← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 128

Sashe 109

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"meya faru Ameera?" Shiru Ameera ba mgn sai Jan zuciya, Nan Ahmad ya Fado dakin shima Inna fure Tace, "Kai lpy kuwa kuke ta guje2?" Sauke numfashi Ahmad yyi Yana zama kan kujera yace, "Dan Allah Inna ki tmbyeta Nima bansan Abinda ya faru ba" "Kamar ya baka sani ba bayan tare kuke?" Mamy dake shigowa tayi Wannan furucin, dafe goshinsa yyi kafin yace, "muna Shirin shigowa ciki wani daga bakin gate ya dinga kwala mata Kira Yana Mika mata hannu tazo badan Allah yasa masu gadin Nan sun tare shi b Toh kuwa ba shakka Saiya shigo ciki" "innalillahi wa'inna ilaihin raji'un" inna fure ta furta hakan tana dora hannu akai Tace, "Wanne irin mutum ne Haka daga zuwanta ko Gama sanin garin batayi ba za'ace an biyota?" "Nima Abinda ya bani mmki kenan" Ahmad ya Furta hakan, ita dai Meera Bata dago Tace musu kala ba Dan gaba1 jikinta rawa yake, hakan yasa Inna fure Tace, "jeka Ahmad ka dubo Mana waye mutumin? A yadda ta firgice dinna Ina kyautata zaton ko ba mutum bane" 'yar dariya Ahmad yyi Yana mikewa tsaye yace, "haba mutum ne sak Kamar kowa Bari dai naji wanene" Mamy Tace, "Wannan Abu Koh da mmki yake" Inna fure ta sauke ajiyar zuciya tana shafa Bayan Meera tace, "Allah shi kyauta." A bangaren su Omar kuwa parlon baki Alhji Kabir ya sauke su Bayan sun zauna ne shi Kuma ya fita Dan a kawo musu abin tabi, Yana shiga gidan ya Kira mamy ya sanar da ita ta kaiwa bakinsa abinci Tace, "Toh" Nan tasa masu aiki suka fara kaiwa su Omar kayan motsa baki da abinci, Sauke ajiyar zuciya Sadeeq yyi bayan masu kawo musu abincin sun Gama ya dubi Omar daya cusa hannayen sa cikin lallausan gashin sa Yana hargitsa shi, Dan gyaran murya yyi kafin yace, "da alama abun zaizo Mana da sauki" Omar ya dube shi cikin damuwa yace, "sauki? Kana gani fah kiranta nake tayi banza Dani Sadeeq" ya Kare mgnr kamar yyi kuka Dan takaici, sauke numfashi Sadeeq yyi kafin yace, "komai a sannu ake binsa Insha Allahu zaku daidaita da wuri" Dan cije lips dinsa Omar yyi kafin yace, "Haka nake fata" dubansa Sadeeq din yyi sannan yace, "gashi duk ka hargitsa gashin naka a Haka kkeso ka birge ta?" Shiru Omar yyi kafin yace, "yeah ko a Yaya nake Ina birgeta" "Haka Tace maka?" Sadeeq ya Fadi hakan d mmki, Omar na tabe baki yace, "Haka nake tunani" Sadeeq yace, "Dan Allah Shiga Koda toilet ne ka duba gashinka a madubi idan ba so kke Dan saurayin can yyi maka kafa ba" wata irin muguwar hararar Omar ya sakar Masa Kamar ya doke shi hakan yasa Sadeeq Yaja bakinsa ya tsuke, dakyar dai suka cusa Abinda ya samu a cikin Abubuwan da aka kawo musu, Alhaji Kabir kuwa na can yana tmbyr dad meyasa ya share su dad ya Gaya masa dalilin sa, Shiru Alhaji Kabir yyi shima ransa ya baci Amma dai dole Abi abun a hankali Dan Haka yace, "toh ita yarinyar ta fada maka saki nawa yyi mata?" Girgiza Kai dad yyi yace, "duk lkcn da aka tmbyeta akan hakan saidai ta fashe da kuka shiyasa nake tunanin sakin wulakanci yyi mata" sauke ajiyar zuciya Alhaji Kabir yyi kafin yace, "kuma gashi yaron yace Bai saketa ba" shiru dad yyi beyi mgn ba, hakan yasa Alhji Kabir yaci gaba da fadin, "inaga kamata yyi a Kira Ameeran sai muji daga gareta tunda Yana wajen idan har ya saketan yanzun Nan zansa subarmin gidana, idan be saketa ba sai musan abin yi" cikin gamsuwa da shawarar Alhji Kabir yace, "ya amince";mamy Alhji Kabir ya Kira yasan tunda dad ya sanar Masa yadda sukayi da Inna fure za'a iya samun matsala idan tasan Omar din yazo Dan Haka yasa mamy ta turo Masa Ameera, Ameera data daina jan zuciya yanzu mamy ta shigo da fara'ar ta Tace, "kije Abban su Ahmad na Kiran ki" mikewa Meera tayi Tace, "Toh,?";Inna fure Tace, "Suna gidan ne dama?" Mamy Tace, "a'a yanzu dai suka shigo" shigowar Ahmad ce ta katse musu mgnr yace, "inaga dai sojojin Nan sun kora su Dan Banga kowa ba" Inna fure na murmushi Tace, "Sun kyauta" Meera Kam tsam tayi da ranta tana tunanin Kuma