← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 128

Sashe 25

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sosai Anty shafa taji jiki sbd duk Wannan karfin a kanta Sageer ya juye, haka dai komai ya kammala tana fama da ciwon kwankwaso. Suna tsakiyar parlon Sageer yaji an kirashi, kamar bazai daga bama Saida aka Kira kusan sau biyar sannan ya cira a tunzure yace,

"Wai uban waye yake mgn?"

Daga dayan bangaren akace,

"kayi hakuri yallabai Nazo gidanku ban same ka ba Ana tuhumar ka da wani lefi ne shiyasa mukeso muje dakai Dan Amsa tambayoyi"

"Mtwss"

Sageer Yaja tsaki yace,

"sai zuwa gobe zanzo"

Daga dayan bangaren Dan sanda yace,

"shikenan"

ya fada jikinsa na rawa kamar Sageer din na gaban sa, gaba1 'yan sandan tsoron mgn suke Masa yanzun ma dalilin tijarar da Dr. Omar ya musu ne yasa sukace zasu sako shi a gaba.

Kallon su Sageer yyi Ransa na zafi har yanzu beji kwadayin sa ya koma ba musamman daya hango kayan alatun Ameera da sukayi Masa ta leko ta koma, yace,

"Yarinyar a gidanku take Koh?"

Anty shafa ta girgiza Kai cikin yauki tana shafa Masa kirji duk murna ta isheta, Turar da hannun nata yyi Yana mikewa tsaye da sauri yace,

"muje ku kaini inda take"

da sauri su Anty Jamila Suma suka Mike tare da yaran sa gaba1 suka shige mota, Faisal yace,

"oga me zamuyi Mata yanzu?"

Sageer yace,

"so nake na nunawa Wancan Marar mutuncin iyakar sa, Wai Dan tsabar wulakanci ni zai Kai Kara?"

Faisal yasa dariya yace,

"Da alama ya manta waye Kai ne"

Sageer Yaja tsaki da karfi yace,

"bar Dan kut*r uba saina nuna Masa hauka zai gane shayi ruwa ne"

Anty shafa ta tsoma baki da fadin,

"Karkaji komai muna bayanka a Koda yaushe"

su Anty Jamila suka hada baki wajen furta,

"kwarai kuwa"

daidai lkcn suka iso kofar gidan nasu.

Anty Jamila ce ta fita Dan Kiran Meera kamar yadda aka Bata umarni, Meera na daki taji shigowar Anty Jamila, Ba zato taji kawai ta jawo ta saura kadan ta bige da kofa tayi azamar rikewa, a kidime tace,

"Ina zamuje ne Wai?"

Anty Jamila tace,

"gidan ubanki zamu shegiya me bakar zuciya"

ta karasa mgnr daidai lkcn suna fitowa parlo, Meera ta kwace hannun ta da karfi tace,

"Babu inda zani"

Anty Jamila tace,

"idan baki wuce munje ba saikin gwammaci kida d karatu"

tayi mgnr cikin daka Mata tsawa, a mugun tsorace Meera tabi bayan Anty Jamilan, suna fita gate ta hango motoci daga nesa dasu, gabanta ne ya Fadi, kafin su karasa har Sageer ya fito waje, Tsumu2 tayi gabansu kanta a kasa ta kasa furta komai jikinta sai rawa yake, A tsawace Sageer yace,

"Ameera Koh?"

Ameera ta girgiza kanta har yanzu Bata dago ba, Sageer yace,

"Toh ki bude kunnen ki da kyau bansan meye hadinki da wancan Dan iskan ba Amma Naga Yana Shiga sabgar da Bata shafeshi ba, Nasan kinsan za'ayi zaman kotu Toh Wannan ba matsala ta bace Dan kuwa ba Wannan ne farkon mu ba, zabi Zan baki cikin biyu kidau daya, Wanda dai yyi Miki wanna matsalar ki ce"

