← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 128

Sashe 93

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Littafin kudi ne, domin Samun cmplt dinsa saiki turo da 200 ta Wannan Account din 0030202448 Nusaiba Mustapha Sterling Bank saiki turo da shaidar biya ta Wannan Number 09039118754 ko Katin MTN ta waccar number👆🏻* 8/15/20, 8:08 PM - Ummi Tandama: Dr. Omar ke ta zabga sauri bayan dawowar da daga masallaci duk hankalin sa Yana Kan Meera yazo Shiga gate kenan yaji an kwala Masa Kira, a mugun firgice ya waiga Yanason tantance shin gsky kunnen sa yaji Muryar data kirashi ko kuwa gizo ne? Da mugun mmki yake kallon Abba dake saukowa daga napep fuskar sa cike da murmushi ganin Dr. Omar din ya zama kamar gunki yasa shi fadin, "nine Nan na kiraka" ya karasa mgnr Yana sallamar me napep, take Dr. Omar ya Isa gaban Abba da sauri murna fal ransa ya Kama hannun Abba yace, "Alhamdulillah, Alhamdulillah Ala kulli halin Abba ka samu lpy, bakinka ya dawo, Oh ya Rabbi Thank you" ya jera maganganun cikin tsananin farinciki, Shima Abba cikin murnar yace, "kayi hakuri nazo a Wannan lkcn Toh Amma dole ce ta sani hakan domin hausawa na cewa da zafi2 akan bugi karfe.." "haba Abba Kuma Dan kazo yanzu meye laifi a ciki? Mu Shiga daga ciki" girgiza Kai Abba yyi yace, "aa inason mu gaisa da Ameera nasan idan taga na warke zatayi farinciki sosai kiramin ita" Tsam da ransa Dr. Omar yyi hankalin sa a mugun tashe da kunya a fahimci halin da meeran take yasan ta wahala kwarai bayason tayi tafiya Dan zata Kara wahala Amma bazai iya yiwa Abba musu ba, a fili yace, "Toh" yyi mgnr Yana Shirin Shiga gida.., har ya Kama kofa zai shige take Abba ya tuna muhimmin Abinda ke tafe dashi, gani yake idan ya sake barin Wannan damar be sanar da Dr. Omar gsky ba za'a sake samun matsala musamman dayasan yanzu Haka Saratu tana can zata sake hada wata masifar, hakan yasa d sauri yace, "Omar dawo" Juyowa Omar yyi da mmki Abba Yana murmushi yace, "kila ta koma bcci Koh? Kada mu takura mata, dawo kaidin akwai wata muhimmiyar mgnr da zamuyi" a boye Dr. Omar ya saki ajiyar zuciya Dan bayason kowa yasan meye matsalar sa tsakanin sa da Meera har Saiya daidaita komai, Dawowa yyi gaban Abba yace, "gani" Abba yyi shiru Yana kallon sa gaba1 Fuskar sa ta canja zuwa yanayi na damuwa da Takaici, hakan yasa Dr. Omar yasha jinin jikinsa Haka kawai yaji zuciyar sa na harbawa da sauri, tunani Abba yake ya sanar Masa shi kadai ne ko kuwa yasashi gaba suje can gidan da Saratu ke Aikatau ya fada musu a tare? "Abba kayi shiru" Dr. Omar ya katse Masa tunanin da yake, sauke ajiyar zuciya Abba yyi kafin yace, "dauko motar ka akwai Inda zamu" A rude Dr. Omar yace, "Meera fah???" Ya Fadi hakan cikin subutar baki dan gaba1 hankalin sa fiye da rabi Yana wajenta, wara ido sosai Abba yyi da mmki yace, "kodai Bata da lpy ne Omar?" Girgiza Kai yyi da sauri bakinsa na rawa yace, "eh..aa lpyr ta kalau Bari na dauko motar" ya Furta hakan da sauri Yana shigewa cikin gidan, binsa da kallon mmki Abba yyi Yana ganin kamar akwai Abinda ya Sami meeran tun daga yanayin reaction dinsa na farko dayace