Sashe 17
Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kai Masha Allah kayi Mata zabi mekyau kuwa kaga kenan abun bazai ja lkci ba tunda a shirye yake"
"kwarai kuwa"
Dad ya furta Yana murmushi, Itama murmushin tayi Amma na munafurci tana kissima yadda take shiryawa Ameera mugunta.
°°°°°°°°°
A bangaren Dr Omar kuwa koda suka koma tun daga bakin kofar gida ake musu sannu har suka Shiga gidan Amma da kowa yaji yadda abin ya juye sai ahau sallallami Ana tausayawa mlm sale, Ba kowa ke Basu lbrn ba sai Saratu Bata gajiya da fadawa mutane mlm sale baya mgn, abin na yiwa Dr. Omar ciwo Amma Babu halin ya nuna Mata hakan Dan shi bega dalilin da zaisa tayita yadawa ba kamar abin be dameta ba, oho ko a kwalar rigarta haka taci gaba da harkokin ta na gida.
Da sassafe kuwa Saratu ta shirya da nufin zuwa gidan Aikatau din ta, Dr. Omar na tare da mlm sale a daki ya kalleta lkcn tazo dakin tace,
"Maru idan Sahabatu ta dawo kace basai tayi abincin dare ba Zan taho dashi"
Maru ya kalleta da mmki, kasa shiru yyi yace,
"ummah nace jikin Abba fah?"
Saratu ta wurgo Masa Harara tace,
"toh Dadi uba so kke ka nunamin bansan meye tausayi ba? Inace tun jiya nake tare dashi har kawo yanzu? Shikenan a gindinsa Zan tare bazan nemi na Kaina ba?"
Girgiza Kai Omar yyi yace,
"kiyi hakuri ba nufina kenan ba"
"Mtwsss..."
Saratu taja tsaki tace,
"Kai ka sani kowa ya sani mlm bazai iya mgn ba Toh me ya rage ayi Masa? Kaima lalaci da Rashin sanin darajar nema yasa ka zauna har yanzu baka fita ba Banda haka me zakaji agun Wanda dashi da dutse duk daya?"
Rai bace ya dago Yana kallon umman zuciyar sa na suya Yana dannewa Tabbas Wannan mgnr da aka fada kan mahaifin sa badan Allah yasa Umma bace Babu me hanashi yiwa mutumin dukar fitar hankali, huci kawai yake kasa-kasa batare da yace komai ba, a hankali mlm sale dake hawayen takaici ya lalumo hannun Dr. Omar ya fara matsa Masa a hankali yasan yaron Yana da zuciya sosai Amma Kan Saratu Yana hakuri matuka har tsoro yake kar watarana ya hadiyi zuciya kan Abinda take masa, Saratu kuwa na Gama balbalin masifar ta tawuce tabar gidan.
Shiru dakin ya dauka idon Dr. Omar yyi Jajir shi gaba daya gani yake baida sa'a a Rayuwar sa, dukda zurfin ciki irin nasa yakan kasance cikin Nishadi da walwala aduk lkcn da suke Hira da mlm sale toh Dan farinciki ma dayake ji babushi yanzu sai zaman kurame, hawayen da yake gani fuskar mlm salen ba karamin daga Masa hankali yake ba Dole ya fita Dan neman Masa mgni bazai iya jurar kallon sa cikin Wannan halin ba,
Dan gyaran murya yyi ya kalli mlm sale, mlm sale yyi murmushi Dan zuwa lkcn ya goge hawayen fuskar sa ya kalli Dr. Omar din ya girgiza Kai, Dr. Omar ya fara mgn cikin nutsuwa yace,
"Abba kayi hakuri da duk Abubuwan da suke faruwa, sannan inaso ka rungumi Abinda ya sameka a Matsayin kaddara Insha Allahu zaka samu sauki duk inda mgnin yake zanyi kokari na Nemo maka shi Insha Allahu kada halin da kke ciki ya saka a damuwa ko wani halin muna tare dakai Babu Abinda zai faru d izinin Allah"
murmushi me ciwo Abba yyi a ransa Fadi yake ni na dace na Gaya maka Wannan kalaman Omar, Wannan kalaman dakai sukafi cancanta Omar, Kaine ya dace a tausayawa Omar, Rayuwar ka na cikin garari Omar, Omar da gatan ka, Omar Kai ba karamin mutum bane, inama inada yadda zanyi kaji zantukan zuciyata Omar?