Sageer ya tako inda take Meera ta matsa baya, Sageer yace,

"Idan aka tsaya a kotu aka tmbyeki gskyr waye yake Shirin Yi Miki fyade? Amsar da Zaki bayar kice *OMAR* ne"

a razane Ameera ta dago kanta tana binshi da wani matsiyacin kallo, Wara hannun sa Sageer yyi Alamar ko a jikinsa yaci gaba da fadin,

"ko ki maida karar Nan ta koma kansa ko Kuma nasa a kashe shi Kuma na Dora Alhakin kisan a kanki"

yanzu kam kallon tsoro Meera ta bishi dashi, Sageer ya Girgiza Kai yace,

"tabbas Wannan shine zabin da zakiyi ko kiyi ko kiji Abinda zai biyo baya zabi ya rage game Shiga rijiya yyi mgnr Yana me juyawa baya Dan shigewa mota,

yyinda ita Kuma aka barta a tsaye tamkar gunki.

•••�
Barinsu wajen keda wuya Faisal yace,

"Oga yanzu meye amfanin saika nemi taimakon ta Dan ta rufa maka Asiri Bayan kanada yadda zakayi ka Kori karar?"

Wani munafukin murmushi Sageer yyi Yana shafa wani Dan iskan Aski kansa da aka gegere gefe yace,

"Da nayi niyya tun Ina zaune a gida zancen karar zata Sha ruwa, Toh Amma wannan itace damata ta farko dazan wulakanta Omar a bainar jama'a dole zancen fyade ya juye ya koma kansa tare da hadin bakin ku, So nake Naga Ina karshen ji da kansa zai tafi? Naga Ina isarsa da mallakar sa zai tafi? So nake Naga disappointed face dinsa idan ya fahimci wacce yake neman taimakawa ta goyi bayana wajen maida karar kansa."

"Dakyau mutumina"

Faisal ya furta Yana tafi kafin yace,

"Amma kana ganin zata yadda a maida martanin kansa?"

Sageer ya kalli Faisal kafin ya kalli su Anty shafa da sukayi suman zaune suna Jin Wanda ya shafe su a iya tuggu yace,

"tare da goyon bayanku nakeson komai ya tafi daidai dole a tsoratar da ita yadda zata amince"

Gaba dayansu girgiza Kai sukayi Alamar zasu bashi goyon baya.
8/15/20, 8:02 PM - Ummi Tandama: *ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA....🐓*
( _ko Ana Muzuru Ana Shaho Sai yayi_)

Na
*Nuceeyluv😘*

*Wannan page din kyauta ne sukutum ga masoyan Wannan buk din gsky Naga ruwan comments harna rasa Wanda zanyi reply akai, Ashe haka DR. OMAR DA HAFSAT(AMEERA) suke da masoya? Kai Masha Allah suna godiya ga masu kaunar su🤪.*

16....

Tunda suka barta a wajen tayi tsaye tamkar gunki Kai kace Bata numfashi sbd Shiga tsananin firgici da tashin hankali, kadan ya rage wani me mota ya bigeta a layin nasu sbd mutuwar tsayen da tayi batajin karar komai, Saida yyi Mata horn me karfi kafin ta dawo hayyacin ta, a tsorace ta matsa gefe tana sauke ajiyar zuciya, cikin hanzari ta nufi gate dinsu kirjinta na dukan uku2, Shigar ta gida keda wuya tayi zaune Nan parlon su tare da rike kanta cikin wani yanayi na tashin hankali, ba'a Dade ba kuwa sai gasu Anty shafa sun shigo gidan sbd suna son sake firgitar da ita, Tana ganinsu ta Mike tsaye cikin takaici da bacin Rai tace,

"yanzu duk Abinda kuka min be isheku ba har saikun sa wani a ciki?"

Anty shafa da Anty Jamila suka bita da kallo tare da rungume hannayen su a kirji, hakan yasa Meera cikin yanayi na me Shirin kuka tace,

"Kunso cutar Dani Allah ya tsare ni a dalilin Wannan bawan Allah sbd hakar ku Bata cimma ruwa ba shiyasa kukeson Bata Masa rayuwa? Toh Wlh ku sani indai nice bazan taba bada shaidar karya a kansa ba saidai ku karata da barazanar ku ku Bari"

Wata irin shedaniyar dariya taga sun fashe da ita suna tafawa hade da nunata,

"like seriously?"

