← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 128

Sashe 32

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dr. Amina ta katse Saratu daga Abinda tayi niyya, juyowa Saratu tayi tace,

"Toh Madallah"

Nan itama ta jawo kujerar data zauna dazu tace,

"Inajin ki"
Dr. Amina tace,

"da farko dai sunana Dr. Amina, ni abokiyar karatun danku ne Dr. Omar"

take Saratu ta fara hade Rai Jin abin ya danganci Dr. Omar ne tace,

"Toh wani abune ya faru?"

Dr. Amina tayi murmushi hade da zira hannun ta cikin jaka ta zaro wasu damun kudi 'yan dubu2 sannan ta dinga juya kudin a hannun ta kafin ta kalli Saratu data saki baki tana kallon bugun Abuja tace,

"Alfarmar ku nake nema ku aura min danku Dr. Omar"

tayi mgnr tana mikawa Saratu damin kudin, Jiki na rawa Saratu ta Mika hannu da sauri tana washe baki tace,

"Ashsha Toh Wai duk Wannan itace Matsalar?"

Dr. Amina ta girgiza Kai tana murmushin Jin Dadi da alama plan din data shirya zai tafi a tsari Dan kafin tazo Saida tasa akayi Mata binciken Ahalin sa gaba1 Dan haka tasan Saratu Sarai wajen son abin duniya, take Saratu ta fara zuba tana juya kudin tace,

"baiwar Allah au Amina, Kin gannin Nan? Nice nake rike da gidan Nan, Kinga mahaifin sa can baida lpy sbd ya hadu da lalurar ciwon baki Dan baya mgn kwata2 shiyasa duk nauyin ya koma Kaina sai Dan Abinda Maru ya kawo sai mu Dan lallaba"

Wani kululun takaicine ya Kama mlm sale sbd yadda ransa ya baci be iya ci gaba da zama ba Kawai ya Mike ya fita waje, Binshi da kallo sukayi Saida ya fice Saratu ta yafito Dr. Amina tace,

"Amina nice Nan mahaifiyar Maru kisa a ranki ko Yana so ko baya so Saiya aureki, Aurenki dashi kamar anyi an gama ne"

Dariya Dr. Amina tayi tana duban Saratu duba na kaskanci hade da ganin dama iri2 daya kamata tayi amfani da saratun tace,

"ni kuwa matukar Kika tilasta shi ya aureni tabbas keda Rashin kudi kunyi hannun riga Dan ko yaushe Zan kasance meyi Miki yayyafin su"

Washe bakinta Saratu tayi cikin murna da ganin kamar tsuntsun ne daga sama gasasshe tace,

"ai ko baki fada ba Naga Alamar hakan 'yar Albarka"

ta fada tana Kara jujjuya kudin hannun nata, Tashi Dr. Amina tayi tace,

"ki bani number ki duk yadda ake ciki sai muyi waya"

da sauri Saratu tace,

"gashi ki dauka zakiga ansa Saratu"

Karba Dr. Amina tayi Bayan ta kwafe itama ta Kira number ta hade dayi Mata saving Nan ta Bata wayar ta, har kofar gida Saratu ta bita tana zunduma Mata Albarka kamar ta goya ta.

•••••�
Hajia Aisha ce tayi shiru cikin wani dakakken lace dinta sai tashin kamshi take tana sauraren Alhji Abdullahi, Alhaji Abdullahi yaci gaba da fadin,

"Wallahi har kawo yanzu fuskar yaron Nan nake gani a idona ban taba haduwa da mutumin daya tsaye min a rai haka ba kamar shi, nake Kuma ganin tsantsar jarumtar sa ta birgewa"

cikin tsoro Hajia Aisha tace,

"Anya Daddyn Safna ba gamo kayi ba?"

