Sashe 61
Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read
shiru Abba yyi yanajin takaicin Saratu kwarai, tunowa da jiya da safe yyi har gabansa tazo tace, "duk wani me bakinciki daci gabana dai saidai ya mutu domin yau dinnan Shirin Nan daka ga nayi na bikin Dana ne Sageer Nan da sati biyu za'a daura shiyasa ma xan tare a gidan tun yau domin bikine za'ayi irin na masu shi, Dan ita kanta amaryar ubanta ba baya bane wajen naira burina Yana gab da cika suna Gama damka Masa komai zan fara zartar da hukuncin Dana dauka a kansu" ta karasa mgnr tana sakin dari hade da ci gaba da fadin, "su dunkum sai Ayita zaman shiru baki na wari Babu damar Fadar gsky kaji waliyyi" tayi mgnr cikin isgilanci tana dariyar keta a Haka ta kada bujenta tabar Masa gidan, Mlm sale yyi kunkan bakin ciki Daren jiya haryau da takaicin Saratu ya tashi a ransa..., Girgiza shi Dr. Omar yyi yace, "Dan Allah Abba" kallon Meera da tayi tagumi Abba yyi itama da sauri Tace, "Eh Abba Dan Allah ka taho muje" tayi mgnr Kamar zatayi kuka ita duk tausayin sa take, Girgiza Kai Abba yyi Alamar ya amince Dan Haka suka Mike da murnar su suna hada Masa kaya, kallon su Abba yake cikin birgewa yanajin dadin yadda Yaga Omar din nasa ya samu mace ta gari, a Haka suka Gama diban kayan nasa kamar wasu masu shiri har suka Kai Masa mota, Bayan sun Gama ne Dr. Omar ya kamo hannun Abba suka fito, Saida ya rufe gidan nasu yaga yaron mlm Shamsu zai Shiga gida yyi masa Alamar yazo, yaron ne ya matso Yana kallon Dr. Omar yace, "gani" Dr. Omar yace, "Abbanku na gida?" Girgiza Kai yyi yace, "yaje kasuwa" Dr. Omar yace, "idan ya dawo ka sanar Masa Abba ya danyi tafiya" "Toh zaiji Insha Allah" yaron ya fada dake yanada hankali. tun kafin su iso Meera ta bude Masa gaban mota anan Abba ya zauna ita Kuma ta koma baya yyinda Dr. Omar Kuma ya shige matukin driver.