← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 128

Sashe 120

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dubai, akwatina ne reras har 24 tamkar za'a bude shago, su kansu akwati Nan abin kallo ne bare Kuma akai ga kayan ciki Masha Allah, komai acan acan komai yaji, tun daga sutura zuwa inners da bangaren Gwalagwalai, su kansu su Inna fure sun girgiza da Wannan kayan na Meera kwarai d gske suka Yaba wa Omar shiyasa basuyi kasa a gwiwa ba wajen bawa mutanen da suka kawo kayan tukwici me tsoka, kawo kayan nasu yasa aka sa ranar maida Ameeran Nan da kwana uku. Dr. Omar na Gama Shirin bcci ya zaro wayarsa Yana Nemo number Ameera, Ameera dake game saman gado taga shigowar Kiran sa dama a daidai Wannan lkcn suke waya kafin su kwanta cikin kayan daya Basu tun ranar dazai tafi ya sako mata iPhone 11 a ciki, dagawa tayi tana karawa a kunne, Dan kishingida Omar yyi cikin taushin murya yace, "sugar babe" Meera na murmushi ta Amsa Masa a hankali yace "gsky na gaji Wlh I missed you alot" Dan murmushi me sauti tayi tasan yanzu zai fara mata rigima Dan Haka Tace, "ya aiki?" "Alhamdulillah" ya Bata Amsa a takaice, Meera Tace, "Masha Allah, Allah ya taimaka" "Ameen dear how is my twins?" Lumshe ido tayi Bata Amsa Masa ba, "uhumm.. nasan kinji pls ya twins Dina suke?" Yyi mgnr a kasalance, juyi Meera tayi a ranta Tace duk yadda naso kaucewa saika sa mutum kunya da Shiga wani Hali...., "Hello kinaji na kuwa?" Meera Tace, "Bcci nakeji sosai" Omar yace, "yau Kuma da wuri Haka?" Meera Tace, "uhum" "Okay Goodnight Muuuuahhh...!" Ya aika mata da kiss me zafi ta waya, har cikin kwanyar kanta taji kuwa Dan Haka tayi saurin kashe wayar d sauri tana rufe Ido tamkar Yana gabanta, murmushi Omar yyi Dan ya hasaso me take, a fili yace, "gsky da saura dole na cire kunyar Nan Dan bazan Bari a cuceni ba" lumshe ido yyi Yana hasaso yadda zai kasance da Meera duk ranar data dawo hannun sa. Suna breakfast dasu daddy ya dubi Omar dake Shan tea a hankali yace, "tunda ka dawo bamuyi mgnr mutanen ba" daddy ya karasa mgnr Yana duban Omar Dan ya fahimce shi Sarai bayaso ayi mgnr daya danganci su Saratu ransa Kuna yake, take kuwa mood dinsa ya canja saidai ya daure kwarai wajen danne bacin ransa yace, "hakane daddy" kallon Mummy dake dubansu yyi kafin yace, "Case din Yana hannun 'yan sanda har yanzu ba'a Mika shi kotu ba" da mmki Omar yace, "Daddy har yanzu? Me ake jira Kuma?" Dan Jan Numfashi daddy yyi yace, "so nake ka dawo ayi komai Akan idonka" Dan cije lips Omar yyi kafin yace, "ai daddy duk Abinda kuka yanke daidai ne" girgiza Kai daddy yyi Yana fadin, "Sageer ma Yana wajen su a tsare sbd har yanzu yaki gaskata hakan" "ikon Allah" Omar ya furta hakan da mugun mmki, daddy yaci gaba da fadin, "shiyasa nakeson aje can kotu gaban kowa a bayyana gskyr Abinda ya faru Saratu ta furta da bakinta cewar lalle ita tayi mugun aikin" shiru Omar yyi Yana tuno dolen da Sageer yyi wa Meera sanda tayi Masa sharrin fyade, ransa ne ya sosu kwarai Dan yanzu iya takaicin Sageer dinne a ransa, lalle ya kamata Meera ta kasance a wajen Dan itama a wanke ta daga zargin da ake musu coz bazai