← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 128

Sashe 43

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

**** Tun daga bakin gate din yake Kara karewa yanayin company din kallo, dukda yau satinsa guda da Fara aiki dasu Amma ji yake kamar Wanda ya Dade dasu Dan ba karamin Dadi yakeji ba idan Yana tare dasu, duk lkcn daya Sanya kafarsa cikin company din ji yake wani irin bakon yanayi na fisgar sa game da company din, idan kuwa Yana tare da Alhaji Abdullahi jinsa yake zuciyar sa na fari, yadda sukayi sabo da Alhji Abdullahi Kai kace sun Dade ne, da Wannan tunanin nasa ya Isa gaban office din Alhaji Abdullahi Dan yace yau yaje da wuri akwai mgnr da zasuyi, Saida aka bashi izini kafin ya Shiga, da murmushi Alhaji Abdullahi ya Amsa sallamar Dr. Omar din sannan yace, "Bismillah zauna" zama Dr. Omar yyi Yana fadin, "Allah yasa banyi late ba Alhaji" Dan murmushi Alhaji Abdullahi yyi yace, "ai ni ban taba haduwa da mutumin dayasan muhimmancin lkci ba sama dakai Omar shiyasa nake jinjina maka domin kaidin na daban ne" murmushi Dr. Omar yyi bece komai ba, hakan yasa Alhji Abdullahi ya dubi Dr. Omar din sosai yace, "Omar" "Na'am" Dr. Omar ya Furta hakan Yana me tattara nutsuwar sa shima, Alhji Abdullahi yace, "tun ranar da Allah ya hadamu kawo yanzu ban taba haduwa da jarumin mutum irinka ba, na gwadaka ta hanyoyi da dama cikin ikon Allah ka haye batare d kasan gwadaka nake ba, hakan yasa naji zuciyata ta Kara nutsuwa dakai dukda tun farko naji na yadda dakai 100% shiyasa a yanzu nakeson Dora maka wani nauyi" "Nauyi?" Dr. Omar ya Furta hakan da mmki, Alhji Abdullahi ya girgiza Kai yace, "kwarai" kafin yaci gaba da fadin, "a zahirin gsky nidin Nan ba mazauni bane, ban cika zama ba sbd wasu harkokin da nake dasu acan other countries din That's why nace Zan Dora maka wani nauyi, Toh Amma a yadda na fahimceka bazaiyi maka wahala ba" Dan Jan Numfashi Dr. Omar yyi yace, "Toh Allah ya bani ikon dauka" "Ameen" Alhaji Abdullahi ya Amsa Yana murmushi sannan ya danna kiran Manager, ba'a dau lkci ba kuwa saiga manager din yazo, knocking yyi aka bashi izinin Shiga kafin ya tura kofar hannayen sa rike da wasu takardu, Amsa Masa sallamar sukayi hakan yasa shima ya samu kujera ya zauna Yana Dan hararar Dr. Omar kasa-kasa a ransa yanajin haushin yadda yaga Alhji Abdullahi yake nan-nan dashi duk ya toshe Masa fadarsa kullum bakajin komai bakin Alhji Abdullahi sai yabon sa, Alhaji Abdullahi ne ya katse Masa tunanin da fadin, "yauwa Habib ka tattaro takardun?" Habib yace, "yes sir gasu Nan ma" Yyi mgnr Yana Mika masa su, karba Alhaji Abdullahi yyi Yana dubasu a hankali harya Gama gani kafin ya ajesu gefe wasu irinsu ya dauko daban dake can gefe ya sake duba su Suma kafin ya dago kansa ya kalli Dr. Omar yace, "karbi ka gani" ya Fadi hakan Yana Mika masa, karba Dr. Omar yyi ya maida hankalin sa kansu yana dubasu sosai da mugun mmki ya dago Yana duban Alhaji Abdullahi kansa ya daure Yana bukatar Karin bayani, Alhaji Abdullahi yace, "kaga sunan kane akai Koh?" Girgiza Kai Dr. Omar yyi har yanzu kansa a daure yake da Abinda ya gani, Dan murmushi Alhaji Abdullahi yyi ya dubi manager Habib