Sashe 27
Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajia Aisha ta furta, Safna tana Shirin fita Dan ta Gama tace,
"Shiyasa yau na jiki so silent Allah ya baki lpy"
"Ameen"
Saratu ta Amsa, Anan Safna tayi musu sallama ta tafi, yyinda Hajia Aisha tace,
"toh idan kinkai wa Hajjaju breakfast din saiki zo ki tafi gida"
Dadi ya Kama Saratu Amma sbd kar a kamo ta tace,
"haba Hajia ayi haka? Ba wani aikin ne?"
Hajia Aisha ta girgiza Kai tace,
"Naso yau muyi aiki sosai sbd Daddyn Safna zai dawo"
adan firgice Saratu tace,
"yau???"
Batare da Hajia Aisha ta lura da yanayin ta ba tace,
"Insha Allahu zuwan bazata zai Mana ai shiyasa ko sauran security ba'a sanar musu ba driver kadai zaije dauko shi"
ta karasa mgnr tana murmushi, Wani irin Kullutun Abu ne ya dankare kirjin Saratu, lalle dole nayi wani Abu kafin Mlm sale ya samu lfyr dazai tona Asirina, A fili kuwa cewa tayi,
"Kai Masha Allah, Allah ya kawo su lpy"
"Ameen"
Hajia Aisha ta furta kafin taci gaba da fadin,
"karki fadawa kowa fa musamman Auta Safna yanzu Sai ta kasa zaman skul sbd murna"
Wai Safna? Wato itace kadai 'ya ba'a ma ta batun danta Sageer ake ba, Saratu ta furta hakan a ranta, a fili kuwa tace,
"Ai karkiji komai Hajia kamar kin haka kin birne"
ta karasa mgnr tana dariya Kai kace gske ne, itama Hajia Aisha dariya tayi tace,
"jeki sai kizo ki tafi sbd yanayin jikin naki nasan dauriya kawai kike"
murmushi Saratu tayi tana tashi tabar wajen, a gurguje ta mikawa Hajjaju kayan karinta ta fito, Bayan tayiwa Hajia Aisha sallama sannan tabar gidan.
****
A bangaren Dr Omar kuwa tun kafin 8 ya shirya Yana Sanya agogo a hannun sa yaga message ya shigo wayarsa, dubawa yyi sai yaga ance _kayi hakuri an dage karar zuwa karfe goma 10am_ kansa ne ya daure sosai Toh meyasa suka dage karar? Dan tabe baki yyi a fili yace,
"ku Gama zagaye-zagayen ku dole ku bawa yarinya hakkin ta"
Yana Gama Shirin ya fito ya samu mlm sale a kofar dakinsa, gabansa yaje ya gaishe shi dukda ba mgn yake ba Amma Yana gaishe shi koyaushe, Lkcn Sahabatu ta Gama shirya kayan siyarwar ta Dan waken safe takeyi, Dauka tayi batayi musu mgn ba ta fice,
binta da kallo sukayi a bangaren Dr. Omar ransa na zafi idan yaga Wai kanwar sa ce keyin talla a tashar mota abin na kona Masa Rai, a bangaren mlm sale kuwa Fadi yake a ransa kin cuceni Saratu, kin tarwatsa min Kan iyalina, sbd son zuciya da kwadayi kin dauko yaron da aka haifo a babban gida kinsa Dan mu a maimakon sa sannan 'yarki mace kullum tana yawon talla Babu zama Insha Allahu duk Abinda kike buri bazai Tabbata ba, Dr. Omar ne ya katse shi da fadin,
"Zan fita Abba ayi Mana fatan nasara kamar kullum"
murmushi mlm sale yyi ya Dora hannun sa bisa kansa ya girgiza Kai Alamar Yana Masa fatan Alkhairi, Kamo hannun nasa Dr. Omar yyi Yana murmushi hade da sumbatar hannun yace,
"Nagode Abba Allah ya baka lpy, Insha Allahu yau mlmin zaizo"
Abba ya girgiza Kai Yana murmushi Nan Dr. Omar yyi Masa sallama ya fita.
