Sashe 115
Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yace, "Mama muje can dayan parlon ayi mgnr a nutse" Nan suka Diba zuwa dayan parlon gidan, Shidai Sadeeq mmkin furucin Dad kawai yake a Haka suka Isa Bayan sun zauna ne dad yace, "Kamar yadda na fada Miki ne tun farko mama Abubuwan daya faru da Ameera tun tana Karama bayin Kaina bane lkcn da kikaje gidana na karshe banji dadin yadda muka rabu ba tun a lkcn naso zuwa baki hakuri har nake sanar da sadiya(Mom) ta nuna min a fuska ta bani goyon baya Amma Wlh bansan ya akai na manta d mgnr ba kwata2 har mancewa nake da Ameera Tanada Dangin mahaifiya...." Nan ya fara Basu lbrn kuncin Rayuwar da Meera ta taso da yadda yyi ta nuna halin ko in kula Kan Meera da fada musu asalin su waye Shafa'atu da Jamila ya dauki kauna d son duniya ya Dora musu kamar shi ya haife su ba Abinda suka nema suka Rasa daga wajen sa sai bayan bikin yaran hankalin sa ya dawo jikinsa, soyayyar Ameera ta dawo Masa, ya fahimci zaman cin Amana mom take dashi, daga karshe yace, "a ranar da abin ya kasance shine cikin bcci na nake mafarkin Aminatu tazo min tana tunatar Dani hakkin Ameera da akaci, sai Kuma fuskar Ameera Dana gani tana kuka sosai ba karamin girgiza nayi d Wannan mafarkin ba da Allah yaso Asirin zai karye Ina farkawa da salati a bakina Abinda ya biyo baya shine Ameera Dama a kwanakin Inajin canji a jikina shiyasa komai sadiya tamin nakejin haushin ta, Koda na fito a dakina ba Abinda nake Fadi sai Kiran sunan Ameera, Sadiya na fitowa a kitchen Jin na ambaci Ameera ta saki plate din dake hannun ta cikin firgici, na matso kusa da ita Ina fadin Ina kuka kaimin Ameera...? A takaice dai duk yadda naso ta bani Amsa kasawa tayi sai cemin take Bata sani ba. A zahirin gsky naji takaici kwarai a lkcn tunanin yadda Ameera tabar gidan ya dawo min, ba Bata lkci na rabu da Wannan annobar Sadiya nasa tabar min gidana ko kwana daya Bata Kara ba dukda taso na barta na rufe idona, tun daga Wannan lkcn na bazama neman Ameera Ina takaicin kalar auren da nayi mata ba bincike ba sanin inda take zaune, Toh da Allah ya taimake ni Ina fitowa ranar da safe muka hadu da ita bakin gate." Abban Ahmad da shi kansa Ahmad daya shigo parlon da Sadeeq ba Wanda be tausayawa Ameera ba, lalle Ameera taga rayuwa Sadeeq Kuma tunani ne ya shige shi kenan idan bazai manta bafa Wannan shafar itace ta auri Sageer? Tab lalle anyi gwarama ya Fadi hakan a ransa, Inna fure na goge hawayen takaici da tausayin Meera Tace, "Insha Allahu sai Allah ya saka wa yarinyar Nan, ace tun tana Karama ake cutar ta? Kai Allah ya Isa Wlh sai sun gani a kwaryar su matsiyata" Sadeeq yace, "ai Inna fure kusan Lbrn Ameera yaso yyi Kama Dana Omar" Nan suka zuba Masa ido da mmki, gyada Kai yyi Yana gyara Zama Nan ya fada musu sauyin da akayiwa Omar lalle sun firgita dajin Wannan lbri Inna fure jikinta har rawa yake sbd firgita cewa take, "duniya Ina Zaki damu? Yanzu wa gari ya waya? Kaii Hasbunallahi wani'imal wakil...." Abban Ahmad kuwa Fadi yake, "Allahu Akbar Lalle inda ranka kasha kallo Abu sai kace a