← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 128

Sashe 60

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mgnr tana nuna Meera, wani irin shocked ne ya Kama Meera din Ranta a mugun bace ta dubu Dr. Omar da Shidin ma yake tantance sunan da aka kirata dashi mmki ne sosai ya Kama shi dayaga bacin Rai karara Akan fuskar Meera sbd sunan da Salma ta kirata dashi duk irin cin zarafin da yake mata be taba ganin bacin ranta Haka ba, hakan yasa take yaji wani Dan guntun tunani ya shige shi, komawa mazaunin sa yyi ya zauna Yana Dan murmushin gefen baki, da alama zaiyi amfani da Salma wajen muzanta Meera din, hakan yasa ya dago da kansa fuskar sa kadaran kadahan Yana duban Salma yace, "Alright mubar Wannan mgnr ki sameni gobe around 11am sai mu tattauna akai" yyi mgnr cikin kulawa, dubansa Salma take da mmki Anya kunnen ta yaji sosai? Karkada hannunsa gaban idon Salma yyi yace, "Yadai?" Yyi mgnr Yana kallon ta a nutse, Salma da murna ta Kama ta Tace, "I..I'm.really surp...." "Shiiiii..." Dr. Omar ya katse ta da sauri Yana sa Dan yatsan sa a baki, shiru Salma tayi tana murmushi tace, "okay Bye" tayi mgnr tana juyawa a hankali hips dinta na cewa bye2 sbd irin juyasun d take, Dan satar kallon Meera Dr. Omar yyi yaga ta cika tayi fam, hakan yasa ya dada maida hankalin sa sosai Kan Salma da niyyar cusawa Meera takaici sbd taga ya bita da kallo, saidai kashhh Irin juya hips din da Salma take Saida tasa mazantakar sa ta motsa har wani Dan girgiza tayi abinka da dama can be Gama warwarewa daga takurar da lollipop din tasa ta Masa jiya ba, d sauri ya kawar da kansa Yana dukar dashi tare dayin Istigfari, Fitar Salma keda wuya ya bawa Meera kwarin gwiwar matsowa inda Dr. Omar din yake ranta a bace tace, "yanzu duk Abinda kkemin be wadatar dakai ba har saika kawoni wajen aikinka ka zubar min kima da mutuncina a idon duniya??" Tayi mgnr Kamar ta fashe Dan haushi gaba1 wani irin makakin kishin Salman ne ya taso mata, Dagowa Dr. Omar yyi zuwa yanzu fuskar sa a daure take sosai yace, "Au Ashe kinsan me ake Kira da kima da mutunci? Shine Kika watsar min nawa?" Ya karasa mgnr da Dan daga murya, Sunkuyar dakai Meera tayi tana Dan share zafafan hawayen da suka zubo mata a hankali Sam Bata da bakin mgn Kuma yanzu itakam Yaya zatayi ta goge Wannan bakin tabon da tayi Masa ne? Zaton ta Abinda tayi shine zai kawo maslaha ga Rayuwar sa Ashe rusa Masa rayuwa tayi, ta kashe shi da ransa Bata sani ba, Tsaki me sauti Dr. Omar Yaja be Kara bi ta kanta ba yaci gaba da aikin dake gabansa, A Wannan Rana dai Haka Meera da Omar suka kwashe awanni a office Babu me cewa da Dan uwansa ci kanka Koh lunch basuyi ba Koda yake Bata sani ba ko Shidin yyi domin ya fita na wani lkci dazu itan ce dai kamar wata me azumi saidai tayita share kwalla lkci bayan lkci, har lkcn tashi yyi, koda yazo tafiya ma Saida yaje har jikin kofa ya waiwayo tana rakube daga gefe a zaune yace, "Zaki taso mu tafi ne Koh