Fitowar sa keda wuya kawai yyi niyyar zuwa skul Dan yace Mata ta fito da wuri Toh yasan Kila zata jirashi, Hawansa napep keda wuya yaji Kiran Dr. Sadeeq Bayan ya daga daga dayan Bangaren Dr. Sadeeq yace,
"Dan Allah kazo AKTH Ana bukatar ganin ka"
Dr. Omar zaiyi mgn Dr. Sadeeq ya katse shi da fadin,
"it's urgent please"
"Okay"
Dr. Omar ya furta Yana fadawa Me Napep din ya kaishi can.
°°°°°
Tun da garin Allah ya waye Ameera take cikin tsananin faduwar gaba da tashin hankali, Babu Abinda ke Kara daga Mata hankali idan taga su Anty shafa suna dariya hade da sake maimaita Abinda Sageer yace zaiyi, zancen karar ko Mom basuyiwa mgnr ba Dan haka Babu Wanda yasan Abinda ake ciki, gani tayi tun 7:30 sun shirya zasu bar gida, Abinda ya Kara daure Mata Kai yadda taga ba driver ne zai kaisu ba Kuma kafin su fita sun Tabbatar Mata karfe 10am ne karar karta sake ta fito idan ba haka ba Sageer ya baza yaransa a lungun unguwar tana fitowa suyi kidnapping dinta idan yaso Nan ma akaje kotu sai a likawa Dr. Omar ne ya sace ta, gaba1 sun dagula Mata lissafi, gashi ko number sa Bata dashi bare ta Gaya masa halin da ake ciki.
~~``
Tun daga kofar gida Saratu take kwadawa Nas sallama, Nas ta fito cikin fada tace,
"Kai ni wacce jarababbiyar ce me min Wannan sallamar?"
Turus tayi ganin Saratu ce a bakin kofar, Kama baki tayi tace,
"Saratu ungulu kenan ganin ki ba Alkhairi ba ni nasan da wata a kasa"
ta fada tana dariya, cire mayafin ta Saratu tayi tana zama kan kujera 'yar tsugunno ta tsakar gida tace,
"Kina dariya kinsan bala'in dake Shirin tunkaro mu?"
Nas na jawo wata kujerar ta zauna tace,
"Kinje kin sake subutar bakin Koh?"
Ta fada hankalin ta na Shirin tashi, Saratu ta girgiza Kai tace,
"Wannan tsinannen yaron Mana Maru"
Nas tace,
"meke faruwa?"
Saratu tace,
"Ana zaune kalau tsabar naci irin nasa kinji Wai ciwon mlm da alama Sihiri ne Dan haka Ayau dinnan zaije dauko mlmin dazai duba mlm"
"kut*r uba"
Nas ta furta cikin masifa tace,
"kina wanne shashanci ne Kika Bari ya fara tunanin haka?"
Saratu tace,
"ke da anyi Abu sai ki likamin lefi Toh ni nasan yaushe ya fara nazarin haka? Zatona da yyi shiru ko bazaiyi komai akai bane"
Nas tace,
"bala'i, kur'ani bamuga ta zama ba Yasin"
Saratu tace,
"Toh Kinsan ance Ana bikin duniya ake na kiyama Koh?"
Nas tace,
"wacce mgn ce Wannan?"
Saratu tace,
"Ina Tabbatar Miki Ayau dinnan Alhaji Abdullahi Omar Mai fata zai shigo kasar Nan"
Nas ta zabura da sauri tace,
"ki rantse?"
Saratu tace,
"Wlh dgske nake ke na karkare Miki zance ma cikin sirri yakeson shigowa driver kadai zaije dauko sa haka dai uwar gidan ke gayamin, shiyasa duk hankali na ya tashi matukar bamu dakatar da Shirin Maru ba to tabbas Babu ja da baya mlm sale saiya Tona Mana Asiri Kuma kiyi tunani gashi Uban gayyar Yana tafe kinsan kuwa zamu fuskanci babban hukunci matukar Abinda ke boye ya fito fili"
Nas tace,
"Na gaji da boye-boyen Nan da ake Saratu"
a rude Saratu tace,
"me kike nufi?"
