← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 128

Sashe 42

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Saratu na Shiga daki ta fara safa da marwa, tunanin zuwa wajen boka take tabbas dole taje a Kara yiwa Asirin da tayi takunkumi, A hakikanin gsky duk Wanda yaga Dr. Omar da Alhaji Abdullahi yasan ba karamin Kama suke ba, a fusge kuwa Yana yanayi da Hajia Aisha, sosai ya matso kyau daga dukkan bangaren su Kai harma ya fisu kyau, haka zalika dukda Safna tana mace ya fita kyau nesa ba kusa ba, shi kuwa Sageer baki ne sosai kamar yadda uwarsa Saratu take baka gwara mlm sale yadan haska, Toh shi Sageer sbd hutu d Jin Dadi da yake ciki yasa ba'a ganin bakin sa sosai kazalika Yana Amfani dasu Mai Wanda zaisa fatarsa tayi haske a kamanni kuwa yanayi yake da Saratu, ganin Wannan siffa yasa Saratu tun suna jarirai ita da Nas sukaje akayi Asirin dazai rufe bakin jama'a, ya share tunanin duk mutumin dayaga Wannan kamar hakan yasa Babu Wanda ya taba Furta wane kamar sa kaza, lkcn da Omar ya fara mgn ta fahimci irin mutanen Nan ne masu zuciya da kafiya Wanda basa barin Kota kwana nanma tsoro ne ya kamata Dan yadda taga baya ragawa kowa yasa tuni taje Nan ma akayi Mata aiki a kansa yadda zata dinga controlling dinsa yadda takeso, taci mutuncin sa yadda takeso, batare da yyi gigin ramawa ba dogon numfashi taja tana tunanin dole tayi asubanci gobe Dan bataga ta zama ba Nan ta fara lalumen Number Nas Dan shaida Mata Abinda ke faruwa, Bayan sun Gama Waya da Nas suka shirya yadda zasuyi tafiya, Washe garin ranar kuwa da duhu2 Asuba ta fice daga gidan.
Chapter 42 · 0% Book details