manta ba yasha Jin lbri daga wajen Sadeeq 'yan skul dinsu na fadin ai lbri ya baza ko'ina ya auri Meera kunyace kawai ta sashi hakan Dan kada yyi biyu Babu ba karatu ba fyaden dayaso Yi shiyasa ya gangare da aure...., "Omar" Daddy ya katse Masa zurfin tunanin daya fada, yace, "kana tare Dani kuwa?" Girgiza Kai Omar yyi Yana sauke numfashi kafin yace, "eh daddy zanso Amma Meera tazo sai a yanke hukuncin" kallon juna sukayi da Mummy kafin ya maida duban sa Kan Omar daya Dan dukar da kansa yace, "hakan ya maka?" Dr. Omar yace, "eh daddy" "Toh shikenan Allah ya kaimu zuwan nata" "Ameen" Omar ya Furta, Mummy Tace, "Toh gyaran gidan da ake an kammala shi kuwa?" Omar yace, "eh Mummy zuwa Anjima ma za'a fara shirya kayan daga Nan kano dad dinta ya tura kayan" Mummy Tace, "ai hakan yafi sauki ma akan daga can Adamawa" Omar ya gyada Kai Yana kokarin tashi yace, "Bari naje gun Hajjaju" da murmushi suka hada baki wajen Furta a dawo lpy, Bayan fitarsa ne daddy ya saki ajiyar zuciya Mummy Tace, "Daddyn Safna lpy dai Koh?" Dan murmushi yyi yace, "yaron ne gaba1 yake ban tausayi" Mummy ta danyi murmushi kafin Tace, "haba Mana sai kace Dan yaro? Yaron ka fa ya girma so ya wuce a dubeshi a Matsayin tausayi pls ka daina Wannan tunanin" daddy yace, "ai Abinda nake nufi shine irin wahalar Rayuwar daya taso lkcn da mlm sale ke bani lbrn Wulakancin da matar Nan take Masa Wlh Saida hawaye ya zubo min" jikin Mummy ne yyi Sanyi Dan itama kwana tayi ranar tana kuka da daddy ya sanar da ita zancen da sukayi da mlm sale Akan renon da Saratu ta Masa, hawaye na gangaro Mata Tace, "haryau Alhji na kasa yafewa Kaina Abinda ya samu Danmu Wlh" girgiza Kai daddy yyi yace, "ki daina daurawa kanki lefi kaddara ce kurum ta riga fata" Mummy na goge hawayenta Tace, "hakane Amma Wlh gani nake kamar da sakacina da nasan Abinda taimakon matar Nan zai jawowa Ahalina Wlh da ko kadan ban kalli inda take ba" ta Ida mgnr tana Jan zuciya ranta na daci tana tuna yadda ta daukaki saratun Kamar wata jinin ta, daddy ya matsa da kujerar sa kusa da ita Yana jawota jikinsa a hankali yake bubbuga bayanta cikin nutsuwa yace, "ki daina fadin Haka Ayush ba'a hada sani da Allah so duk Abinda ya faru mu dinga dangana dashi Dan ya fimu sanin daidai, daya tashi ikonsa ma duk yadda matar Nan taso ya wulakanta ya tozarta ya zama mutumin banza marar amfani Allah beyi ba Saiya iyoshi nutsatse, kamili, me riko da Addini da Kuma kaifin basira, Allah ya hore Masa baiwa kala2 wadda tun farko ya kamata ace ta fahimci ba'a yiwa Allah wayo Amma ta kasa gane hakan, Haka zalika ki duba Rayuwar Sageer harga Allah munyi Masa riko irin na Iyaye da 'ya'yansu kullum burinmu yaci gaba, ya zama mutum na gari abin kwatance dukda Yana Bata Mana Rai a kullum bama gajia wajen Yi Masa Addu'ar shiriya Amma me gari ya waya? Cikin tsarkin mulkin Allah ya nuna Mana ikon sa, dama Fadar Allah ce shi kadai ne zai iya shiryar ga Wanda yaso bawai mutum ba, Koda duniya zasu taru su hanaka ci gaba idan Allah yaso ikonsa sai kaga kaci gaba idan Kuma kowa naso kaci gaba idan Allah beyi niyyar hakan ba babu me sawa hakan ta faru a kanka, so