai Abba yyi kafin yace, "Toh Masha Allah, godiya ga Allah subhanahu wata'ala daya bani Aron Rai har izuwa kawo Wannan lkcn da nake tare daku." Shiru parlon ya dauka Ana sauraron Abba dake mgn kowa mmki ne dankare a ransa daidai lkcn Sageer ya fado parlon ba ko sallama, zuruf Dr. Omar ya Mike Yana kallon Sageer, Sageer shima da mugun mmki ya kafe Dr. Omar da kallo, daddy ne yace, "lpy dai Omar?" Dr. Omar na kallon daddy Yana kokarin danne zuciyar sa yace, "yaron ka ne?" Girgiza Kai daddy yyi, cije lips Dr. Omar yyi wasu irin zafafan takaici na safara a ransa ya maida kallon sa Kan Abba da yake kallon sa da mmki shima yace, "Abba tashi mu tafi" Abba yace, "meyasa kace Haka Bayan ban sanar daku dalilin taraku da nayi ba?" Shafa sumar kansa Dr. Omar yyi cikin Jin haushi yace, "Abba ni zan wuce idan kun Gama zan dawo mu tafi ko Menene zamu hadu ka fadamin" yyi mgnr Yana Shirin tafiya, saurin rikosa Daddy yyi Yana fadin, "duk me ya jawo bacin Rai Haka lkci guda? Ka sanshi ne? Koh wani Abu ya taba hadaku?" Dan cije lips Dr. Omar yyi kafin yace, "I'm sorry daddy but Ina tunanin lkcn barin aikina ne yazo yau" hankali tashe daddy yace, "Omar?" Lumshe Ido Dr. Omar yyi yanajin wani irin zafi a ransa harga Allah da yasan a karkashin mahaifin Sageer yake aiki da ko kadan beyi marmarin karbar aikin ba, yadda akai yyi sanadiyar barin karatun sa ne ya dawo Masa sabo sai yakejin haushi da bacin Rai na barazanar tarwatsa ransa sbd Kuna, Muryar Abba ce ta katse su da fadin, "Wai Omar meye matsalar?" Sai a lkcn Dr. Omar ya bude idonsa da suka fara rinewa daga fari zuwa ja ya dubi Sageer dake bakin kofa hankalin sa a mugun tashe Yana tsoron kada Dr. Omar ya sanar da daddy Abinda ya Masa a skul shiyasa duk ya gagara tsayuwa Yana fatan Omar din ya tafi, zuba Masa ido Dr. Omar yyi na wasu seconds kafin yace, "Abba ka tuna dalilin barina skul?" Abba ya gyada Kai Dr. Omar ya cije lips dinsa Yana kallon su duka yace, "ba kowa bane face Wannan mutumin" ya karasa mgnr Yana pointing Sageer cikin tsantsar takaici, "innalillahi wa'inna ilaihin raji'un" duka suka hau salati Mummy gaba1 ji tayi ranta ya mugun baci bare daddy dayake Jin Kamar yahau Sageer din da suka shikuwa Abba kwallar bakin ciki ne ta Kama shi sbd Jin yadda akai Dan daya Haifa ma halin uwarsa ya biyo wajen mugunta ga kamarta Nan a fuskar sa Banda mugun Asiri ma ai kowa ya ganshi yasan ba Dan gidan bane Dan kuwa su Dukansu farare ne tastas Kamar jinin larabawa, Fuska Sageer yyi ya juyar da kansa gefe saidai acan cikin ckinsa hanjinsa kadawa yake sosai, daddy ne ya kalli Dr. Omar yace, "I'm very sorry for...." "Bakai kamin lefin ba daddy meyasa zaka ban hakuri?" Dr. Omar ya katse Masa mgnr, daddy yace, "dole a baka hakuri sbd Abinda yyi maka Babu Adalci a ciki tun a lkcn da kace kabar skul naso sanin dalili ka rokeni da kada na tmbyeka da duk ba'a kawo Wannan lkcn ba Amma yanzun lkci be kure ba zan dauki mummunan mataki a kansa dashi da duk Wanda yyi sanadin barinka skul din" Cije lips Dr. Omar yyi Abba ya kamo hannun sa yace, "ka zauna tun kafin na Rasa bakin dazan sanar muku" Nan dukansu suka bishi da kallo a mugun firgice, take gun yyi tsit Ana son Jin tabakin sa, Abba yyi gyaran murya kafin yaci gaba da fadin, "bansan ya zaku dauki lamarin ba Amma dai duk Abinda kukaji nace tofah tabbas gskyne" har yanzu shi suke kallo, shima Dagowa yyi ya dubesu daya bayan daya kafin ya dire kallon sa Kan daddy yace, "Alhaji ko ka tuna da 'yar aikin ku Saratu?" "Saratu..?" Mummy ta fadi hakan da mugun mmki, "Anty Sara..?" Safna ta furta hakan itama da mmki, shima Dr. Omar da mmki yace, "Ummah..?" daddy yace, "Eh wani Abu ne ya faru?" Abba yace, "ehto Amma dai idan zan iya tunawa ta Dade a gidan Nan tana aiki sama da shekara talatin" "confirm" daddy ya furta hakan, sauke ajiyar zuciya yyi zuciyar sa na tarabbabin yadda zai sanar dasu Wannan kulli kafin can yyi ta maza yace, "a zahirin gsky matatace saidai Kai tsaye