Sashe 75
Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta: 65-70 a suratu Dhaha, za'a karanta su, sai a tofa a ruwan da aka zuba ganyen magarya guda bakwai, sannan a yi wanka da shi, Insha Allahu aka jimanci Wannan mgnin da izinin Allah za'a samu waraka, Me tmbyr yace Toh Masha Allah duka-duka Anan muka kawo karshen Amsa tambayoyin mu sai Kuma me kowa me komai ya Kara nuna Mana wani lkcn, cikin tsananin farinciki Meera ta sake karanta Abinda ta rubuce kaf akan takardar kafin ta zari katon hijab dinta ta saka batare da tunanin komai ba tayi waje duk murna ta Kama ta, bangaren da Abba yake taje Nan ta tarad baya daki Nan ta fara dubansa can ta hango shi tare da mlm habu a bakin gate, da sauri ta Isa wajen bakinta a washe, Abba na ganin ta ya fara fara'a Kamar koyaushe, mlm habu yace sannu Hajia kina bukatar wani Abu ne? Meera data karaso yanzu tace Abba Insha Allahu ciwon ka yazo karshe, da mmki suka zuba mata Ido mlm habu yace kin samo mgnin ne? Shi Kuma Abba ba bakin mgn bare yace wani Abu sai kallon ta yake d takarda a hannu, bakin Meera yaki rufuwa ta fara nunawa Abba rubutun da tayi kamar Wanda Shidin zai fahimcin Abinda aka rubuta tace kalli Abba yanzun Nan na Gama rubuta Ayoyin da ake amfani dasu wajen karya Sihiri, kallon ta Abba yyi da sauri Meera Tace eh Abba anan sunnah TV naji wani mlmi na wa'azi ta Fadi wa'annan Ayoyin tayi mgnr tana karanta Abinda mlmin yace Tace Insha Allahu zamu gwada maka shi Abba da izinin Allah zaka samu bakin mgn ta karasa mgnr bakinta na rawa sbd mugun tausayin Abban da take gaba1 idonta cikowa yake da ruwa, mlm habu yace Kai Masha Allah gsky hajiya Allah ya saka Miki da Alkhairi Allah Kuma ya dafa Miki bisa kokarin aikin Nan da Kika dauko, kallon sa Meera tayi tana kokarin maida kwallar data taho Mata Tace saidai mlm habu bansan inda zan samu ganyen magaryar ba sonsamu ma na samu danyen ba Wanda ya bushe ba wato ba irin na kasuwa ba, mlm habu yace Abu me sauki? Nan Nan kauyen mu idan naje zan tsinko miki shi dayawa gashi Nan a hanyar garinmu Kamar banza, Da fara'a Meera Tace Toh Amma har sai yaushe za'a samu? Inason Abba ya samu lpy d wuri, Mlm habu yace karki damu Hajia zansa yarona yau dinnan ya kawo ganyen Nan domin ki fara aikin ki da wuri, da murna Tace Nagode mlm habu, mlm habu yace haba ai yiwa kaine Alllah ya bashi lpy, Ameen Meera ta furta hakan tana kallon Abba, Abba tun dazu share kwallar murna yake ya rasa bakin mgnr da zaiyiwa Meera godiya, Allah ya amsa Addu'ar sa tun ranar da Saratu ta juyar da tunanin su Dr. Omar akan neman mgnin Abba yake rokon Allah ya bashi lpy, ya kawo wata silar dazai wargaza Alqadarin Saratu, Kallon sa take da tausayi tace Dan Allah Abba ka daina zubar da hawayen ka Insha Allahu zaka sami lpy, kallon ta yake da murmushi Yana girgiza kansa so yake ya fada mata kukan Dadi yake bana bakin ciki ba, Saida ya share hawayen nasa Tass kafin tabar wajen tanaji a ranta Insha Allahu Nan da wani lkci Abban zai warke shima ya fara