Mlm sale ya karasa mgnr a ransa yanajin zafi da kuncin halin da yake ciki, a fili kuwa Dr. Omar saidai yaga mlm sale Yana murmushi da hawaye zaton sa yanajin dadin tausar zuciyar sa da yake ne besan cewa murmushi me ciwo mlm sale yake ba. Kusan dai Dr. Omar shiya kasance da mlm sale a Wannan ranar, saidai Dr. Omar yyita zance shi kadai mlm sale na murmushin takaicin halin daya samu kansa silar matarsa Saratu.
*****
A bangaren Ameera kuwa yadda taga rana haka taga dare gaba1 hankalin ta a mugun tashe yake sbd yadda mom tazo ta Tabbatar Mata yadda sukayi da dad kenan aure Babu fashi, babban bacin ranta kuwa yadda su Anty Jamila suke ta Mata dariya suna siffanto yanayin Alhji buba sai taji tamkar duniyar ta juye Mata a haka sukayi bcci suka barta hakan ya Bata damar tashi cikin dare tana kaiwa Allah kukanta.
Washe gari kuwa Ameera naji na gani taga su Anty shafa suka tafi makaranta tsabar Basu damu da kr2n ba ko files din nasu Basu dauka ba haka suka tafi,
Dad yyiwa Alhji buba mgnr Ameera kamar kuwa dama jira yake take ya amince yace idan Babu damuwa zaizo da yamma dad yace sai yazo, mom tana gida haka tayi ta sa Ameera aiki da gyare2 gaba1 sai Ameeran ta fita hayyacin ta, toh dama ba cikin kwanciyar hankali take ba wani tashin hankali ya sake samunta duk sai ta birkice kamar figaggiyar kaza.
*****
A bangaren Sageer kuwa ya Dade Yana takaicin cizon Meera a hannun sa, a Jima ya duba karshe ya Kira mutanen sa ya Tabbatar musu da su fara sawa Meera ido Dan gani yake idan be kekketata ba bazai huce ba Sam. Washe garin ranar kuwa da wuri zugar motocin nasa sukayi convoy zuwa B.U.K, suna barin gidan Saratu na zuwa sai kurar wucewar su ta gani, washe baki tayi tace,
"Dana kenan kanajin dadinka Nima dab nake da a dangwali Arzikin Nan Dani"
tayi mgnr tana shigewa cikin gidan itama.
••••�
Dr. Omar na Shirin zama Bayan ya Gama shirya mlm sale da safe mlm Sale ya riko hannun sa, Dr. Omar yace,
"da mgn?"
Mlm sale ya girgiza Kai, Dr. Omar ya zuba Masa ido yace,
"toh Abba Inajin ka"
mlm sale yyi murmushi ya tashi tsaye hade da riko hannun sa suka fito, binsa kawai Dr. Omar yyi Yana jira yaga me yake nufi, sai gani yyi sun nufi dakinsa, Laptop dinsa ya dauko ya bashi yyi alama da hannunsa zuwa waje sannan ya girgiza Kai, Dr. Omar da sharp brain dinsa ya hango Abinda yake nufi yace,
"Wai na tafi hospital?"
