← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 128

Sashe 103

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ka kwantar da hankalin ka Ameee, ka manta da duk Abinda ya faru a baya ka maida yanzu Kamar mun dade da sanin juna a Matsayin Uwa da 'Danta ka fadamin gsky idan ka Fadi akasin hakan ma kasa a ranka zan gane" cikin tsoro Dr. Ya fara ja baya Dan gaba1 ya dauka ko Mummy nada Aljanu ne yaji Tace, "Bayan Haka ma nidin da ka gani psychologist ce Dukda ba wani aiki nake ba saidai naji takaicin karatuna da beyi aiki akan Saratu ba coz na yarda da ita hundred percent sam-sam ban taba maida kula ga yanayin reaction dinta ba duk Wanda na yadda dashi bana negative thinking a kansa but daga lkcn Dana ji Abinda ya faru brain Dina ta Fara aiki akan kowa ma so ka gayamin mene ya faru" tsakanin Kai da Meera? Ya bude baki zaiyi mgn kenan wayarsa tahau ringing kallon wayar yyi yaga Sadeeq ne ke kiransa kasa dagawa yyi sbd Suna mgn da Mummy ganin Haka yasa Tace, "ba frnd dinnan naka bane?" Gyada Kai yyi Tace, "ka dauka Mana" Kamar Yana jira kuwa ya Kara a kunne ko Jiran Sadeeq beyi ba ya fara mgn Fadi yake yanzu me ake ciki Sadeeq? An samo Address din kuwa?" Duk yyi mgnr da sauri2 Yana fatan ace an dace, cikin sanyin murya Sadeeq yace, "sorry frnd Wlh har yanzu Wai be tuna ba har dakinsa na Shiga tayashi bincike Babu wata paper Babu Alamar ta" tsaki Omar Yaja cikin tsantsar takaici da alama ya fara mancewa Yana gaban Mummy Fadi yake, "Wannan wanne irin rikataccen mutum ne Wai? Dan Allah Sadeeq ka sake cajemin shi" Sadeeq yace, "don't worry duk yadda ake ciki zamuyi mgn" $Okay Thanks" Omar ya Fadi hakan Yana Jan tsaki, Mummy da batasan Kan zancen nasu ba Amma still ta tare shi da fadin, "Wai har yanzu Paper ce ba'a gani ba?" Tayi mgnr cikin damuwa tanason ya saki baki ya fada Mata Abinda suke boyewa, cikin damuwar shima yace, "Wlh kuwa Abu tun safe Kuma yauyau dinnan fa aka bashi takardar Amma harya manta" Mummy Tace, "ikon Allah kamata yyi ya caje Koda jikinsa ne Koh Kuma ka Kira Wanda ya bashi takardar" Cije lips yyi yace, "da ace zan samu number dad din Ameeran ma da sauki to ni Banda ita Mummy gashi sun tafi Adamawa tun safe na kasa sukuni Wlh." Shiru Mummy tayi tana kallon sa at last taji Abinda ke damunsa wato dai Ameera Bata Nan, shirun nata ne ya fargar dashi sakin bakin nasa da yyi tsabar ya Shiga tension ya Masa yawa da sauri yace, "am....Mummy dama Ameeran taje ganin gida ne" Jan zuciya Mummy tayi Tace, "taje ganin gida shine ka kasa sukuni?" Sunkuyar da kansa yyi kirjinsa na harbawa, mikewa Mummy tayi Tace, "kaci food dinka sosai ka koshi yanzun Nan zance nayi mgn da Daddyn ku" ta karasa mgnr tana ficewa, bin kofar yyi da kallo hankalin sa a tashe shikam yau da Alama littafin kundin kaddarar sa aka bude. Koda Mummy ta fito waje direct wajen daddy ta nufa domin harsun tashi a wajen an raka Abba inda zai zauna dukda ma yaso tafiya suka rikeshi, Yana Shirin Shiga Wanka ta shigo dakin fuskar ta cike da damuwa, rikota yyi Yana shafa bayanta Nan suka zauna gefen gadonsa, a nutse yace meke faruwa Na ganki, "cikin