kuwa anan Zaki kwana?" Yyi mgnr Yana binta da Harara, Tasowa tayi da hanzarin ta domin ta gaji dama d Wannan zaman a Haka suka sauko har izuwa can inda yyi parking motar sa. Direct unguwar su Abba ya nufa dama tun jiya be leka yaga yadda Abba yake ba, Meera d kanta ke duke saijin tsayuwar mota taji Ashe har sunzo, shiru yyi Yana tunanin Shiga da Meera gidan wajen Abba, Yasan idan Abba ya kalleta a Wannan yanayin zai iya tuhumar sa dukda bazaiyi mgn ba yasan zai nuna alama, Kallon gorar ruwan gefensa yyi ya Ciro a hankali Yana dubanta Yace, "kee" Meera da har yanzu hawayen Basu daina zuba ba ta dago da kanta a hankali tana kallon sa duk idonta yyi ja, kawar dakai yyi Yana Mika mata gorar ruwan dake hannun sa yace, "karbi Wannan ki wanke Wannan hawayen munafurcin da kikeyi banason ganin sa" yyi mgnr Yana cilla mata robar jikinta, dauka Meera tayi har yanzu Jan zuciya take batace Masa komai ba ta bude motar kadan ta fara wanke idonta, Saida ta Gama ta rufe murfin muryar ta a dashe Tace, "na Gama" juyowa Dr. Omar yyi yaga har yanzu kwalla Bata bar idonta ba yace, "sauran munafukar kwallar da Kika Bari fah?" Yyi mgnr Yana tsareta da Ido, Dukar da kanta tayi kasa tace, "kayi hakuri hawayen yaki tafiya ne" "Mtwsss.." Dr. Omar Yaja tsaki yace, "look banason gulma duk yadda za'ayi kiyi domin Wannan shegun hawayen naki su bace daga fuskar ki Dan bazamu Shiga gida a Haka ba" Kallon sa tayi da sauri kirjinta na bugawa da karfi kodai gidan ubanta ya maida ta? Tayi mgnr a ranta tana kokarin karewa yanayin unguwar kallo, sai yanzu ta fara ganin wata unguwar ce ba tasu ba a hankali ta sauke boyayyar ajiyar zuciya jawo Dan kwalinta tayi da niyyar goge kwallar Dan ta tafi gaba1 taji ta taho da dogon gashinta harya fito waje, a rude ta Dan saci kallon Dr. Omar taga Ashe ba itan yake kallo ba Nan ma ajiyar zuciya ta saki tana kokarin nannade dogon gashin nata ta cikin hijab, bayan ta Gama ne tasa Dan kwalin nata ta goge sauran kwallar da Bata Gama tafiya ba, Saida fuskar ta tayi wasai kafin ta maida dankwalin nata tana gyara hijab taji yace, "muje" fitowa sukayi daga motar tana daga gefensa suna tafiya a hankali saidai shi yadan zartata sbd yanayin tafiyar tasa da yakeyi cikin Isa da takama Wanda ya kasance nature dinsa ne amma a fili sai aga Kamar da sanin sa yake hakan, itadai nata shine ta bishi a Haka har suka karasa kofar gidan nasu, batayi mmkin ganin yanayin gidan nasu ba Dan tun tuni taji su Aunty Shafa na lbrn asalin Dr. Omar din sai kallon yanayin gidan nasu take har suka Shiga ciki, Shiru Kamar ba mutane a gidan Dr. Omar ya sake Yin sallama sai sukaji alamun tahowar Abba daga dakinsa, Meera dake gefensa ganin Abba ya iso da fara'ar sa ya tarbesu Yana binsu da kallo yasa ta saki ranta sosai hade da Isa wajensa ta tsugunna Tace, "sannu Abba barka da yamma" tayi mgnr cikin tsantsar ladabi, kallon ta Abba yyi da murmushi ya juya ya kalli Dr. Omar kallo na tuhuma Dan yyi