Mlm sale ya girgiza Kai Yana washe baki, Dan murmushi Dr. Omar yyi Yana girgiza Kai yace,
"Abba ai ni Ina Nan tare dakai Zan dinga tayaka Hira"
mlm sale ya fara Girgiza Kai Yana hade fuska ya nuna kirjinsa da hannunsa sannan ya nuna bakin kofa Yana kallon Dr. Omar, Dr. Omar ya lumshe ido Yana shafa sumar kansa tabbas ya fahimci me Abba yake nufi wato idan ya Isa dashi toh ya tafi hospital din kenan, bazai iya musu da Abban ba Kawai yace,
"toh shikenan Abba duk yadda kace hakan za'ai"
Murmushi Abba yyi Yana Dan bubbuga kafadar Dr. Omar din, shima murmushin Dr. Omar yyi kafin ya karbi jakar laptop din nasa, sallama yyiwa Abba ya tafi dama cikin shirinsa yake tsaf, Yana dagawa Abban hannu harya bar gidan Bayan ya rufo kofa.
Tsaye Abba yyi Yana goge hawayen dayake ta rikewa tun dazu, shi gaba1 tausayin Dr Omar din yake, ya rasa dame zai taimaka masa ya gano asalin sa, Addu'a ya fara yi a ransa Yana fatan Allah ya kawo wata mafitar dazai tona Asirin Saratu.
8/15/20, 8:01 PM - Ummi Tandama: *ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA...ðŸ“*
( _Ko Ana Muzuru Ana Shaho Sai yayi_)
Na
*Nuceeyluv😘*
12...
Kamar yadda Alhji buba yace hakan ce ta faru da yamma sai gashi cikin gidan su Meera yazo ganin ta, Meera na daki ta hada Kai da gwiwa sai kuka take ta rasa inda zata dura ranta taji Sanyi,
"Ke taso Yana jiranki a parlon baki"
Taji muryar mom ta daki dodon kunnen ta, a tsorace ta dago tana kallon mom tace,
"Dan Allah kuce ya tafi Wlh bana sonsa"
mom ta saki wata muguwar dariya tana tafi tace,
"Au Ashe? Lallefa 'yarnan wuyanki ya Isa yanka kin tashi a wajen Nan kuwa ko saina zo na harbe ki da kafa?"
Ta karasa mgnr cikin tsawa, jiki na rawa Meera ta tashi tana jawo hijab dinta zata saka Kan doguwar rigar ta, da sauri mom ta fisge hijab din tana kallon jikin meera yadda rigar tabi ta lafe jikin meeran sai ya fito da shape dinta karara tsaki Mom taja Dan tun ba yauba itama takejin haushin Kirar Meera da ace 'yarta ce ba karamin jari zatayi da ita ba, wani siririn gyale data gani Kan gado ta Miko Mata tace,
"karbi Wannan Zaki sa"
Zaro ido Ameera tayi tace,
"kiyi hakuri mom bazan iya sawa ba"
mom ta wurgo Mata Harara a tsawace tace,
"Kin saka ko saina watsa Miki Mari yanzu?"
Ta karasa mgnr tana zaro ido, karba Meera tayi da sauri jikinta na Bari, dakyar ya rufe Mata jelar gashinta haka ma dai Saida gashin ya fito ta baya sbd tsawon d yake da shi kallon kanta tayi ko mazaunan ta ma besan da zaman gyalen ba ko Ina na jikinta ya manne da rigar, ta dago a hankali da nufin ta roki mom ko zata barta sai kuma taga an bita da mugun kallo, haka ta hadiye mgnr Tata tayi hanyar kofa, tsaki Mom ta sake ja tabi bayanta itama, a parlo mom ta Mika Mata Tray me cike da snacks da drinks Akan takai masa har bakin kofar parlon bakin mom taje Saida ta Tabbatar Meera ta Shiga sannan ta juya duk Wannan Abubuwan mom tanayi ne sbd tasan halin Alhji buba akwai sakin hannu, haka taci gaba da harkokin ta tana dariyar mugunta lokaci zuwa lkci, Koda Meera ta Shiga parlon bakin kasa motsawa tayi daga jikin kofar,