Wannan ya ishemu izina domin Allah shi keyin yadda yaso a lokacin dayaso." Ba karamin kwantar Mata da hankali kalaman daddy sukayi ba, Dan Haka ta dago kanta da murmushi Tace, "har abada bazan daina yiwa Allah godiya daya hadani dakai a Matsayin mijina ba, domin kaidin na dabanne a cikin Jerin magidanta masu kokarin tunatar da iyalan su Abinda Allah yace Annabi yace" murmushi shima ya mata yace, "Kedin ma ai ba kowanne namiji ke samun mace ta gari irinki ba" dariya Mummy tayi tana me shigewa jikinsa. Yau ta kasance ranar da aka tattara Ameera tun daga Adamawa aka kawota kano tare da rakiyar, Inna fure, Asma'u, Mami, da Kuma Ahmad dad da Kuma Abban Ahmad ne ma kawai suka Bari a gidan tun kafin su iso kuwa gidan Alhaji Abdullahi suka shirya musu tarba me kyau d gara kala2 Kai kace biki ake Koda yake kusan ma bikin ne ya taru Dan Mummy walima ta hada ta gayyato duk wani masoyinta na nesa Dana kusa kawaye da abokan arziki Abu dai daga dawo da Meera dakinta ya juye zuwa wani shahararren biki dama a waje anata kishin2 Nan fa mutane suka sake Tabbatar wa domin Mummy speaker ta dauka ta sanar da waye Omar a gareta, kowa ya tausaya musu Haka kowa ya girgiza da Jin Wannan lbrin, a ranar dai Omar be samu ganin Meera ba Dan tana wajen Mummy Haka 'yan Adamawa Suna Nan, washe garin ranar kuwa Bayan sun gano gidan Meera suka Fara Shirin juyawa har Airport Omar da Sadeeq sukai musu rakiya Bayan Sha Tara ta arziki da aka hada musu lalle su Inna fure sun yaba kwarai da dacen gidan mutunci da Meera tayi har kwallar farinciki Saida tayi da taga yadda kowa ke kaunar Meera jinin Aminatu yanzu Kam hankalin ta ya kwanta kwarai dgske. A hanyarsu ta dawowa ne Sadeeq ya dubi Omar dake kallon window yace, "Ango kasha kamshi" Omar ya juyo da murmushi fal fuskar sa yace, "saura Kai" Sadeeq yace, "ai karka wani damu Nan da wata daya Nima zan Faso" 'yar dariya Omar yyi kafin yace, "harta amince ne?" Murmushi Sadeeq yyi Yana juya steering mota yace, "toh an Gaya maka nidin na wasa ne?" Omar yace, "yeah I see baka da sauki" Sadeeq yace, "kwarai kuwa ba Kamar Kai bane dazan ta aje Abu a Raina naki fitar dashi" Omar yace, "Toh aku sarkin mgn" Sadeeq yasa 'yar dariya yace, "congratulations once more again" "tofah irin Wannan congrats Haka?" Sadeeq yace, "Kai ai dole a tayaka murna Wlh domin kasha dakyar, ka Kuma tsallake rijiya da baya" hararar sa Omar yyi yace, "sai kace gudun yaki* Sadeeq yace, "uhum..uhumm bawan Allah daina tuna baya kawai" murmushi Omar yyi yace, "Toh me akai a bayan?" Sadeeq yace, "da za'a hasko maka yadda ka gigice a tsakankanin kwanakin daya wuce billahi sai kayiwa kanka dariya tab.." ya Ida mgnr Yana sakin dariya, cije lips dinsa Omar yyi kafin yace, "Toh naji ya Isa Haka sarkin Sharri" Sadeeq yace, "dama Haka zakace ai" Dan murmushi ya Masa Yana kauda Kai, Sadeeq yace, "idan na ajeka gida yanzu da wanne time zanzo maka rakiya zuwa wajen Amarya?" Juyowa Omar yyi da sauri yace, "rakiya?" Sadeeq na Dan danne dariyar sa yace, "eh ai kasan Haka ake a Al'adance abokan Ango na yiwa Ango rakiya har dakin matar" "kuttt..." Omar ya furta
Chapter 120 · 0% Book details