mgn. Yamma liss Dr. Omar ya dawo gidan a bakin gate ya tarad da Abba tare da mlm habu, be karasa da motar sa gun parking ba ya tsayar ta kafin ya fito daga ciki, wajensu ya nufa suka tarbe shi da fara'a, Dr. Omar da murmushi yace Abba hutawa ake Anan? Abba ya girgiza kansa bakinsa a washe yanaso ya bawa Omar lbrn Abinda ya faru dazu Babu damar mgn, mlm habu ne yace ai yallabai dazun Nan hajiya tazo Nan da fara'ar ta, da sauri Dr. Omar ya dubeshi bece komai ba Yana jiran Karin bayani, Mlm habu yaci gaba da mgn yace Da murnar ta tazo nan Tace ta samo Ayoyin da ake amfani dasu Dan karya Sihiri, wani irin sarawa Kan Dr. Omar yyi ya dafe goshin sa da sauri ba komai ya sashi Jin hakan ba sai tunowa da Kamar yyi irin kaman cacceniyar mgnr Nan a baya take Kuma ya manta, Batare da mlm habu ya fahimci halin daya shiga ba Nan ya fara feso Masa bayani, kallon Abba Dr. Omar yyi yaga fara'ar sa ta karu, shima samun kansa yyi dajin dadin abinda za'ayiwa Abban, suna Nan sukaji sallama daga waje, lekawa mlm habu yyi yaga Ashe yaron sa ne yace shigowa Mana Musa, shigowa Dan samarin yaron yyi ya gaishe su kafin ya Mika Ledar hannun sa yace ga sakon baba, karba mlm habu yyi yace yauwa Musa Allah yyi Albarka Ameen Musa ya Amsa da murmushi, kallon su mlm habu yyi Yana mikawa Dr. Omar Ledar dake cike da ganyen magarya yace ga Wannan dashi Hajia zatayi amfani saika Bata idan ka Shiga ciki, karba Omar yyi Yana juya Ledar hannun nasa, mlm habu yace ganyen magarya ne, Dan murmushi Dr. Omar yyi yasa hannu ya debo kudi ya mikawa Musa, kin karba Musa yyi Saida Abba yyi Masa Alamar daya karba kafin ya karba din sannan yyi musu sallama ya tafi, Dr. Omar ma sallamar yyi musu ya nufi cikin gidan bayan ya gyara parking din motar sa, Yana Shiga ciki kuwa Meera na zaune a parlo tayi shiru ta fada tunani ba komai take tunawa ba sai Dad dinta, Tabbas a yadda taji wa'azin mlmin Nan ya Fadi Abubuwa da yawa na alamomin Wanda aka yiwa Sihiri da tayi dogon nazari ta fahimci tabbas Dad dinta Yana daya daga cikin Wanda aka lissafo shima, tunani take Taya zata taima Masa? Yanzu me yakamata tayi Dan ceto Dad dinta daga hannun mugaye da yake ciki? Ji tayi an bugi kujerar da take zaune a firgice ta dawo daga duniyar tunanin data Lula idonta ne ya sauka Kan Dr. Omar da tun dazu yake tsaye kanta duk mmkin Wannan dogon tunanin data tafi yake, Meera ce tayi azamar janye nata idanun tana kawar da kanta da sauri bakinta na rawa Tace Ashe ka dawo sannu, tayi mgnr tana gyara zaman ta, Shiru taji yyi beyi mgn ba hakan yasa ta juyo ta kalleshi, ga mmkinta taga still itan yake kallo, wara ido tayi Tace Ya Omar? Gani tayi ya tabe baki Yana zagayowa Kan kujerar ya tsareta da Ido sosai yace kalleki duka2 baki wuce 18yrs da wani Abu ba yarinya dake Sharaf wacce Ba'a Dade da Gama goyonta ba kila ko kirgen dangi baki Gama ba Kika zauna Anan harda fadawa tunani kamar wata babbar mace me Yara Ashirin, dubansa tayi d mmki tace Ya Omar? Cikin tsare gira yace fadamin tunanin