damuwa mu daya kamata ace an hada liyafar farinciki" Mummy ta danyi murmushi kadan kafin Tace, "Ameer ne" gyara zamansa sosai daddy yyi yace, "meya samu Ameer din?" Nan Mummy ta fada Masa komai akan Rashin Ameera, sosai hankalin daddy ya tashi dukda Basu taba ganin Ameerar ba Amma a yanda Abba keta Basu lbrnta yasa Sukaji kaunar yarinyar ta Shiga ransu, Dan Haka yace, "Bari yyi Wanka asan abin yi" Dadine ya Kama Mummy Dan Haka itama tabi bayansa Suka shige toilet. Omar da tunda Mummy ta barshi yake ta faman tunani abincin ma spoon biyu yyi yaji ya cika Masa ciki Dan Haka ya Mike da sauri Yana kwasar key din motar sa yyi waje, Yana fitowa kuwa yyi sa'a Babu kowa a parlon hakan ya bashi damar zare jiki zai gudu yaje can gun Ayuba ya caje shi, Yana dab da fita kuwa yaji an Kira sunan sa, a tsorace ya waiga yaga Ashe Abba ne dake tsaye can kasan wata bishiya, juyawa yyi ya nufi inda yake, Yana zuwa kuwa Abba yace, "Ina zaka ne kketa sauri?" Shiru Omar yyi Dan besan mezai fadawa Abban ba, a bisa mmkin nasa yaji Abba yace, "ta gaji da Halinka ne ta tafi?" A mugun firgice yake bin Abban da kallo, Abba ya danyin murmushi irin na Manya kafin yace, "haba Omar ko kwana daya mutum yyi a gidanku ai Saiya fahimci Rashin jituwar ku bare ni da nayi fiye da wata a gidan" kunyace ta Kama Omar ya Rasa inda zai dura kansa yaji Dadi hannayen sa kurum yasa cikin lallausan gashin sa Yana hargitsa shi, Abba yaci gaba da fadin, "a lkcn daka Zo min da zancen Meera Tace ka Kara aure a Wannan ranar na Kara Tabbatar da Rashin zaman lpyr ku Omar, Babu yadda za'ayi a Wannan zamanin kaji mace tana neman kishiya da kanta saidai ko Bata da lpy" bakin Omar ne ya fara rawa yanaso yyi mgn ya kasa, Dan sauke numfashi Abba yyi kafin yaci gaba da fadin, "lkcn daka roki Sadeeq ya koma gidansu Meera a lkcn nasan bakwa tare" "Kayi hakuri Abba" Omar ya furta hakan ransa a dagule, tabe baki Abba yyi kafin yace, "toh ita salmar tana Ina bakazo da ita ba?" Oh Ya Salam! Question again, Omar ya Fadi hakan a ransa Amma Toh ya zaiyi? Haka dai yyi ta maza ya sanar da Abba ya saketa, "Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un..." Abba ya furta hakan a rude Fadi yake, "Omar yaushe ka zama Haka? Wanne irin haline ka tsiro dashi Wanda ni ban sanka dashi ba?? Daga aure Rana daya sai saki???" Lumshe idon sa yyi Yana Sunkuyar da kansa kasa, sosai Abba hankalin sa ya Tashi yace, "kaifa da kanka kaje ka auro musu yarinya meyasa kke nema ka maida mu kananan mutane?" Omar na cije lips dinsa yace, "Kayi hakuri Abba" "Banason ka kasance cikin maza masu auri saki ne Omar, tashi guda Kamar Wanda aka maka baki ba Uwargida ba Amarya??" Still Omar ya Rasa bakin mgn, Jan Numfashi Abba yyi yace, "kaje can gidansu Meeran ka sake jiyo Mana lbrn ta banaso kakai dare baka samota ba" ya karasa mgnr cikin fada2, girgiza kansa yyi cikin ladabi kafin ya juya a hankali ya nufi parking space Yana tada motar sa ya fice a gidan Bayan ya dage glasses dinsa bayaso a ganeshi Dan yasan yanzu Haka hotunan su da labaran su ya Gama game ko'ina, direct gidan su Meera ya nufa. Meera data sauko parlo