← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 128

Sashe 50

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

daddy ne yace, "ai indai Safna ce yadda kasan parrot Haka take ai anyi maka ma da sauki" daddy ya Furta Yana dariya shima, Dr. Omar Yana dubansu dukkansu yaji wani irin nutsuwa ta Kama shi ji yake kamar irin family dinnan an hadu Ana Raha, Dan Haka da 'yar dariya shima yace, "yeah I see, so ya mummy?" Ya tmby Yana tsareta da ido, Safna da murna ganin ya fara sakewa da ita tace, "Mummy tana lpy, tace ma a gaishe ka, yaushe zaka Zo gidan mu?" Ware Ido sosai Dr. Omar yyi Yana kallon ta da mmki still murmushin be bar fuskar sa ba, tashi daddy yyi Yana dariya yace, "ah Toh kadai gani Bari na Amsa waya" yyi mgnr Yana barinsu a wajen hade da Kara wayarsa kunne ya fita, Kame bakinta Safna tayi da sauri tana Dan zaro Ido tace, "Sorry Yaya" dariya ce ta Kama Dr. Omar yace, "kamata yyi a kiraki da parrot ba Safna ba" rufe Ido Safna tayi tace, "na daina fa" Dr. Omar yace, "okay nuna min picture din mummy" dauko wayarta a jaka tayi da hanzarin ta ta duba gallery dinta duk hotunan family din gidan ne harda su Hajjaju, Mika masa wayar tayi tace, "gashi duk mune a ciki" karba Dr. Omar yyi Yana murmushi sbd yarintar ta, da hoton ta ya fara cin Karo Yana matsawa kuwa yaci Karo Dana Mummy, Wani irin sarawa kirjinsa yyi sbd yadda yaji bugun kirjin kadan ya rage ya jefar Mata da wayar ta yyi ta maza ya rike, Safna dake kallon sa tace, "Ya Omar lpy?" Dagowa yyi Yana Dan yake yace, "No ba komi" yyi mgnr Yana sake kafe hoton mummy da Ido kamar wacce dama can ya santa, kasa janye hoton yyi yabar na mummy still Yana kallo, Safna ce ta katse shi da fadin, "ya Omar ka ganmu? Kaga Mummy Koh? Tana Kama Dani?" Tayi mgnr tana dariya, Dagowa yyi yaga suna Kama din Dan Haka yace, "Wannan ce Mummy?" Yyi mgnr Yana nuna Mata wayar, Safna tace, "eh itace ga kamar mu Nan kamar an tsaga Kara" kallon ta yyi ya sake kallon hoton yace, "mummy ta fiki kyau da alama yayanku ne ya dauko kyawun ta" ware Ido Safna tayi kafin ta kwashe da dariya, kallon ta yyi da mmki bece komai ba, Safna na dariya tace, "Toh Wlh gwara ni, Hajjaju dai tace kila acan zuri'ar ta ta iyaye da kakanu karni na hamsin Yaya ya iyo Kama tacan" "karni na hamsin Kuma?" Safna tace, "kwarai kuwa Bari fa ka ganshi" tayi mgnr tana Mika hannu ya Bata wayar, Mika Mata wayar yyi ta karba zata duba kenan daddy ya shigo, Kallon su yyi gwanin sha'awa sun birgeshi yadda yagansu cikin fara'a sannan yace, "safna time din lecture dinku fah har kin kusa makara" dafe goshinta Safna tayi tace, "Wlh daddy harna sha'afa" Daddy yace, "yeah naga alama" ya Furta hakan Yana murmushi yace, "Omar zamu tafi sai tomorrow Zan shigo Insha Allah" tashi shima Omar yyi yace, "badan lecture ba da sai nace da wuri Haka?" Murmushi sukayi Masa Safna tace, "ai Ina Nan Zan dawo" daddy yace, "ki dawo ko ki hanashi aiki da surutun ki?" Dariya Safna tayi tace, "Kai daddy" daddy na dariyar shima yace, "ehmana" har jikin mota Dr. Omar ya raka su shima sai murmushi yake Dan sun birgeshi, Yana daga musu hannu suna daga Masa hannu da Haka suka rabu. A can bangaren Ameera kuwa sai wajen 12am ta Gama duk wani aiki na gida hatta farfajiyar gidan ma ta share tas Kai kace ba mutum dayace tayi aikin ba, ta gaji iya gajiya gabban ta sai ciwo suke a Haka ta samu ta sakarwa kanta ruwa anan cikin daya daga cikin dakunan dake kasa, tana Gama shirinta kuwa taga mota na shigowa gidan zaton ta ko Omar dinne ya dawo tana fitowa kuwa taga motar daukar kayace shake da kayan furnitures, Mutanen maza ne na wasu company da alama sun Saba d Kai Kaya ko'ina Dan Haka suna Gama sauke kayan sukace ta fito, fitowa tayi Nan taga suna Shiga da kayan kamar Wanda aka shirya dasu tuni sun Gama shirya komai na gidan Kama daga kujeru har kayan set na gado da sauran su, hatta kayan kallo ma Saida suka saka, abin dai gwanin kyau Dan tashi guda parlon ya fara daukar Ido kamar dakin amarya Koda yake amaryar ce #lol, Meera na waje suka Gama komai suka dawo suka gyara kamar Basu suka wargaza kwalaye da ledoji ba, Bayan sun kwashe komai sun shirya wajen sukayi Mata sallama suka tafi, Saida suka tafi Meera ta sauke ajiyar zuciya tana Kara karewa yanayin parlon kallo Ashe fa ita ko kayan daki ba'ayi Mata