'yar dariya yyi Yana rungumo Hajia Aisha jikinsa yace,

"wayace Miki gamo nayi? Ana Miki mgnr ra'ayil ainun"

murmushi tayi tace,

"Naga tunda kazo kketa bada lbrinsa har kasa Nima inason Naga Wannan yaron daya Shigar maka Rai"

Alhaji Abdullahi yace,

"Insha Allahu zaizo sbd inada number sa Zan nemeshi"

Hajia Aisha tace,

"Daka bashi katin ka ai shikenan yafi sauki Kuma bazai Sha wahalar zuwa ba"

girgiza Kai Alhaji Abdullahi yyi yace,

"Ina sane na boye cikakken sunana gareshi sbd zuciyata tana ayyana min nayi wani Abu a kansa"

cikin gamsuwa sosai Hajia Aisha tace,

"Toh Allah ya dafa maka ya Kara tsareka daga sharrin makiya da massahada"

"Ameen Queen"

ya fada Yana me lalumar bakinta cikin shauki.

~~~~~`
A bangaren Dr. Omar kuwa shima kusan hakan ne daga gareshi, harya shigo gari Yana mmkin yadda ya kasa cire mutumin daya gani a ransa, dukda har yanzu Abinda ya faru da safe be manta shi ba Amma hakan be hanashi tunanin Ganin Kwarjinin mutumin ba, Ko takan Mlm Haruna bebi ba sbd ya manta ma da mgnr kawai ya wuce gidansu Dr. Sadeeq Dan mayar Masa mota.

Lkcn dayaje Dr. Sadeeq na gidan Nan suka wuce part dinsa sbd Hajia tadan fita, Ada Dr. Sadeeq jira yake Dr. Omar din ya dawo suje gurin mlm Haruna, Amma yanzu da alama shima zancen ya shafe a kansa saima zama da sukayi suna tattauna matsalar data faru da safe, kamar Dr. Omar jira yake Nan ya fara fada Akan Abinda Meera tayi Masa yace,

"Ban taba tunanin za'aci Amana ta ta hanyar Wannan jaririyar yarinyar ba, Na tabbata duk Abinda ya sameni da hadin bakinta Ina me Tabbatar maka saina koya Mata hankali"

Dr. Sadeeq yace,

"be kamata ka yanke hukunci cikin fushi ba Omar yarinyar Nan abin a duba yanayin ta ne"

Dr. Omar yace,

"Yanayin ta? Ni lkcn data nemi zubar min da mutunci na ta tuna yanayin dazan Shiga? Look ni da ita duk 'yan Adam ne Dan haka yadda suke da brain haka Nima nake da brain ba Kwakwalwar kifi gareni ba"

Shiru Dr. Sadeeq yyi sbd yadda yaga Dr. Omar din yadau zafi sosai, can yace,

"Toh duk wannan kumfar bakin d kkeyi wanne mataki kke Shirin dauka a kanta?"

Cije lips dinsa Dr. Omar yyi cikin takaici hade da shafa sumar kansa yace,

"AUREN TA zanyi..."✍�
8/15/20, 8:02 PM - Ummi Tandama: *200 ne kacal👌🏻 ba yawa Domin sanin yadda Zaki biya ki nemi Wannan number 09039118754*

......🐓🐓🐓

Na
*Nuceeyluv😘*

20....

Zaro Ido Dr. Sadeeq yyi cikin matukar mmki yace,

"aure Kuma?"

Dr. Omar ya dube shi sosai kafin yace,

"haramun ne?"

Girgiza Kai Dr. Sadeeq yyi yace,

"yanzu sbd kanason Rama lefin da tayi maka shine zakabi ta hanyar aure? So kke ka munafurci iyayen ta sannan ka cutar da ita sali'alin batare da'an sani ba? Haba Omar ka dawo hayyacin ka Mana karkazo kayi Abinda zakazo kana Dana sani"

Cikin bacin Rai sosai yace,

"and so what?? Wannan matsalar tace"

Ya fada Yana buga gefen kujera da karfi, Dr. Sadeeq yace,

"Toh karatun ta fa? Yanzu ta fara fa"

tsaki Dr. Omar Yaja Yana Shirin tashi yace,

"Ba Abinda ya kaita makarantar ba kenan Dan haka bana tunanin Zan barta taci gaba"

Dr. Sadeeq yace,

"Haba da..."

"Enough pls"

Dr. Omar ya katse shi yana daga Masa hannu hade d mikewa tsaye kafin ya fice a parlon gaba daya, binsa da kallo Dr. Sadeeq yyi Yana jinjina girman hukuncin da Dr. Omar din yake Shirin yi.

****
Nas da Saratu har dare suka Kai kunnen su a bude suna jiran suji lbrn mutuwar Alhaji Abdullahi Amma shiru kkeji ba lbri, ta bangaren Nas sai neman number ogan 'yan daba take Bata samu ba, ita Kuma Saratu sai duba waya take taji an kirata Kan zancen mutuwar taji shiru, har bcci ya kwasheta bataji wani lbri ba hakan yasa Koda Dr. Omar ya dawo batasan ya shigo ba sbd be shigo gidan da wuri ba sai Bayan Isha sosai, Dan haka washe garin ranar da wurwuri ta shirya Dan jin Abinda ake ciki saidai kirjinta bugawa yake sosai sbd tana tunanin ko Kama 'yan daban akayi Basu sani ba? A tsorace dai ta karasa Shiga gidan nasu.

