← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 128

Sashe 59

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ja baya Meera tayi a tsorace jikinta na rawa Tace, "Dan Allah kayi hakuri na dauka bakaji bane" Wani mugun tsaki Dr. Omar Yaja kamar ya maketa Haka yakeji Dan haushi juyawa yyi da nufin tafiya a hanzarce Meera Tace, "dama cewa zanyi Dan Allah ka Barni na koma school" cak Dr. Omar ya tsaya shi be juyo ba shi beyi mgn ba, Meera na ganin Haka tadan matso kusa dashi tace, "Wlh duk banajin Dadi zaman kadaici yamin yawa ne Kuma...." Bata karasa mgnr da take furtawa ba taji an debe ta da wani irin gigitaccen Mari, sbd zafin Marin daya shigeta Saida tayi wata irin katantanwa saura kadan ta zube kasa taji an cakumo hijab din nata, Dr. Omar ne ya riketa sosai jikinsa na Bari sbd tsabar dacin bacin ran da yake ciki a yanzu Ashe shirun d yyi tsuma kurum yake Yana kokarin controlling anger dinsa yaji taci gaba da mgn Wanda yakejin Kamar Ana dura Masa dalma ne a kunne, idonsa ne yyi jajir Yana fitar da hucin zafi ya fara mgn a kausashe yace, "kinaso ki koma school? Kadaici ya dameki?" Yyi mgnr Yana tsareta da Ido, Meera da tun dazu take ambaliyar hawaye ba damar ware baki sai Jan zuciya ta kasa ce Masa komai jikinta itama sai rawa yake Dan azabar da take ciki, Tsaki Dr. Omar Yaja Yana Kara tamke rikon da yyi mata yace, "kin Kara Tabbatar min da kedin kwata2 bakida hankali, wawiya ce ke, Bakida tunani, Oh na manta kinason haduwa da shedanin naki dake waje Koh? Ah no wonder zaman kadaici ya dameki domin kin kwana biyu Baku kebe ba" Meera dake Jan zuciya dakyar sbd mugun shakar da yyi Mata tahau girgiza Kai dakyar take fadin, "Wlh ba nufina kenan ba" buge mata lips dinta yyi d hannu Yana fadin, "Dallah yimin shiru, An Gaya muku ban gane Shirin ku bane? Kun dauka kowama irinku ne me Kwakwalwar kifi? Sbd ki Taya shi zubar min da mutunci Kika zabi ya tube Miki kaya a filin Allah Kuma..." da hanzari Meera ta katse shi da fadin, "haba ya Omar nifa ba Haka nake ba, ka daina zargina akan Abinda Babu tabbas" binta da kallo yyi Yana sake hade Rai sosai yace, "musu zakimin?" Girgiza Kai Meera tayi tana Jan zuciya, a zuciye ya sakar mata hijab din saura kadan ta Fadi sbd yanayin sakin na mugunta d yyi mata, hakan ya bawa Meera Daman matsawa can nesa dashi tana share hawaye, Cije lips dinsa yyi harya juya Kuma Saiya juyo Yana dubanta yace, "kee.." Meera data sunkuyar da kanta ta dago tana kallon sa duk idonta yyi ja, "Biyoni bazan barki a gidan Nan ba Dan ban yarda dake ba" yyi mgnr Yana wucewa gaba, binsa da kallo tayi Anya taji daidai kuwa? Wata zuciyar tata ce ta Kara Tabbatar Mata da zancen nasa hakan yasa ta bishi da sauri Dan har ya shige mota, Kokarin bude baya take Dr. Omar ya juyo tare da zube mata zakunan idonsa a kanta yace, "I'm ur driver?" Yyi mgnr Yana sake wara Mata idon nasa, juyowa tayi a rude ta dawo kofar gaba Kamar wacce aka shafe mata komai na Kai Haka tayi ta Kokarin bude kofar ta kasa sbd yadda hannunta yake rawa, "Mtwsss.." Dr. Omar Yaja tsaki me karfi yana me bankada kofar da