Sashe 127
Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
har hakoran sa na bayyana ya jawota jikinsa Yana Kai hannun sa Kan shafaffen cikinta yace, "Ina tayamu murna" da murmushi Meera Tace, "wani Abu ne ya faru?" Dr. Omar ya kwanto da kansa daidai saitin kunnen ta yace, "kina dauke da ajiyata" da sauri Meera ta dubeshi Ido cikin Ido Tace, "bestie ban gane me kke nufi ba? Dr. Omar yace, "duk wani alamu ya nuna kina dauke da ciki babe" da murna Meera Tace, "dgske ya Omar?" Girgiza Kai yyi yace, "yes" "OMG!" Meera ta Fadi hakan ta rungume shi da murna shima murnar yake ya rungume ta sosai a jikinsa a kunne ya rada mata, "lalle mun samu Dan Paris" kankame shi tayi tana sa dariya sosai a ranar dai sunyi kwanan farinki har Nafila sukayi Dan nuna godiyar su ga ubangiji, a Jima a shafo ciki Ana Santi Haka dai yau din tasu ta tafi da farinkin samun baby. washe garin ranar kuwa suka bar Paris zuwa Singapore Nan dinma dai akwai sanayyar business ta daddy hakan yasa Basu Sha wahala ba suka Fara yawon bude Ido dukda dai yanzu takatsantsan suke sbd jaririn cikin Meera, sati daya sukai suka tafi Japan, daga Nan dai aka fara yawo Suna lallaba cikinsu har Saida suka Gama bude Ido sosai kafin suka gangaro kasa me tsarki zuwa lkcn cikin Meera har yakai wata bakwai, daidai lkcn ma azumi ne hakan yasa suka tsaya yin umara da Hajj sun ziyarci wurare da dama a Wannan tafiya tasu a lkcn da aka Gama aikin Hajj sukayi nufin dawowa gida sbd Mummy ta bukaci Meera tazo ta haihu a gida Haka ma bikin Safna d Sadeeq za'ayi bayan babbar Sallah. Sun dawo gida cikin koshin lpy, Sadeeq da Safna sune sukaje tarbar su Kamar yadda wancan Karan sune suka musu rakiya, aikuwa sunyi farinciki da ganin junan su, direct gidansu Mummy aka wuce dasu Aiko kamar a goyasu duk gidan son ganinsu suke Hajjaju ma rike Meera tayi a wajenta duk Dadi ya cikasu zasu ga jinin Omar sai Nan Nan ake da Meera dad daya kasa Zama Saida yazo har gida yaga Ameeran sa Haka ma Abba da yanzu yake business sbd daddy ya bude Masa babban shago a wambai Yana sayar da kayan kitchen duk Abubuwan ciki daddy yasa ake kawo Masa daga waje, Abba an Zama babban mutum yanzu ya murje yyi Shar dashi Yana Kuma linkaya a cikin katon gidan da daddy ya bashi, saidai bashi da kowa yanzu ba Mata ba Yara don Sahabatu lkcn da akaje daukota tana ta fama d nakuda jini ya zuba sosai a jikinta baci ba Sha kwana biyu a guje sukayi hospital da ita saidai kafin su karasa Tace ga garinku. Dr. Omar da Meera sun nuna farincikin su kwarai ga duk Wanda yazo gunsu Haka zalika sun bawa kowa tsarabar da suka kawo Masa, Bayan zuwan su garin da sati biyu aka fara shagalin bikin Dr. Sadeeq da Safna d yanzu suka shaku sosai tamkar Wanda suka Dade da sanin juna Kuma duka bangaren kowanne Ahali sunyi farinciki da Wannan aure, aure ne irin na masu dashi hakan yasa akayi gagarumin Biki na gani na fada Dr. Omar ya taka muhimmiyar rawa sosai a bikin frnd din nasa Haka zalika Meera ba'a barta a baya ba dukda tana fama da tsohon ciki hakan be hanata taka rawar gani ba, abin dai gwanin sha'awa Haka dai biki ya gangare ya Kare Safna ta zama matar Sadeeq cikin katon gidansa daya gina. saida aka Gama biki Dr. Omar ya kwashi matarsa suka koma gidansu Dan ya gaji da ganinta daga nesa ba damar latsawa Dan Hajjaju ta riketa Kam, aikuwa Suna zuwa gida ya roki ta barshi ko 5secs yyi Dan a bukace yake da fara'a tace Masa ba komai Dan kuwa itama a daidai Wannan time din jinta take a sama tana bukatar mijinta sosai, Omar harda kukan Dadi yyi Akan Meera lkcn daya kusanceta yaji ta Kara dandano sosai Bayan wata biyu Meera ta haifo katon bbynta sak Dr. Omar harya so zarta Dr. Omar din ma kyau, yaro yaci sunan daddy Abdullahi Suna kiransa da annur, ranar suna kuwa sunga dubban jama'a Kai kace wani bikin auren ake a ranar dollars ne sukayi kuka domin anyi barinsu garin kano da kewaye ba inda ba'ayi zancen bikin sunan Nan ba bikin Suna irin na 'ya'yan Gata Dan shi kansa Dad ba'a barshi a baya ba wajen yin tasa bajintar Haka ma mutanen Adamawa sunzo Kuma sun juya cikin farinciki, Renon yaron su suke cikin kwanciyar hankali, a gefe guda Dr. Omar da Dr. Sadeeq sunata shirye-shiryen yadda zasu bude katon hospital din da daddy ya budewa Dr. Sadeeq a Matsayin kyauta ta nuna farincikin sa ga gudumarwar daya bawa dansa tun yarinta, iyayen Sadeeq har gida sukazo yiwa daddy godiya yace ba komai ai an Zama daya, Dr. Omar ma tun Suna yawon bude Ido ya zana final exam dinsa ta internet Kuma ya samu kyakkyawan sakamako AKTH sunso rike shi yace Sam ba Abinda ya dawo dashi ba kenan, license dinsa Yana hannu Dr. Sadeeq yace toh Saiya Zama babbban Likita wato Wanda zai dinga kawo musu ziyara lkci zuwa lkci, Omar yyi Na'am da tayin sa hakan ya kudirta idan sun koma kasar waje zaiyi Karin karatu Dan ya dinga taimakawa Sadeeq din. Bayan Wata biyar da haihuwar annur suka tattara nasu ya nasu suka koma England inda kasuwanci Daddy yafi karfi sosai.