~~~~
Acan bangaren Dr. Omar kuwa Yau skul dinsu ya wuce direct sbd Kiran gaggawa da ake Masa daga shugabansu na faculty dinsu, lkcn dayaje skul din wajajen 10 ne sbd Rashin bccin da beyi ba jiya yasa duk ya makara, Tunda ya Shiga skul din yaga kowa sai kallon sa yake sharewa yyi sbd yasan Abinda ya faru a kotu ne yasa kowa ke Masa irin Wannan kallon take wani irin zazzafan takaici ya sake makure Masa wuya sbd tunowa da wacce tayi silar zubewar mutuncin sa a idon duniya, harya Isa faculty din nasu ba'a daina kallon sa ba wasu har leken sa suke duk Yana lura dasu ta Wutsiyar Ido idan ba an gaya maka bama tabbas bazakace yasan Allah yyi ruwansu a wajen ba, zuwansa office din keda wuya yyi knocking aka bashi damar Shiga,

Professor Akilu ne Kan kujera Yana juyawa a hankali hade da system a gaban sa, Tsayawa Dr. Omar yyi be zauna ba saima harde hannayen sa da yyi, professor Akilu ya dago kansa a hankali ya dubi Dr. Omar sannan ya nuna Masa kujera Alamar ya zauna, zama Dr. Omar yyi sannan yace,

"Sir naji kana nemana"

Prof Akilu ya girgiza Kai Yana Dan gyara medicated glass dinsa yace,

"Karbi Wannan"

yyi mgnr Yana Mika masa Wata doguwar takarda dayayi printing yanzu, Karba Dr. Omar yyi be duba jikin takardar ba ya zubawa Prof Akilu Ido Dan neman Karin bayani, Prof Akilu ya maida bayansa jikin kujera Yana Dan juya biron dake hannun sa yace,

"Dr. Omar salees"

"Yes sir!"

Dr. Omar ya Amsa still idonsa Akan Prof, Prof yace,

"ba iya Wannan faculty din ba, harta sauran faculties din dake school dinnan kowa Yana sane da irin zubar Mana da mutuncin da kayi especially you da bamuyi tsammanin hakan daga gareka ba"

Cije lips Dr. Omar yyi Yana Dan lumshe ido hade da budesu Kan Prof Akilu, Prof yaci gaba da mgn Yana fadin,

"Ada hukuncin da makaranta ta yanke a kanka shine mu koreka sbd bazamu lamunci duk wasu Bata gari da zasu kawo Mana cikas wajen gurbacewar daliban mu ba, Toh Amma sbd kwazon ka da yadda ka kasance zakaran gwajin dafi first class yasa ka samu rangwame zaka sake maimaita wata shekaran ma'ana bazaka zana jarabawar final year da colleagues dinka ba, sai next year, Dan haka sai a kiyaye gaba"

prof Akilu ya karasa mgnr Yana tsare Dr. Omar din da ido. A bisa mmkin sa sai gani yyi Dr. Omar din Yana murmushi, Dan haka ya zuba Masa ido Yana jiran me zaice, kallon takardar Dr. Omar yyi Yana Dan jujjuyawa a hankali fuskar sa cike da murmushi Shiru office din ya dauka Babu me mgn, can Dr. Omar ya kalli Prof Akilu duba na kaskanci sannan ya maida Masa takardar Kan table yace,
Chapter 32 · 0% Book details