dake zaune Yana cika Yana batsewa a ransa Yana Raya duk lkcn da Alhaji Abdullahi yabar kasar Saiya wulakanta Wannan me shegen ji dakai din mutum yazo a bayanka ya dinga nuna maka Isa sai kace shine manager yasan dai duk tsiya idan an bashi aiki a company din shine a saman sa...., Katse Masa tunani Alhaji Abdullahi yyi da fadin, "sakon Dana fada maka jiya kasa an sanar musu?" Habib yace, "Yes sir ai tun dazu ma'aikatan company dinnan suke can wajen Meeting Kai ake jira Nima yanzu can zanje mu jiraka" "Weldon" Alhji Abdullahi ya Furta Yana ci gaba da fadin, "aikin ka yyi kyau kaje Ina Nan tafe" ya Furta hakan Yana dauko wani file, tashi Habib yyi ya sake hararar Dr. Omar da tun dazu ya zama kamar statue sai bin Alhaji Abdullahi yake da kallo hade da takardun wajen sa, Bayan tafiyar Habib da minti goma Alhaji Abdullahi ya umarci Omar su tafi, Nan suka fito a office din kowa da file a hannun sa, can hall wajen meeting sai surutu ake yyinda matan wajen ke gulmar Dr. Omar kowa Fadi yake wani handsome guy yazo company din, Wanda Basu San da zuwan sa bama duk sun qagu ace Dama su ganshi, Ana haka akaji zuwan me company din Alhaji Abdullahi, wajen da ake tanadar Masa na zama ya nufa tare da Dr. Omar Nan dukannun suka zauna yyinda hall din yyi tsitt kamar ba kowa, Bayan Addu'a da akayi aka shafa Alhji Abdullahi yyi gyaran murya Yana duban ma'aikatan company din nasa yace, "Kamar yadda muka Saba lkci zuwa lkci muna haduwa ayi zaman meeting sannan a tattauna Abinda ya shafi Wannan company din, anan zamu fahimtar da kowa shin company din Yanaci gaba ko yyi kasa?" Yyi mgnr Yana dubansu sosai duk sunyi tsitt anajin ta bakinsa, kafin yaci gaba da fadin, "Alal hakika tun Bayan rasuwar manager na Abdul Kareem wata 8 kenan ban sake ganin ci gaban Wannan company din ba, Ada duk inda ka waiga a Nigeria bama iya kasar Nan ba harda sauran kasashe zakaji Ana fadin sunan company dinnan (A.A OMAR MAI FATA) Amma yanzu ko a kasar tamu ma ba ko Ina kkejin muna tashe ba shin na tmbyeku meye matsalar?" Shiru yanzun ma akayi Babu me mgn, Hakan yasa Alhaji Abdullahi yace, "dukda bana kasar hakan baya nuna Wai bansan meke gudana ba, Dan haka Ayau dinnan a gaban kowa nake sanar daku sabon GENERAL MANAGER din company dinnan wato DR. OMAR SALEES" yyi mgnr Yana pointing din Dr. Omar Da hannu, a firgice Habib manager ya kalli Dr. Omar, yyinda Dr. Omar ke kallon Alhaji Abdullahi inda Kuma sauran mutanen company din suka zubawa Dr. Omar Ido.Girgiza Kai Alhaji Abdullahi yyi Yana dubansu duka biyun Dr. Omar da Habib yace, "kwarai kuwa shine sabon manager dinku, Yanzu shine me fada aji a Wannan company din, duk wani shige da fice ya dawo wajensa" kafin ya juya Yana duban sauran ma'aikatan da suka fara kus-kus kallon su yasa kowa yyi tsit, yace, "Ina fatan zaku bada hadin Kai domin samun cigaban Wannan company din?" Nan kowa ya fara mgn eh zasuyi, ba matsala, Daga musu hannu Alhaji Abdullahi yyi yace, "Ina fatan hakan domin duk Wanda yyi Sanya a aikinsa zaiga Sanya a offer sa" Yyi mgnr Yana kallon Dr. Omar da yyi shiru tun dazu ba bakin mgn, Dan murmushi yyi a Karo na farko Dan tunda aka shigo Alhji Abdullahi beyi