me kike? Girgiza Kai Meera tayi Tace ba komai, yatsina fuska yyi Yana aje Ledar hannun sa yace ga sakon ki inji mlm habu, karba tayi da sauri tana Buda Ledar Tace Alhamdulillah Insha Allahu komai ya kusa zuwa karshe tayi mgnr da fara'a sosai Kan fuskar ta, kallon ta yyi yace me Zaki dashi? Nan Meera ta fada Masa komai akan Ayoyin balla Sihiri, Girgiza Kai yyi yace Good Allah ya taimaka, Ameen Meera ta furta da fara'a tana kokarin tashi daga wajen kafin ta wuce dakinta, tashi shima yyi ya wuce can sama Dan rage kaya. Washe garin ranar Meera na parlo da azahar lkcn ta Gama girkin Rana taga shigowar Dr. Omar da saurin sa ya wuce sama, bin sa da kallon mmki tayi ta leka can kofar waje taga be shigo da motar sa ba, Abba ma baya bakin gate da alama da yyi Sallah dakinsa ya wuce, Meera na tsaye tsakiyar parlon tana nazarin Abinda ya dawo da Dr. Omar da Rana Haka ta hango shi daga can sama Yana taku da hanzarin sa ya canja kaya zuwa wasu bakaken kananan kaya d facing cap hade da mask daidai zai wuce ta gabanta da sauri ta Isa wajen sa tace ya Omar, ko kallon ta beyi ba yyi haramar fita da sauri Yana duba agogon hannun sa, da mugun mmki ta sake bin bayansa daidai zai bude kofa ya juyo Yana kallon ta ransa a hade yace kada ki soma sanar da Abba nazo na fita kin gane? Girgiza Kai Meera tayi a tsorace ta kasa mgn, Juya fuskar sa yyi yaci gaba da tafiya Yana Isa gaban gate mlm habu ya bude Masa kofa ya fita Yana Masa fatan nasara, fitar sa keda wuya Ashe a kofar gida yyi parking motar sa kawai ya shige cikinta ya Bata wuta a tamanin kafin wani lkci harya bace a unguwar Kamar walkiya, Sosai ya dinga ratsar shortcut harya cimma layin da yake kokarin Hawa, a hankali yake bin bayansu a fisge Kamar ba Dan su din yake tafiya ba, Motar su Sageer ne sbd haushi ma Sageer yace da kansa yakeson Harbin prof Aliyu sbd ya bashi gardama a department, prof Aliyu dake tafiya a nutse Sam besan da Ana binsa ba dake hanyar da zata kaishi gida tana Dan wajen gari yasa su Sageer suka samu damar binsa suna jiran ya Shiga lungun da zasu kashe shi batare da an fahimce su ba, Sageer shine me driving din sai Faisal a gefensa, wasu yaransa biyu a Bayan motar a takaice dai su hudu ne a ciki Daidai wani Shan kwana Sageer ya zaro Bindigar dake ajiye gefensa ya rike dayan hannun sa da steering dayan Kuma ya fiddo dashi waje cikin salo na mugunta ya saita gun din Kan tayar motar prof ta gaba Yana Shirin harbin wajen yaji harbi ya daki hannunsa, cikin wata irin kururuwar azaba Sageer ya saki gun din hannun nasa Yana me sakin Kan motar gaba1 sai ihu yake azaba ta isheshi besan a wanne Hali yake ciki ba, karar ihun Sageer ita ta fargar da prof dake driving a gaba, rage gudun motar sa yyi Yana duban bayansa a hankali, take ya hango motar bayansa na layi Akan titi ita kadai, besan meke faruwa ba hakan yasa yyi kokarin dakatawa, Daidai lkcn Dr. Omar dake can nesa dasu ya Kara wayarsa a kunne Yana fadin hello Sadeeq turo su, Sadeeq dake dayan Bangaren