ba? Goge guntun hawayen ta tayi tace, "Shikenan Dad ka siyar min wulakanci a gidan mijina" Zuwa yanzu ta fara Jin yunwa Dan tun safe batayi breakfast ba, tunawa da guntun Naman data rage jiya tayi Dan Haka ta Mike da sauri ta Isa inda ta ajiye, budawa tayi duk Naman yyi Sanyi harya fara yaushi sbd an kunshe shi, Ba yadda ta iya sbd cikinta juyawa yake irin uwar aikin data ci dole 'ya'yan hanji su zazzage, Dan Haka ta zauna kan barandar ta fara cin Naman tana kora guntun fresh milk dinta a ranta Fadi take da alama Sadeeq yasan Abinda abokin sa ya shirya shiyasa yasai kazar Nan badan wai na bawa Dr. Omar ba Dan ga alama Nan har yazo ya tafi be bukaci sakon Sadeeq ba, da Wannan tunanin dai ta karasa cinye kazar da sauran fresh milk, tattare Ledar tayi ta watsa dustbin kafin ta dawo ta zauna zaman jiran tsammani. Sai around 5pm Dr. Omar ya shigo gidan Meera har yanzu tana bakin baranda taki zaman parlon Dan batasan inane mazaunin ta ba, tana kallon sa ya Gama parking ya fito, kawar da kanta tayi gefe sbd yadda take jin zuciyar ta na fisgar ta gareshi ji take kamar taje ta rungume shi, shi kuwa gogan fuskar Nan a hade take tamau ba Alamar fara'a, har inda take ya karaso ciki2 yyi Mata sallama, amsawa tayi a hankali tace, "sannu da dawowa" ko kallon inda take beyi ba ya tura kofar zai Shiga, harya Sanya kafarsa cikin parlon Kuma ya juyo Yana kallon ta, Cikin tsare gira yace, "me kikeyi zaune anan?" D mmki ta dubeshi tace, "ina jiran wajen zaman da za'a bani ne" Dan tsaki Yaja Yana kawar dakai yace, "jeki Bayan boot Dina ki kwaso Kaya a ciki Ina jiranki a parlo" "Okay" Ameera ta Furta hakan tana mikewa tsaye, yyinda shi Kuma Ya Sanya kansa cikin parlon. Dakyar ta iya Ciro ledojin dake ciki Wanda bazata iyaba kuma ta barshi, tana zuwa da kayan hannun nata ta tarar dashi zaune Kan kujera ya kwanta harda lumshe ido Yana shakar iskar dake ratsa jikinsa, Bata ce Masa komai ba tazo gabansa zata ajiye taji yace, "bakya amfani da brain dinki ne?" Meera ta dago ta kalle still idonsa a rufe, katse Mata kallon nasa yyi da fadin, "Dallah wuce kikai kitchen" jikinta na rawa Tace, "I'm sorry" ta Furta hakan tana wucewa kitchen, wani mugun tsaki ya sake ja Yana me juyawa dayan barin, Haka dai Ameera taci gaba da kwaso kayan mota harta Gama, Bayan ta Gama ne ta Isa gabansa lkcn yana canja channel tayi gyaran murya kafin tace, "na Gama saidai akwai wasu buhun da bazan iya dauka ba" kallon ta yyi ya watsar bece komai ba, hakan yasa Meera ta tashi zata fice, "Keee.." ya Furta hakan da tsawa juyowa tayi a rude, Ashe ma ba ita yake kallo ba Amma taji yace, "ki kwashe kayan ki dake bakin kofar Nan ki kaishi daya daga cikin dakunan dake kasan Nan" "Okay" Meera ta Furta hakan tare d juyawa da sauri, kinkimo akwatin ta tayi ta wuce Nan ta zabi daki daya kafin ta Shiga da Bismillah tana Addu'ar Allah ya sada ta da Alkhairin dake cikin dakin yyi Mata tsari da sharrin dake cikin dakin. Tana Gama shirya 'yan kayanta a wardrobe kenan taji Yana kwala Mata Kira Dan Haka ta fito da hanzarin ta, Kallon ta yyi na wulakanci yace, "kwanciyar kikayi?" Girgiza Kai Meera tayi sai Kuma da sauri tace, "No na shirya kayana ne" tabe baki Dr. Omar yyi Yana kallon ta Cikin mugunta yace, "Inason kafin Sallar Isha kimin sakwara da miyar egusi ki Tabbatar dukkansu suyi kyau suyi Dadi kin gane?" Zaro Ido Meera tayi tace, "da Daren Nan?" A wulakance yace, "kin manta Matsayin ki a gidan Nan ne?" "A'a" Meera ta furta, "Good Dan Haka banason duk wani Abu dazai kawo cikas, ki lura sosai duk Abinda yyi karanci ko yyi yawa kamar Maggi ko gishiri Zaki fuskanci hukuncin me tsauri" a sanyaye Meera tace, "toh" Dr. Omar yace, "again" Meera ta zuba Masa ido Tama kasa Furta komai, kawar da kansa yyi yace, "akwai ganda cikin kayan Dana kawo itama inaso najita cikin miyar egusi" da sauri Meera tace, "har yaushe gandan ya dahu kafin Sallar Isha?" Tayi mgnr tana kallon agogon parlon da aka manna yanzu ma shida befi sauran mintuna ba ayi magrib sannan Isha, Tabe baki yyi Yana kwasar keys dinsa batare daya kalleta ba yace, "Wannan Kuma ruwanki" ya Furta hakan Yana me taka stairs, Binsa Da kallo Meera tayi a sanyaye tana me share wata siririyar kwalla data sirnano Mata. 8/15/20, 8:04 PM - Ummi Tandama: *YADDA ZAKI BIYA*
Chapter 50 · 0% Book details