gayya harta sameta a ciki, rike cikin nata Meera tayi cikin zugi taji yace, "Zaki shigo ne mu tafi ko saina fito wajen?" A firgice Meera ta fada motar tasa tana dafe cikinta da yake mata ciwo dakyar ta jawo murfin motar ma sbd yadda taga ya fisgi motar da sauri, Lumshe ido Meera tayi hade da kifa kanta cikin cinyarta tana share hawaye masu dumi da suke zubo Mata. Direct company din da yake aiki ya wuce da ita, lkcn da suka Isa Meera kanta a duke yake batasan sun iso ba sai karar rufe kofarsa da taji yyi, Dagowa tayi da sauri tana binsa da kallon mmki be mata mgn ba yyi gaba abinsa, Ganin Haka yasa Meera ta fito da sauri itama Dan bataga amfanin zaman nata ba, fitowar ta keda wuya ta tsinci kanta da karewa yanayin company din kallo, ba karamin mmki tayi ba Dan tabbas tanajin sunan company din kenan anan Dr. Omar yake aiki? Bata da Wannan amsar tmbyr tata Dan Haka ta bi bayansa da sauri domin ya fara Yi mata nisa, kanta ne ya sake daurewa musamman da taga duk Wanda ya wuce zai duka ya gaishe shi sai kace shine me company din, Haka ta dinga binsa kamar jela yyinda Dr. Omar yake tafiyar sa cike da izza ransa a matukar hade duk Wannan gaisuwar da sauran ma'aikatan suke Masa baya kulasu, a Haka suka karasa har can sama ya bude kofar office dinsa ya shige, Meera na zuwa daidai kofar ta daga kanta sama tana karewa sunan office din kallo, General manager ta maimaita hakan a ranta, What? Me hakan ke nufi? Ya Omar Yana Dr. Ya koma General manager na company? Tayiwa kanta Wannan tmbyr da Babu me Amsa mata, tura kofar itama tayi da sauri ta hango shi Yana kokarin bude wata kofar dazai sadashi da ainahin office dinsa, PA dinsa Habib dake gyara takardu ya taso da sauri Yana tare Meera din yace, "ke wacece ke da Zaki wuce mutane ba mgn ko an Gaya Miki dandalin mabarata ne Nan?" Yyi mgnr cikin tsawa, bude kofar d Dr. Omar beyi ba kenan ya juyo a zuciye, d sauri Habib yace, "sorry sir yanzun Nan zan sata tabar Nan wajen mutanen ne da kulafuci sun fiye nacin roko..." "Enough Habib" Dr. Omar ya Furta hakan cikin karaji zuciyar sa na zafi, a tsorace Habib Yaja gefe jikinsa na rawa Dan zuwa yanzu shakkar Dr. Omar din yake, Kallon yanayin office din Dr. Omar yyi yaga Babu Alamar shara, ya tsaida kallon sa Kan Habib daya takure waje daya yace, "meyasa yau ba'a gyara wajen Nan ba?" Yyi mgnr Yana tsaresa da Ido, cikin kaduwa Habib yace, "har yanzu me aikin be iso bane" "Mtwssss.." Dr. Omar Yaja tsaki yace, "kaje yanzun Nan ka tattaro duk wani kayan aikin da za'a gyara office dinnan ka kawo" "Okay Sir" Habib ya furta hakan da sauri Yana barin office din, yyinda shi Kuma Dr. Omar ya shige nasa office din ko kallon bangaren inda Meera take beyi ba, Meera data Sha jinin jikinta ta takure waje guda ta kasa Koda daga kafa daya gaba1 hankalin tane ya sake tashi bisa ganin Isa da mulkin da taga Dr. Omar din yake nunawa a Wannan company din lalle ta dauro dala ba gammo domin Sha'anin Dr. Omar ya girmi tunanin ta, Kamar bazata bishi cikin ba taga cewa Babu amfanin tayi ta tsayuwa batare da tasan Matsayin zuwanta wajen ba yasa ta