film? Koda yake ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA....." Dad kuwa tsabar tausayin Omar din ma kasa Furta komai yyi Ashe na Meera Nafila ne tunda tasan iyayenta shi kuwa dungurungun aka dauke shi daga wajen su tun besan kansa ba kaii duniya akwai macuta dayawa, duk Wanda ka jawo shi inuwa daga rana sai kaga wata Rana shike kokarin turaka ranar, shi kansa Ahmad ba karamin tausayi suka bashi dukansu ba hakan yasa a ransa lalle sun cancanci su mallaki junansu domin sun dace da juna kowa yaga rayuwa. Matsawa Meera tayi baya tana kada kanta Tace, "no ya Omar duka yaushe nazo garin? Ko sati fa banyi ba Kuma rabona da garin Nan tun Ina Karama" matsawa yyi dab da ita zai kamota ta zame tanayin hanyar kofa hakan ya sashi binta da sauri Dan yaga kamar zata gudu Aiko kafin ya karaso harta fece, dafe kansa yyi Yana takowa a hankali zuwa wajen daidai lkcn Sadeeq ya fito waje Yana Amsa Kira ya hango Omar din ya fito ita Kuma Meera tabi wata hanyar, Dan murmushi yyi Yana matsawo gun Omar din wayarsa a kunne zuwan sa wajen yyi daidai da Gama wayar tashi ya dubi Omar daya zube hannayen sa cikin Aljihun wando sa Yana bin hanyar da Meera tabi da kallo, ganin kamar baida niyar kulashi yasa shi Shan gabansa Yana tare inda yake kallon, dubansa Omar yyi Yana Dan yatsina fuska yace, "mlm lpy kke keta tsakanin mata da miji?" Gwalalo ido Sadeeq din yyi yace, "Amma Wlh Omar ka dinga Jin tsoron Allah" Omar na Dan hararar sa yace, "toh da Kai zanji tsoro? Haka kawai ka katse ni" "kuttt Amma Kai Dan iskane Wlh kaga ni duk ka maido da nutsuwar ka Nan muyi mgn" sai a lkcn Omar ya danyi murmushi yace, "Inajin ka" Sadeeq yace, "Kun daidaita ne?" Omar yace, "Eh Insha Allah" "Kai Alhamdulillah gsky naji Dadi" kallon sa Omar yyi yace, "tun dazu tare kke dasu ne?" Sadeeq yace, "hmmm kaidai Bari kawai frnd" Omar yace, "meya faru?" Sadeeq na sake sauke ajiyar zuciya yace, "Rayuwar Nan gaba dayanta cike take da Abubuwan tsoro" yanzu Kam da mmki yace, "wani Abu ne ya faru?" Dubansa Sadeeq yyi kafin yace, "ai ya Dade da faruwa ma saidai Allah ya kiyaye gaba yasa iyakar wahalar Taku kenan" Omar Adan tsorace yace, "kamin bayani yadda zan fahimta mana" Sadeeq ya Buda baki zayyi mgn kenan yaga fitowar su dad harda Ahmad dake bayansu hakan yasa ya hadiye Abinda yaso Fadi dukansu suka Isa garesu, Abban Ahmad ne yace, "toh Omar mu zamu fita saiku Kai kayanku can part din Ahmad ku zauna, gyada Kai yyi da murmushi yace, "Mun gode Allah ya saka da Alkhairi" "ba komai Omar mune da godiya" Nan sukayi masu sallama suka tafi, bayan tafiyar su ne Ahmad yace, "muje na nuna muku wajen" Amsa Masa sukai da Toh daidai zasu wuce inda Meera tabi Omar ya juya wajen yanata kallo kamar Wanda zai hango ta, kayansu suka kwashe Nan suka wuce dashi part din Ahmad da yanzu ya ware Yana musu Hira. Inna fure na saka hijab tace, "tafiya zamuyi can gidana" Asma'u dake rokon Inna fure Tace, "haba Inna duka fa kwana daya tayi Amma Zaki kwashe ta ku tafi" Inna fure Tace, "ke idan kinaso ki biyomu Amma nikam munyi gaba, maza karasa Shirin