murmushi ba Yana kallon Dr. Omar yace, "ina fatan zaka tashi ka gabatar musu da kanka?" Girgiza Kai Dr. Omar yyi cikin ladabi ya Mike tsaye kowa na wajen ya zuba Masa ido Kai kace Wani sabon halittar ne Dan cije lips yyi yanajin wani iri yadda yaga an zuba Masa ido Dan shi bayason yawan kallo to Amma ya ya iya? Dan haka dakyar dai kamar bayason mgn ya gabatar musu da kansa, "Wow!" Wasu Mata suka Furta hakan cikin birgewa, Sbd yadda sukaga Dr. Omar yyi mgn da aji ga Isa ga murya Kai kace Dan sarki ne hakan yasa tashin farko yyiwa da yawan matan company din farat daya a soyayya Gama mgnr sa keda wuya kuwa ya fara Jin tafi raf-raf daga matan har mazan sbd yadda ya birgesu, Dan murmushi yyi hade da daga hannun sa daya kafin ya sake hade hannun nasa Alamar godiya sannan ya koma wajen zaman sa, habawa Wannan salon da yyi tuni ya sake tafiya da imanin sauran matan, har wasu suna fadin kodai ba'indiye ne? A bangaren Habib kuwa ji yake kamar ya fashe Dan haushi harma yaji zaman ya gundure sa Amma sama takai yaji Alhji Abdullahi yace, "Wanda zai zama PA dinsa shine Habib sani" Nan fa aka fara surutai wasu na dariya kasa2 Habib kuwa ji yyi kamar yaje ya shake Alhaji Abdullahi ya huta, a haka dai aka tashi a Taron. lkcn da suka koma office Dr. Omar yyi gyaran murya yace, "inada mgn Alhji" Alhji Abdullahi kansa na kasa Yana rubutu yace, "kozan iya samun damar ka kirani da daddy?" Yyi mgnr Yana Dagowa hade da zube idanun sa Kan Dr. Omar, wata irin kunya yaji Dr. Omar din ta Kama shi, hade da Kara ganin girman Alhaji Abdullahi a idon nasa sosai, Dan haka ya zame idon nasa zuwa gefe a hankali yace, "Eh" Daddy yyi murmushi kafin yace, "Thank you" kallon sa Dr. Omar yyi da mmki shifa lamarin mutumin Yana bashi mmki matuka yadda yake tsammanin sa har ya wuce haka shikam besan wanne irin Gamon jini ne Wannan ba, "Fadi mgnr taka" yaji Alhji Abdullahi ya katse shi, Dr. Omar yace, "am..Toh Daddy dama nace Wai Naga background din karatuna medicine ne Kuma kasan haka Ina lefin ko karamin aiki a bani memakon manager?" Alhaji Abdullahi ya maida dubansa sosai Kan Dr Omar yace, "dame ma ka kirani?" Dr. Omar yace, "Daddy" Alhji Abdullahi yace, "Dakyau hakan ya nuna nidin mahaifin ka ne" Alhji Abdullahi ya Furta hakan a ransa yanajin wani Abu na Dakar kirjin sa, daidai lkcin da Dr. Omar yaji shima wani Abu ya tsirga Masa a zuciyarsa, take suka kalli junansu na wasu seconds kafin Dr. Omar ya janye idonsa d sauri, Alhaji Abdullahi ya sauke ajiyar zuciya Yana ci gaba da fadin, "Yess ni din kamar mahaifin ka ne Dan haka iyaye nada damar su bawa Dansu Abinda suke so, karka dauka sbd karatun ka zakayi aikin no ka dauka Kamar mahaifin Kane ya baka company dinsa ka kula dashi, Banson kayi musu Akan Abinda na baka ko Wanda zai biyo baya sbd tuni ka Aminta Dani a Matsayin mahaifi, Banda saurin sabo ko sakewa da mutane Amma cikin ikon Allah a kanka Naga canji, Kuma ka cancanci rike Wannan ragamar company din, Ina maka kyakkyawan zato bana tunanin zaka cutar Dani" Yyi mgnr Yana Mika masa wasu keys, karba Dr. Omar yyi yace, "su Kuma Wannan na miye?" Alhaji Abdullahi yace, "daidai inda
Chapter 43 · 0% Book details