a kirata zuwa yanzu, Dr. Omar na shiga gidan ya wuce wajen motar tasa sbd yaji akwai key a jikinsa Daman tunda yaje dakinsa da Asuba ya dauko akan idan ya dawo masallaci zai dauki Meera zuwa prvt hsplt ya gani ko ya mata rauni ne, me gadi ne ya bude Masa gate din Yana daga ciki besan da zuwan Abba ba harya kulle gate din, Yana fita kuwa Abba ya shige motar Nan ya jata suka tafi, shiru motar tayi kowa da tunanin da yake, Abba na tunani da tausayin Yadda Dr. Omar zai dau abin shikuwa Dr. Omar na fatan ace ba wani daukan lkci zasuyi ba Dan Yana bukatar ganin Meera shiyasa ma yake ta tuki da sauri, Saida sukazo main road Dr. Omar yace, "Ina muka nufa Abba?" Abba yyi Masa bayanin unguwar da zasuje, girgiza Kai Dr. Omar yyi kafin ya maida hankalin sa Kan tuki, dukda safiya ce hakan be hanasu samun goslow ba hakan ya jawo musu delay kafin su samu Karasawa unguwar har 9am tayi, kallon unguwar Dukkansu suke yyinda Dr. Omar yake mmkin me Kuma zasuyi a Wannan unguwar? Dan daga yanayin unguwar kasan ta manyan mutane ce duba da yanayin gidajen Wannan Yana wane Wannan, har lkcn Abba beyi Masa mgn ba Saida sukazo saitin gidan dayafi kowanne girma da daukar hankali sbd kyawunsa yace, "dakata anan" tsayawa Dr. Omar yyi yace Masa su fita, Shidai Dr. Omar bin umarnin Abba kawai yake batare daya fahimci komai ba, bayan ya gyara parking dinsa ne suka nufi gate din dake gabansu, wasu security ne suka taso suna binsu da kallo kafin suce, "Kai suwaye ku?" Abba yace, "Dan Allah ko Alhaji Yana ciki?" Wani daga cikine yace, "da sassafen Nan Dan jaraba kabar mutum da iyalin sa man..." Kafin ya Gama rufe bakin nasa kuwa yaji an kwashe shi da Mari, a gigice kuwa ya rike Kumatu hankali tashe Yana kallon Dr. Omar dake tsaye cikin zafin zuciya, sauran security din ne suka taso hade da pointing Dr. Omar da guns dinsu, a rude Abba yace, "Dan Allah kuyi hakuri karkuyi Masa komai" yyi mgnr Yana kokarin hade hannayen sa da nufin roko Dr. Omar yyi saurin rikewa Rai bace yace, "Ina wajen kke kokarin Basu hakuri Abba? Allah ya sauwake Wai mema zamuyi anan inda ba'asan darajar mutane ba? Dan Allah mu tafi" ya Ida mgnr Yana Jan hannun Abba, kin motsi Abba yyi Yana kallon Dr. Omar cikin damuwa yace, "kayi hakuri Omar Amma ganin megidan Nan yanada matukar muhimmancin a garemu" baki sake Dr. Omar yake kallon Abba, yyinda sauran security din suka fara musu isgilanci suna fadin da gani rokar maka jari zaiyi idan hakane kuwa sai ku jira Nan da karfe daya tunda weekend ne Saiya fito Sallah, ran Dr. Omar ne ya Kara baci zaiyi mgn Abba ya dakatar dashi da fadin, "Dan Allah karkace komai da sannu zasu gane mutum daraja gareshi ko a Yaya yake" dariya suka fara musu sbd gani suke Kamar talauci yasa Abba ya nace su tsaya Dan a Basu taimako, shi kuwa Dr. Omar ji yake kamar ya bubbuge su ba damar hakan sbd Abba ya Hana, Abba Yaja hannun sa yace, "muje gefe mu jirashi" cikin matukar takaici Dr. Omar yace, "I don't know why Abba ka nace saimun tsaya a inda ake cin zarafin mu Kuma kace muyi hakuri bayan inada damar na saita musu hankali" girgiza Kai Abba yyi yace, "dama ai Manzon