← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 128

Sashe 105

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*200 Zaki turo ta Wannan account din 0030202448 Nusaiba Mustapha Sterling Bank saiki turo da shaidar biya ta Wannan Number 09039118754* 8/18/20, 10:21 AM - Ummi Tandama: Ganin yawan kallon da Ahmad yake mata ne yasa ta dafe kanta Alamar kamar Yana Mata ciwo, Inna fure ce Tace, "kin gaji Koh?" Ameera ta gyada kanta tana Dan cije lips dinta, Inna fure Tace, "gashi har yanzu Mahaifan naki Basu dawo ba nasan baban Ahmad da zance yanzu Haka Hira suka tsaya Yi wani wajen" Dan murmushi Meera tayi Tace, "ba komai Bari na jira su" Inna fure Tace, "haba 'yar Nan tashi na rakaki makwancin ki" mikewa Ahmad yyi da sauri Yana fadin, "ai Inna basai kin wahalar da kanki ba Bari Asma'u ta dauko mata hijab saimu wuce Koh?" "Ikon Allah" Inna ta furta hakan tana Kama haba, kafin taci gaba da fadin, "jikata fa anan zata kwana na fada maka hakan tun dazu" Kallon Inna yyi cikin sigar roko yace, "Dan Allah ki Bari muje tare Mana kinaga fah har yanzu ta kasa sakewa damu saikace ba 'yar uwa ba" Inna tace, "Toh ai daga zuwanta bazaka ga hakan ba ka Bari goben Nan Insha Allahu can wajenku zata yini" Asma'u ce tayi saurin tsoma baki da fadin, "hakane Inna da gani Wlh duk ta gaji" itadai Meera kanta ne a kasa tana sauraron ikon Allah, Kwafa Ahmad yyi badan ya so ba murya can ciki yace, "Shikenan" ya Fadi hakan Yana matsawa gefe hade da rungume hannayen sa, sai a lkcn Meera ta dubeshi dukda Yana fushi be hanashi sakar mata murmushi ba, Dan yake tayi Masa a hankali Tace, "Goodnight" "Night" shima ya Furta hakan a hankali, tare da Asma'u suka wuce dakin Inna fure Kan lallausan gadon ta tazauna Asma'u ta dubeta da murmushi tace, "yayana ya cika takura Koh?" Meera ta girgiza Kai da murmushi tace, "meye abun takura Kuma?" Asma'u Tace, "yanada son mutane sosai especially Dangin sa kinsan ba anan ya taso tare damu ba shiyasa Sam be San da lbrn ki ba dayake kinsan yadda Abubuwan suka faru a baya nimadai Ina Karama nakejin lbrn naki daga baya Kuma yyi kasa" kwalla ce ta cikowa Meera sbd tuno muguntar da mom tayi mata a hankali tasa gefen gyalenta ta goge wadda ta gangaro Tace, "rayuwa kenan" Cikin Rashin fahimta Asma'u Tace, "Kamar ya kenan?" Girgiza Kai Meera tayi tana murmushi Tace, "No ba komai Bari na kwanta I need rest" "Okay Saida safe" Asma'u ta Furta hakan tana tashi tsaye, "Allah ya nuna Mana d Alkhairi" Meera ta Bata Amsa itama, ja mata kofa Asma'u tayi yyinda Meera ta sake shigewa cikin gadon ta kwanta lumshe idonta tayi, tayi lamo kamar me bcci, Rayuwar ta na baya take tunawa daga lkcn da aka rabata da dad dinta har lkcn da kaddara ta hadata da Omar, gabanta ne ya Fadi da sunan sa ya Fado a cikin tunanin ta, ba komai ke daga mata hankali ba sai aurensa dake kanta, ya kamata ace ta karbi takardar ta ne, Toh Amma tataya? Mutumin da besan inda ta tafi ba? Da irin wa'annan tunanin bcci barawo ya saceta. Dake Alhji Abdullahi ya kawata gidansa da gine2 da Kuma bangarori d dama Saiya kasance inda aka sauki Omar Kamar wani bangare ne daban