tana Shirin zama kenan taji Anyi sallama tana juyawa taga wata budurwar wacce Bata wuce tsarar ta bane ta shigo, da murnar ta budurwar Tace, "oyoyo Ameera welcome to Adamawa state" ta Fadi hakan tana rungume Meera, Meera ma rungume ta tayi cikin fara'a sosai tace, "Thanks you very much" sakinta tayi suka zauna tare budurwar Tace, "sunana Asma'u kanwar Ahmad ce ai da tare zamu Zo daukar ku sai Kuma naje islamiyya" Ameera Tace, "Allah sarki Mlm Asma'u ya karatu" Asma'u na murmushi tace, "Alhamdulillah Wai Ina Inna furen ne?" "Gani Nan akwatin radio" Inna fure ta Fadi hakan tana kawo kular abinci inda suke zaune Tace, "Naga alama bakwason zaman wancan kujerun" dariya Asma'u tayi Tace, "haba sai kace ke Inna, mu ai da kwarin mu Koh Ameera?" Ameera na dariya tace, "gaky Kam" Inna tana dariyar itama Tace, "kwaji dashi Banda iyayi meye na tashi sama aci abinci saikace tsuntsaye" Nan suka sa Mata dariya dukansu Suna cikin cin Abincin kuwa Ahmad ya shigo da tasa sallamar, Inna fure ce ta dubeshi da mmki tace, "Ashe kuwa dgske kke" Ahmad yace, "meya faru?" Inna fure Tace, "gashi kuwa ka dawo banyi zaton hakan ba" 'yar dariya yyi yace, "ke kuwa munada bakuwa guda ai dole na dawo mu gaisa" "ikon Allah gaisuwar ta dazu Bata Kare ba?" Ahmad yace, "kedai Inna akwai tmby Kamar 'yar jarida" Meera ce tasa murmushi hakan yasa shi zuba mata Ido tana dago Ido kuwa taga Yana kallon ta hakan yasa ta fara rage dariyar ta, Asma'u ce Tace, "Ya Ahmad yau Babu kallon kwallon ne?" Hararar ta yyi yace, "ban sani ba" 'yar dariya tayi kawai batace komai ba, hakan yasa yace, "Ameera da fatan dai garin Adamawa kinajin dadinsa?" Dan bushashen murmushi ta Masa tana gyada Kai, Inna fure Tace, "haba ita da garin Ummanta? Ai Allah ya kaimu gobe Dan liti ya zaga damu dangi kowa yaga 'yar Aminatu" Ahmad yace, "haba Inna wanne Dan liti Kuma?" Inna Tace, "toh inada wani driver ne daya wuce shi?" Ahmad yace, "ki fada min lkci da Kaina zan zaga daku" Kama haba Inna tayi Tace, "oh su Ahmad an fara mutunci" dariyace ta kwacewa Asma'u da take ta dannewa tun dazu, Bata Rai Ahmad yyi cikin tsawa yace, "ke wanne Dan iskan kike ma dariya?" Tsuke bakinta Asma'u tayi Bata Kara cewa komai ba hakan yasa Meera tayi murmushi ba komai ya Sata hakan ba sai tunowa da Dr. Omar itama yadda yake mata tsawa Yana Bata Rai. Ayuba na zaune yaga fitowar Omar da sauri cikin mota, mikewa yyi tsaye hankalin sa a tashe yace, "yau na Shiga uku nikam ko kisa nayi karshen zarya kenan..." kafin ya rufe bakinsa kuwa Omar ya karaso inda yake fuskar sa a hade yace, "kaga Paper?" Jikin mlm Ayuba ne ya fara rawa yace, "Dan Allah kayi hakuri Wlh na caje ko'ina Banga komai ba dazu2 Nan ma saida muka Gama birkice ko'ina bamuga takardar Nan ba" Omar na matsowa gabansa yace, "ka duba jikin ka?" Mlm Ayuba yace, "sbd Allah kaikuwa me takarda zatayi a jikina?" Bata Rai sosai Omar yyi yace, "inason yanzun Nan ka caje min duk wata maboya a jikin ka" badan Ayuba ya so ba Haka yasa hannun sa a duka Aljihun jikinsa Yana cajewa, duk fitowa yyi da Aljihun ba komai, idon Omar akansa Yana
Chapter 103 · 0% Book details