bishi har cikin office din, Yana zaune Kan doguwar kujerar dake cikin office dinsa wasu takardu yake dubawa da alama sunada muhimmanci yadda taga ya bada hankalin sa wajen sosai, daga gefen kofar ta rakube Bata karasa ciki ba, tana daidaita tsawurta kenan Habib ya shigo da sallama, Dagowa Dr. Omar yyi Yana kallonsa bece komai ba, Habib yace, "Sir kayan suna Nan waje duk na kawo" girgiza Kai Dr. Omar yyi kafin yace, "kaje can waje ka jira kafin a Gama" da mmki Habib ya kalleshi ya kalli Meera dake manne jikin bango kamar kadangare a takure ya bude baki zaiyi mgn Dr. Omar ya katse shi da tsawa yana fadin, "ko bakaji Abinda nace bane?" A rude Habib yace, "i'm sorry Sir" yyi mgnr Yana juyawa da sauri Dan barin office din, shiru office din ya dauka Kamar ba mutane sai karar takardun da Dr. Omar yake dubawa a hankali, Meera Kam kallon ikon Allah kawai take agun miskilancin Dr. Omar, kamar daga sama taji yace, "kije ki dauki kayan aikin da Habib ya kawo ki fara gyara wajen kafin ki shigo Nan shima ki gyara" wara ido sosai Meera tayi da mugun mmki batasan lkcn da tace, "nidin?" Dago dara-daran idanunsa yyi Yana kafeta dasu yace, "a'a ni" yyi mgnr Yana binta da mugun kallo, Kame bakinta Meera tayi batace dashi komai ba Kawai ta juya cikin tsananin tausayin kanta tabar Masa office din, tana fitowa ta tarad da kayan inda Habib ya ajiye, kallon su tayi tana Dan goge kwallar data ziraro mata ta Wutsiyar Ido, Bata da zabin daya wuce tayi Abinda yace din, Dan Haka ta zage sosai ta gyara inda PA dinsa ke zama, bayan ta Gama ne ta shiga ciki inda yake har yanzu Yana Kan kujera, batayi Masa mgn ba ta fara aikinta shima be dago ya kalleta ba harta Gama gyara wajen ta shige cikin toilet dinsa, Shigarta toilet din keda wuya aka turo kofar office din, Dr. Omar na zama kenen shima akan kujerar aikinsa yaji turowar kofar harda sallama cikin siririyar murya tajan hankali, zamansa ya gyara Kan kujera kafin ya dago kansa a tunzure yace, "Wai ke wacce irin mayyace ban sani ba?" Salma data Sha kwalliya sosai fuskar ta cike da Annuri ta matso gabansa cikin takun yanga tana juya cikakkun hips dinta tace, "haba Mana Dr. Calm down meye abin zafi Kuma?" Ran Omar ne ya sake baci zaiyi mgn kenan Salma ta tare shi da fadin, "ai Naga sakon ka na korar da kayimin shiyasa nazo Yi maka godiya" tsaki me sauti Dr. Omar yyi yace, "ko ki ficemin a office ko na sa a Kira cleaners din company Dinna su fitar min dake" 'yar dariya Salma tayi tana Dan rankwafowa Kan table din gabansa tace, "Dr. Omar kenan naji da farko Kamar kace mayya, Yes mayya ce Amma mayyar da take kwana da tashi da kwadayin samun ka" ta karasa mgnr tana kyasta Masa ido daya, a tunzure Dr. Omar ya tashi Yana fadin "cleaners" da karfi duk ya mance ma ba lalle su jishi ba, saidai Kash daidai lkcn Meera ta fito daga toilet din nasa tana gyara zaman hijab dinta, dukansu juyawa sukayi suna kallon ta, itama dagowar da zatai ta gansu a tare, Salma ce ta kwashe da dariya tana nuna Meera Tace, "Wai dama irin Wannan cleaner dinne zasu fitar Dani?" Tayi
Chapter 59 · 0% Book details