Allah S.a.w. yace muyi hakuri a inda muke da karfin ramawa shiyasa nakeso kayi hakurin" cije lips dinsa Dr. Omar yyi Yana shafa sumar kansa hade da lumshe ido Meera ce ta bayyana a idon nasa take ya bude idon da sauri hankalin sa a mugun tashe gsky zai tafi idan mutumin ya fito Saiya dawo bazai iya jurewa ba da Wannan tunanin ya dubi Abba zaiyi mgn kenan Sukaji an bude gate, da murna Abba yace, "Alhamdulillah kaga ma ya fito muje" yyi mgnr Yana nuna bayan Omar dake ya juyawa gate din baya Juyawa Dr. Omar yyi Yanason ganin Wanda Abba Ke nuna Masa yyi Arba da Alhaji Abdullahi, da mugun mmki Dr. Omar yace, "Abba ka sanshi ne? Meye hadinku dashi?" Ya karasa mgnr Yana sake waigawa daidai lkcn Alhaji Abdullahi ya dubesu shima take ya cika da mmkin ganin Dr. Omar kofar gidansa, nufar su yyi da sauri fuskar sa a sake yace, "Omar Kaine? Meyasa baka kirani na fito ba?" Ya karasa mgnr Yana Ida zuwa wajensu, yanzu Kuma mmki ne ya Kama Abba sosai Saiya koma kallon Alhji Abdullahi da Dr. Omar, kawar da nasa mmkin Dr. Omar yyi Yana shafa sumar kansa yace, "I'm sorry daddy" daddy ya Mika Masa hannu sukayi musabaha zuciyar sa fari Tass yace, "gsky kamin zuwan bazata Kuma naji Dadi ainun dama kullum burina kenan naga kazo" Sunkuyar da kansa Dr. Omar yyi duk kunya ta Kama shi ya tuna yadda Alhji ke Masa tayin zuwa shikuma yyita zamewa sbd bayason Abinda zai sashi rikici da masu kudi, sai a lkcn Abba da daddy sukayi musabaha daddy yace, "Masha Allah ku shigo ciki" Abba ya gyada Kai tamkar kadangare duk mmkin sanayyar su yake, Sam Alhji Abdullahi be kawo komai a ransa ba Shidai kawai ya amshe su a Matsayin baki Kuma masu muhimmancin Nan yyi gaba suka bishi a baya, direct parlon baki yyi dasu, suna shiga kuwa motar Sageer ta sharo gidan a guje har Yana tada Kura. Bayan sun zauna ne daddy yace, "abin mmki Taya ka samu Address din gidana?" Shiru Dr. Omar yyi Yana Sunkuyar dakai Abba yyi saurin saka baki da fadin, "mgnr gsky Alhaji nine Nan na kawo shi bawai Dan yasan gidanka bane" kallon sa daddy yyi d mmki yanaso yasan Toh Ina ya sanshi? Saidai duk tunanin sa ya manta, Abba yaci gaba da fadin, "wata muhimmiyar mgn ce ta kawo ni Nan, saidai inaso duk kuyiwa zancen nawa kyakkyawar fahimta" yanzu Kam harda Dr. Omar yake kallon Abba duk ya Matsu yaji wacce irin mgn ce Wannan? "Ikon Allah bawan Allah wacce irin mgnce Haka daka zabi ka hadamu waje guda muyi?" Murmushin takaici Abba yyi yanajin zuciyar sa na rawa yace, "Bayan ku biyun ma idan da son samu ne ace duka Ahalin gidan Nan suna Nan" yanzu Kam gaba1 kansu ne ya kulle Dr. Omar yace, "Abba tun da Allah ya baka lpy naji Kanata min mgnr da Sam ban fahimta ba, dama kasan shi ne? Meye dalilin Wannan taramun da kke? Meyasa ka zabi muzo Nan? Bayan tun d can bamu taba zuwa ba?" Girgiza Kai Abba yyi cikin yanayin tausayawa yace, "dama ya za'ayi ka samu zuwa Nan Omar? Nima bansan zan kawo ka Nan din ba Saida dalili me girma ya jawo hakan" daddy ne Yaja ajiyar zuciya yace, "shikenan Bari na Kira su" Nan ya Mike ya fice a parlon, Kallon sa Dr. Omar yyi yace, "Abba Dan Allah
Chapter 93 · 0% Book details