dake cikin bangarorin gidan, Safna tana gaba Suna binta a baya harta kaisu part din da aka budewa Dr. Omar Bayan ta bude parlon ne ta juyo tana kallon Omar dake ta Bata Rai Tace, "Ya Ameer" kallon ta yyi yace, "yes sister" Dan murmushi Safna tayi Tace, "ga inda zaku Shiga Nan ni zan koma" ta Kare mgnr tana kallon Sadeeq dake kallon ta, dage Masa gira tayi Tace, "Ya Sadeeq?" Murmushi yyi yace, "godiya muke kanwarmu" Dan murmushi tayi Tace, "wlcm" tana Gama fadin Haka ta juya itama. Shiga parlon sukayi Dr. Omar na zuwa inda aka kawata da kujeru suke yyi jifa da jakar wajen sa, Juyowa Sadeeq yyi da sauri Dan ya tsaya kallon yadda aka kawata parlon ne yaji Omar Yana Fadin, "seriously da an Barni a Daren yau dinnan zan nufi Adamawa Kamar Nan da wudil ni nake kallon ta" ya Fadi hakan kamar ya kurma ihu Dan haushi gaba1 an katse Masa hanzarin sa, sauke tasa jakar Sadeeq yyi kafin ya taka har gaban kujerar dake facing Omar ya zauna Yana Dora daya Kan daya hade da sa tagumi Kamar yaga sabon halitta, Hannayen Omar na cikin lallausan gashin sa Yana hargitsa su Fadi yake, "da ace inada fiffike tabbas Dana tashi sama yanzun Nan" dariya me sauti Sadeeq ya fashe da ita har Yana rike ciki, cikin mmki Omar ya bishi da kallo yace, "are you okay Sadeeq?" Sadeeq na ci gaba da dariyar tasa yatsan hannun sa na pointing Omar yace, "seriously Kai ka dace da Wannan tmbyr" nuna kansa Omar yyi yace, "why me?" Sadeeq na Dan daidaita nutsuwar sa yace, "sbd tsabar gigicewa Akan Meera Fadi kke dama kanada fiffike? Wai Omar me yarinyar Nan ta maka ne duk kabi ka Susuce lkci guda?" Cije lips dinsa Omar yyi Dan ya fahimci Sadeeq Iskanci yakeson Masa Dan hararar sa yyi yace, "u never understand" "Oh! Really?" Sadeeq ya Furta hakan Yana 'yar dariya, shiru Omar ya Masa bece komai ba, Sadeeq yaci gaba da fadin, "Koda yake let me ask you 1 question, Wai a jiyan Nan da Salma ka angwance ne ko kuwa innocent Meera aka farma?" Kallon sa omar yyi a razane hakan yasa Sadeeq ya sake fashewa da wata muguwar dariya, hade Rai yyi cikin son basarwa d borin kunya Omar yace, "Kamar ya na far mata saikace yaki??" Sadeeq yace, "toh Kai a yadda kke tsohon tuzurun Nan ka samu yadda kkeso ai saita Allah..." "Banason iskancin fa Sadeeq idan tazurancin ne ma Kai yanzu me kke? Ai gwara dai ni" Sadeeq yace, "daka samu lpy jiya ba? Bayan Haka ai ni da Kai duk kanwar ja ce..." Kokarin Kai Masa dukan abokai yyi Sadeeq ya goce Yana barin wajen sai dariya yake Daidai lkcn kuwa aka Kiran magrib, Sauke ajiyar zuciya Omar yyi kila idan sunje Sallah Sadeeq ya sarara Masa Haka Nan. Koda sukazo bcci ma Sadeeq yaki sararawa Omar sai tsokanar shi Yake, gaba1 yabi ya takura Masa hakan yasa Omar yabar Masa dakin ya koma wani Dan Yana bukatar ya samu space, kwanciya yyi ya lumshe Ido take er babe din nashi ta bayyana, tunanin farkon haduwar su yake lkcn data sharara Masa Mari, dafe kumatun sa yyi a maimakon da dayake Jin haushi da Takaici yanzu kuwa shafo kumatun yyi yakaiwa hannun nasa kiss Yana Jin a ransa kamar hannun data mareshi yyi kissing, cije lips dinsa yyi sosai lkcn daya Kara tuna haduwar su ta