ki Ameera mu tafi" Ameera dake Sanya cikin Shirin nata tace, "Toh." Mami na parlo sai ganin fitowar su daga daki tayi tana dubansu da mmki wajen karfe 8pm kenan tace, "mama wani wajen zaku da Daren Nan?" Inna fure Tace, "gida zamu tafi" mami Tace, "Amma fa dare yyi da kin Bari sai gobe" Inna fure tace, "nayi harama nikam ke Asma'u Kira min Ahmad yazo ya kaimu" Asma'u badan taso ba Tace, "Toh" itadai Meera na gefe tana jinsu, wayarta Asma'u ta dauko kafin ta Danna Kiran Ahmad, yana tsakiyar su Omar anata Shan lbrin kwallo kowa na wasa gwaninsa Kiran Asma'un ya shigo, dagawa yyi Yana fadin, "yane?" Asma'u Ta sanar dashi sakon Inna fure, kallon Omar yyi sai Kuma yace, "toh Ina zuwa" ya karasa mgnr Yana kashe wayar, duban Omar ya sake Yi yace, "zankai su Inna gida" "harda Meera?" Omar ya Furta hakan da sauri, Dan murmushi Ahmad yyi yace, "shiyasa ma na fada maka nasan baka sani ba" dafe goshin sa Omar yyi shida yakeso zuwa Anjima yasa a Kira Masa meeran suyi mgn sai Kuma a dauke ta? Sadeeq ne yace, "Wannan Abu Dan sauki tunda kanason ku hadu a Daren Nan Kai saika karbi tukin" sai a lkcn Omar ya dago yace, "dake nasan gidan Koh?" Ahmad yace, "Wannan ba matsala bane Bari na fita da dayar motar gidan can bakin Hanya Kai Kuma saika zauna a mota na a Matsayin ni nasan Inna tana Shiga gida zata fita a motar tayi gaba a lkcn sai ku zanta kafin ta ankare" Dadi Omar yaji sosai Dan Haka yace, "Thank you" Ahmad na tashi yace, "haba ai Ana tare" Nan ya dauki key din motar sa ya bawa Omar kafin yyi hanyar waje yace ma Sadeeq, "idan na fita saika fito muje tare kaima" Sadeeq ya gyada kai, bayan fitar Ahmad ne Sadeeq ya dubi Omar yace, "Dan Allah karka bamu kunya garin zantawa a samu mishkila" hararar sa Omar yyi yace, "dake kowa irinka ne Dan iska" 'yar dariya Sadeeq yyi yace, "No tunatarwa ce" Saida Ahmad ya fitar da motar bakin layi kafin yyiwa Sadeeq waya dake sunyi exchanging numbers, mikewa yyi ya fita, shi Kuma Omar yasa kananun kaya da facing cap ya shige motar Ahmad, daidai lkcn ma kuwa su Inna suka fito Meera na tafe a sanyaye, Shiga Bayan taso Yi Inna fure Tace, "jeki gaban Nan kafata nakeso na Mike tsami take min" Meera Tace, "toh" Nan ta koma gaban motar zaton ta dai Ahmad ne, tana shiga kuwa ta juyar da kanta gefe tana kallon window hakan da tayi kuwa ba karamin birge Omar din tayi ba Ashe dai meeran tasa first class ce, a hankali ya fara driving harya Kai ga bakin layin nasu daga can nesa ya hango motar su Ahmad, hakan yasa ya fara binsu a hankali, Inna fure Tace, "oh Amadu wani lkcn kanada kirki yau tukin naka da alama irin na kwararru ne Babu jijjiga bare barin hanji" shiru motar tayi Omar be iya cewa komai ba saima dariya data bashi yyita a ciki, tabe baki tayi tace, "wani lkcn miskilancin ka ya tashi tsiyace dakai ai sai kayita Yi Mtwss" taja tsaki tana me Dan kishingida, juyawa baya Meera tayi Dan taji ba Dadi Akan shareta da yyi ta sake Juyowa da nufin kallon sa Daidai lkcn shima ya Dan jiyo da fuskar sa a hankali, a firgice Meera taso Wara baki tayi saurin rufewa da hannun