zan iya kiranta da muguwa marar tsoron Allah" Dr. Omar ne yace, "Abba Ummah kke mgn akai?" Kallon sa Abba yyi yace, "kwarai kuwa, domin ita din Azzaluma ce me raba iyaye da yaransu, Kai idan akwai Wanda yafi cutuwa a Wannan Rashin tausayin nata ma ya biyo bayanka" wara ido sosai Dr. Omar yyi yanzu Kam ya fara tunanin kodai Abba ya kunce ne? Abba kuwa yaci gaba da fadin, "Kuna tare da itane batare da kunsan kullun data Dade tana muku ba domin tun farkon zamanku da ita take muku zagon kasa" daddy ne yace, "bawan Allah tun dazu kke Mana mgn me Kama da surkulle kasa kanmu ya daure me kke nufi da duk Abubuwan da kace?" Abba yace, "a takaice dai Wannan yaron da kke gani" ya dafa Dr. Omar yace, "shine jininka Ina nufin shine Dan da matarka ta Haifa shi kuwa wancan.." ya nuna Sageer daya dago kansa a firgice yace, "shine danta data Haifa lkci guda tayi Wannan canjin tun suna jarirai" Qalu innalillahi wa'inna ilaihin raji'un gaba1 parlon ya dauka da salati kowa ya rude ya firgice, kafin wani yyi mgn sukaji an kwada sallama hade da shigowa parlon Hajjaju ce ta shigo tana fadin, "naje bangaren ku duk bakwa Nan me ake tattauna anan...??" Bakinta ne ya makale lkcn datayi Arba da fuskar Dr. Omar, karasowa tayi da sauri tana nufar inda yake bakinta na fadin, "yau Naga ikon Allah Kai baban Safna kaga me kamar ka kuwa? billahil Azeem kamar an tsaga Kara kodai idona ne?" Ta Ida mgnr tana shafa fuskar Dr. Omar da gaba1 ya zama kamar gunki sbd fadawa tashin hankali, a firgice daddy ya dubeta Yanason ganin Abinda take nuna Masa, tabbas sai yanzu yake hango tsagwaron kamarsa da Dr. Omar yyinda a fusge yake Kama da Hajia Aisha "Hasbunallahi wani'imal wakil...." daddy ya samu bakinsa da Furta hakan a kidime, Mummy kuwa wani irin kuka ne ya kwace mata take ta fashe dashi jikinta na rawa, sai a lkcn Hajjaju ta dubi yanayin su Tace, "Wai meke faruwa Anan?" Abba ne ya samu kwarin gwiwar sanar da ita Abinda ake tattaunawa akai, da mmki suka ga Hajjaju tayi sujjadar godiya ga Allah kafin ta dago bakinta a washe tace, "billahillazi mgnr bawan Allah Nan gsky ce, ni dama tun tuni nake jin zuciya tana kokwantan Anya ja'irin Sageer dinnan jinin mu ne?" Tashi Dr. Omar yyi domin ya kasa gaskatawa da hakan sbd rudani yyi nufin ficewa daga parlon daddy yyi saurin riko shi yace, "ai tunda kazo Nan Babu inda zakaje kazo gidanku" yyi mgnr Yana bin Dr. Omar da kallo sosai yadda yake Abubuwan sa ne suka fara dawo Masa musamman a company idan yyi wani abun sai yaji tamkar jininsa ne sbd ra'ayinsu da izzar su da Kuma Rashin tsoron su dake zuwa kusan daya domin shi Dr. Omar harya take daddy a wa'annan halayen dayake shi yanzu yake cin duniyar tasa daddy Kuma an kwana biyu, Mummy ma mikewa tayi da sauri ta kamo dayan hannun sa hawaye na zuba a kumatun ta sosai bakinta na rawa tace, "laifina ne Ameer" da sauri Dr. Omar ya juyo Yana kallonta da mmkin sunan da yaji ta kirashi dashi, Mummy kuwa ta sakaye sunan ne sbd sunan mahaifin daddy gareshi wato uban mijinta, girgiza Kai tayi tana ci gaba da fadin, "sakacina ne dayasa na aminta da matar da ban santa ba harna jawota jikina da tun farko naji mgnr Hajjaju duk hakan bazai faru ba Dan Allah kar ka tafi" rintse ido Dr. Omar yyi kafin ya juyo garesu gaba1 take kuwa yaji zuciyar sa ta kamu da tsananin son mahaifan nasa na gsky, yanajin feelings irin na Iyaye da Dansu, Safna ce ta rungume shi ta baya hawaye duk ya wanke Fuskar ta Tace, "Dan Allah ya Ameer karka tafi Wlh muna son ka" itama ta sake kiransa da sunan daya Kara Jan hankalin sa, besan meyasa yaji tashin farko lakabin *Ameer* ya shiga zuciyar sa sosai Haka ba, Hajjaju ma matse kwallar ta take tace, "Amma Wannan mata kin cucemu Saratu Allah ya Isa tsakaninmu dake" Daddy yace, "dole ne Ayau dinnan a kamo ta domin ta fuskanci hukuncin daya dace da ita" Cije lips dinsa Dr. Omar yyi yana tuno irin zaman da yyi da Saratu Ashe duk lkcn dayake tunanin kodai
Chapter 94 · 0% Book details