Anty shafa ta furta tana dariyar keta kafin taci gaba da fadin,

"Kina Wasa da Abinda Sageer yace Koh? Ah lalle da alama kinason Kare Rayuwar ki a prison Dan matukar Kika ki bada shaidar Dr. Omar saidai wani bashi ba"

Anty Jamila tace,

"ni dariya ma ta bani Wai itace me ja damu? Haa lalle yarinya kina Wasa da Rayuwar ku duka"

ta fada tana kallon Ameera, Takaici ne ya Kama Ameera kawai ta wuce dakinsu tana share hawaye gaba daya hankalin ta ya kasa kwanciya, Tafiyar ta keda wuya Anty shafa ta Danna Kiran Sageer Yana dagawa da sauri tace,

"da alama fa bazata yadda da Abinda kace ba Dan gashi ma har tana maida Mana mgn"

Wani wawan tsaki yaja kafin yace, su saurari zuwan shi Nan suka yanke wayar, ba'a fi mintuna 30 ba saiga kiransa ya shigo unguwar shi da mutanen sa na dazu, da karfi da yaji Anty shafa da Anty Jamila suka fitar da Meera daga gidan har izuwa bakin motar su, dake unguwar irin me shirun Nan ce sai a yanka mutum ma ba'asan anyi ba me gadin su kuwa tsoron yaran gidan yake sbd kar a koreshi shiyasa yake lallaba aikinsa, Mom kuwa Bata dawo gidan ba haka zalika Dad baya gari,

Zuwansu bakin motar keda wuya Su Sageer suka fito, Dagowa Kai Meera tayi tana binsa da mugun kallo tace,

"Azzalumi bazan bada shaidar karya Akan mutumin dake son kwatar min 'yanci ba"

Sageer ya Busa hayakin Sigari Yana Mata Wani kallo kasa2 irin na tataccun 'yan iska kafin ya bushe da dariya yace,

"Gskyne Har ya fara koya Miki Jan wuya irin nasa?"

Banko Masa Harara tayi batace komai ba, Sageer ya kalli gefen sa wani yaron sane a wajen yyi Masa Alama da ido Nan yaron yazo gaban Meera sai ji tayi an wanke ta da Mari, a gigice ta dafe kumatun ta tana kallon Sageer, daidai lkcn taga yyi Mata nuni da wata bindiga, zaro ido Meera tayi kirjinta na bugawa, Sageer yadan kada Bindigar Yana dosar inda take kafin ya Dora Mata akan goshi cikin Tsawa yace,

"kin taba ganin inda ake harbi daga nesa?"

Jiki na rawa Meera ta girgiza Kai, Murmushin mugunta yyi Mata yace,

"So Zaki fara gani Akan Dr. Omar matukar baki bada wannan shaidar ba"

Hankalin Meera idan yyi dubu to ya Kuma tashi tabbas taga tsantsar Rashin Imani da tausayi a idon Sageer hakikanin gsky zai iya duk Abinda ya furta a yadda ta fahimta zai aiwatar, Sageer ne ya katse Mata tunani da fadin,

"wannan shine warning Dina na karshe dazan Yi Miki kindai ga Bindigar a hannu na Koh?"

Meera ta kasa motsi, Sageer yaci gaba da fadin,

"har Kotu zanje da Bindigar kina bada shaida a Kaina ba akansa ba da an fito saidai uwarsa ta haifi wani bashi ba Wannan Alqawari na ne, sanna da an rufeki a prison baki tsira daga gareni ba zansa kowanne lkci Ana bani ke Dan kashe kwadayina a kanki a haka Zan more jikin kina prison har na Gama cin moriyar jiki na saki a bola"

Yana Gama fadin haka yyima sauran yaran nasa Alama da su tafi, Nan suka shige mota aka bar su Anty shafa da Meera a wajen, Bayan sun wuce Suma Barinta sukai a wajen sukayi tafiyar su batare da sun kulata ba sai dariyar su suke ta mugunta.
Chapter 25 · 0% Book details