biyu a ruwa, gsky baya manta lkcn domin ya wahala a Wannan Rana to Wai meyasa ma tun wuri be tsaida hankali akan Meera ba? Koda basuyi aure ba tsautsayi da neman taimakon ta suka zube cikin ruwa Suna gangarawa a kasa kowa a bisa kirjin kowa ya Isa ya Tabbatar Masa da cikakkiyar mace yake tare ba hotiho ba, Amma sbd taurin Rai irin nasa Sam ya mance da Wannan nunannun kayan alatun har Saida aski yazo gaban goshi ya farga, juyi yyi cikin takaicin kansa Yana fatan gari ya waye ya nufi Adamawa. Washe garin ranar kuwa Meera na Gama breakfast dad ya shigo gidan, gaishe shi tayi da murmushin ta, dad yace, "jiya kafin na dawo harkin kwanta" Inna fure ce ta shigo parlon tana fadin, "ai da alama ta gaji jiyan Nan" dad yace, "kwarai kuwa ai zaman ne ba sauki" Inna fure na dariya Tace, "Toh da tafiyar mota tayi fah?" Shima dad dariyar yyi yace, "gsky kuwa da abin sai yafi Haka" itadai Meera murmushi kawai take, can taji dad din nata yace, "Ameera ya Matsayin auren naki yake Dan jiya baki bani wani kwakkwaran Amsa ba" dam... Kirjin Meera ya buga da karfi, Inna fure Tace, "Aurenta akayi?" Dad ya girgiza Kai yace, "a lkcn tunani na an dauke shi akan Meera tana cikin karatun ta baiwar Allah Nan Wlh na aurar da ita auren ma irin na marasa Gata Dan ko shi yaron ce Masa nayi kada yyi mata kaya ko kala daya idan taje ta samu acan" cike da masifa Inna fure Tace, "haba Ibrahim wanne irin aure ne Babu lefe? Gsky banji Dadi ba Wlh ka wulakanta min jinin 'yar Aminatu" shiru dad yyi ganin kamar Inna furen tadau zafi a hankali yace, "kiyi hakuri Inna shiyasa nace a lkcn bana cikin hayyacina an dauke min tunani na akanta" kwafa Inna fure tayi Tace, "ke Ameera da kukayi auren ya Miki lefen?" Meera da hawaye suka fara tarar mata tayi kasa da kanta tana kokarin maida su, "mgn zakimin ba shiru ba" Inna fure ta sake furta hakan, jikin Meera na Bari ta girgiza kanta a hankali, "La'ilaha'ilallahu Muhammadun Rasulul lahi S.A.W" Inna fure taja salati ta dire ranta a mugun bace Tace, "ke kuwa wanne Dan iskan yaron ne ya aureki Wanda besan darajar mace ba?" Kasa Dagowa Meera tayi jikinta kuwa naci gaba da rawa, shi kansa Dad ransa ne ya baci akan Abinda Omar yyi sai yanzu ya tuna tun ranar daurin Aure ma be Kara ganin fuskar sa ba, Inna fure ce tace, "ke gayamin gsky ke kikace kinason sa ya taimaka ya aureki ko kuwa wulakanci ne kurum irin na maza yaga bulus??" Jan zuciya Meera ta farayi sbd kukan da take ta dannewa yaci karfin ta, takaici kuwa ya Kama Inna fure kamar tayi tsuntsuwa ta ganta gaban Dan banzan yaron Nan daya wulakanta mata jika, ganin kamar meeran Bata da niyyar Amsa duk tmbyr da akai Mata ne ta yanke maganganun nata da fadin, "toh daya Gama cin moriyar gangar Dan Bantan uban saki nawa ya Miki?" Fashewa da kuka Meera tayi tana kokarin tashi, hakan yasa suka bita da kallo har cikin ransa dad yakejin kukanta Yana ganin kamar duk Wannan lefin sa ne da be wofintar da itaba a lkcn da tafi bukatar sa tabbas da duk hakan Bata kasance ba, tana mikewa kuwa tayi hanyar daki da saurinta still Bata daina kukan ba, sauke ajiyar zuciya
Chapter 105 · 0% Book details