Ina ya tafi? Mamy ce ta katse mata tunanin da fadin, "Suna jiranki fah" tashi tsaye tayi hakan yasa mamy ta kamo hannun ta Dan ta rakata parlon Abban su Ahmad, Ahmad ne yace, "mamy wani wajen zaku ne?" Mamy Tace, "Abbanku ke kiranta" "okay" Ahmad ya Furta hakan Yana zama hade da kwalawa Asma'u Kira, kafin suje parlon Alhji Kabir ya kirata a waya yace ta sameshi a parlon baki, hakan yasa mamy ta canja direction dinta zuwa can, ita dai Meera Kamar jela Haka take binta zuciyar ta nadan harbawa kadan, acan kuwa dad da Alhji Kabir ne a parlon bakin tare dasu Omar Bayan sun sake sabuwar gaisuwa Alhji Kabir na Amsa musu da fara'a be tmbyesu komai ba Dan jira kawai yake meeran tazo, Suna cikin Haka kuwa su Meera suka Isa gaban kofar Mamy Tace, "ki shiga ciki ni zan juya" Ameera ta gyada kanta mamy ta juya ita Kuma ta tura kofar da sallama, muryar Tace ta makale lkcn da tayi tozali da idon Omar dama bakin kofa yake kallo hakan yasa idanun su ya sarke da juna, Sam Bata lura dasu dad dinba tana Shirin juyawa kenan taji muryar Alhji Kabir na Fadin, "ina Kuma zakije Meera?" Juyowa tayi jikinta na rawa Nan ta karewa mutanen wajen kallo, , "karaso ki zauna kinji" Alhji Kabir ya sake Furta hakan, a hankali ta fara takowa Kamar Wanda kwai ya fashe mata a ciki ta raba can gefen su Alhji Kabir din ta zauna a dofane, still idon Omar a kanta Yana kallon ta akaikaice ji yake kamar ya jawota ta fada a kirjinsa Dan kawai ya shaida mata yyi missing dinta sosai, Alhji Kabir ne ya dubi Ameera dake ta ta raba Ido ta kasa sukuni yace, "kin gane wa'annan?" Ya Mata nuni dasu Omar, kanta ta dukar kasa batace komai ba, Alhji Kabir yace, "mgn nake Miki Ameera, Ameera jikinta na Bari ta daga kanta a hankali Alamar eh, Toh Masha Allah tunda kin gane su "shi Wannan waye dinki?" Ya nuna mata Omar dake kallon ta, ko Bata gani ba tasan Omar yake nufi Hannayen ta tafara murzawa a hankali ta kasa furta komai, hakan yasa dad yace, "Meera ki fada Mana a kawo karshen matsalar" Meera bakinta na rawa Tace, "mi....mi..mijina ne Ada." "mijinki Ada Kuma?" Alhji Kabir ya maimata Abinda Tace shi kuwa Omar a rikice yaso Yin mgn Alhji Kabir ya dakatar dashi da hannu, hakan ya sashi hadiye Abinda yaso Furtawa badan yaso ba, Meera da taji Abinda Alhji Kabir yace ta daga kanta Alamar eh, Alhji Kabir yace, "idan nayiwa abun kyakkyawar fahimta kenan bakwa tare yanzu?" Zuwa yanzu kukan da take dannewa ne ya taso mata hannun ta a baki take fadin, "muna tare Amma so nake mu rabu ya sakeni..." Ta Furta hakan tana rushewa da kuka, shiru dakin ya dauka Banda Omar daya Shiga rudani matuka, Bayan shirun na wani lkci Alhji Kabir yyi gyaran murya Yana duban Omar daya Gama rudewa matuka yace, "Kai kaji Abinda Tace Koh?" Bakin Omar na rawa yace, "pls Ameera kar muyi Haka dake man ni Wlh ban shirya rabuwa dake ba" yyi mgnr da sauri2 hankalin sa na Kara tashi, kallon dad daya sunkuyar da kansa Alhji Kabir yyi kafin yace Masa komai harya Mike ya fice fuskar sa bazakace Yana farinciki ko akasin hka ba, hakan yasa shima Alhji Kabir din yabi bayan Dad Dan ya lura akwai kuriciya sosai akan Ameera, wayar Sadeeq ce tayi ringing hakan ya sashi fita Dan answer call, Kamar Wanda Omar ke jira dake Ameera duk batasan ficewar su ba kanta na Duke sai ji kawai tayi an jawota, a firgice ta dago kanta Nan taga Ashe ba kowa sai Omar da yake kokarin cusata a kirjinsa, cike da Takaici ta dinga zamewa daga jikinsa Fadi take "sbd bakason cigaba na shiyasa kkeson ka sake komar Dani? Wlh bazan yadda ba auren ka a Kaina ya Kare" "Meera pls ki saurareni ni yanzu Wlh nafi bukatar ki bazan iya zama Babu ke ba" Omar ya Fadi hakan Yana sake riketa sosai a jikinsa Dan hanata tashi, kokarin tirjewa taci gaba dayi Tace, "sbd kanason jikina Koh?" Ta Fadi hakan tana zubar da hawaye masu zafi, "No Meera ba Haka bane" Meera tace, "ba gsky bane bana sonka Omar ka sake...." Difff kkeji sakamakon hade bakinsu da yyi Dan kawai ya hanata Furta kalmar sakin nan.
Chapter 109 · 0% Book details