Nas ta Mike tsaye tana zarya hannun ta a baya tana nazari can tace,
"Dole mu fara zubar da jini"
Wata irin wawiyar ajiyar zuciya Saratu tayi hankalin ta na kwanciya dan da duk zaton ta Nas zata zare hannun ta ne, kallon ta Nas tayi sai kawai ta kwashe da dariya tace,
"zaton ki Zan barki? Haba Inaa ai Wlh matukar Ina numfashi saina kunsawa Hajia Aisha takaicin dazai kaita har lahira ke nifa na tsani matar Nan tsana ta Inna naha."
Saratu na dariya tace,
"toh wanne irin zubar da jini zamuyi?"
Nas tace,
"lkci yyi da Hajia Aisha zata fara dandarar zafi da takaicin duniya, Ayau dinnan zamu sa a salwantar da Rayuwar Alhaji Abdullahi"
Saratu ta zaro ido tace,
"mutumin da yake da manyan security ta Yaya za'a kashe shi?"
Nas ta dubeta sosai kafin tace,
"kikace yau zai dawo?"
Saratu tace,
"Tabbas"
Nas tace,
"Tunda driver kadai zaizo daukar sa Kinga kenan za'a iya salwantar da Rayuwar sa cikin sauki, Dan haka zamu samu 'yan daba su duba Mana shi cikin sirri daga lkcin daya diro kasar su fara bibiyar sa har suje inda Babu kowa su aiwatar da aikin su"
Cikin jin Dadi kwarai Saratu tace,
"Wlh bakiji yadda hankalina ya fara kwanciya ba kice dab nake da naci moriyar Dana"
Murmushi Nas tayi kafin tace,
"Abu yaki ci yaki cinyewa gwara ayi musu kwaf daya a wuce wajen"
Saratu tace,
"kinyi tunani mekyau Wlh, yanzu kafin lkci ya kure Ina zamu samo 'yan daba?"
Dariya Nas ta kyalkyale dashi kafin tace,
"kece bakinsan Kan garin ba tunda kikaga na kawo zancen ai kinsan akwai dahir"
"Wannan haka yake"
Saratu ta fada tana washe baki kafin tace,
"mgnr mlm sale fa?"
Nas tace,
Naso shima a kashe shi Ayau Amma sbd kawar da zargi kawai zamu koma gun boka ne yanzu asan abin yi akansa."
"Dakyau ta wajena"
Saratu ta furta cikin jin Dadi kwarai, bada Bata wani lkci ba Nas tayi Kiran ogan 'yan daba, ta sanar masa da bukatar ta, Ogan 'yan daba ya Tabbatar Mata da kartaji komai kamar an kashe Alhaji Abdullahi an gama saidai suji lbrn mutuwar sa, Koda sukaji haka murna ta kamasu kwarai Dan haka Nas itama ta shirya Dan komawa gun boka Akan mgnr mlm sale.
######
Cikin Sanda Meera ta fito daga parlon su, Mom Ashe harta fice Dad be dawo daga tafiyar da yyi ba, Dan haka a fili tace,
"Babu Dan iskan daya Isa ya hanani zuwa yanzu"
cikin sauri ta nufi gate dinsu fatan ta shine kawai ta samu Dr. Omar, zuwanta bakin gate keda wuya kawai taga sabon fuska Bata ga me gadinsu ba, Bata kula da hakan ba Dan Bata cikin hayyacin ta kawai taje zata bude kofa taga an Dora Mata dalma(bingiga) a hannu a firgice ta sake kallon mutumin, Fuska a hade yace,
"kina bude kofar Nan Zan harbe hannun ki"
Da sauri ta cire hannun bakinta na rawa tace,
"Kai waye? Ina mlm Shehu? (Me gadin su)"
ta furta hakan tana waige2 Tabe baki yyi yace,
"koma ciki lkcin karar ku beyi ba Dan haka bazaki fita ba ko kin manta da dokar da Sageer ya saka Miki?"
Sai yanzu ta fahimci lalle Sageer ba karamin daurin takunkumi yyi Mata ba, kwallar bakin ciki ne ta cika Mata Ido Dan haka kawai ta juya zuwa parlon su.