mmkin ace matar daya aura tsawon Wannan lkcn ace batasan baya mgn ba? Wanne irin zama sukeyi Wannan?? ganin irin kallon da Abba yake masa ne yyi hanzarin matsawa gaban Meera cikin taushin lafazi kamar gske yace, "Oh! Meeeraaa kin manta na fada Miki Abba baida lpy baya iya mgn ai" yyi mgnr kamar gske, Dagowa Meera tayi a hankali ta zube Masa manyan idanunta da suke kyalli gaba1 mmkinsa ne ya kamata kanta Kuma ya daure tamau, yaushe sukayi Wannan mgnr dashi? Ganin zata jika Masa aiki ne yyi mata mgnr Ido Yana dage mata gira, hakan da yyi da Kiran sunan ta da yyi besan cewa Yana tafiya da dukkan Imani ta bane domin gani take kamar b Dr. Omar din daya Gama ci Mata zarafi bane yanzu, Amma dake itama tasan kalar irin Wannan abun ta juyo da sauri harga Allah dukda batasan mafarin meye matsalar Abba ba taji a ranta tana tausayin sa sosai cikin yanayin tausayawa tace, "eyya sannu Abba Wlh na sha'afa ne" tayi mgnr tana matsawa gefe ta zauna kan kujerar tsungunno data gani, taci gaba da fadin, "Allah ubangiji ya baka lpy" girgiza Kai Abba yyi cikin murmushi Yana nuna alamun Jin dadinsa, zama shima Dr. Omar yyi yana gaishe da Abba, Nan Abba ya girgiza Masa Kai, Bayan sun Gama gaisuwar ne Dr. Omar ya dubi gidan kaca2 Alamar dai Babu shara da mmki yace, "Sahabatu Bata Nan ne?" Yyi mgnr Yana tsare Abba da Ido, Dan Jim Abba yyi be nuna Alamar komai ba, Dr. Omar ya Kama hannun sa yace, "ta samu saukin ne harta samu damar fita?" Girgiza Kai Abba yyi yanayin sa na canjawa, Gaban Dr. Omar ne ya Fadi Toh meke faruwa ne? Ciro wayarsa yyi da nufin Danna Kiran Saratu, Meera na gefe tayi shiru duk tausayin Rashin mgnr Abban ya dameta, Dr. Omar kuwa Saida ya gwada Kiran Saratu har sau uku ya kasa, Ana hudun ne dai yyi nasarar danne zuciyar sa ya Danna Kiran, bugu biyu yaji ta dauka muryar ta raurau tace, "Alo" Dan cije lips dinsa Dr. Omar yyi yace, "Ummah" Jin muryar Maru ce yasa Saratu ta Mike da sauri domin a parlon hajiya Aisha take ana shirye-shiryen bikin Sageer, Saida ta matsa can bayan fulawa kafin tace, "ya akai?" Danne zuciyar sa yyi yace, "dama Nazo gidan ne sai naga Sahabatu Bata Nan shine nace ko ta samu saukin ne?" Saratu dake can barin tace, "au so kke kazo ka ganta kwance ita kadai gwalam a gida?" Girgiza Kai Dr. Omar yyi kamar Yana gabanta yace, "ba Haka bane Ummah" Saratu taja tsaki tace, " 'yata na kaita inda za'a kularmin da ita bazan barta a gidan Nan ba domin mahaifinta ma baida amfanin dazai iya tmbyr ta Abinda takeso" rintse ido Dr. Omar yyi kamar ya kwada wayar a kasa Haka yakeji, can yaji Saratu Tace, "Kai gwara ma daka Zo kasan yadda zakayi da wannan tsohon marar amfani domin Nan inda nake aiki zamuyi bikin babban Danmu, bikin da ba'a taba yin irinsa ba, biki na Dan masu dashi ba irinka da kayo gadon talauci ba" Sauke wayar Dr. Omar yyi Yana me kawar da kansa gefe Dan baya son daga Abba har Meera su fahimci irin mugun bacin ran da yake ciki, Abba ne ya riko hannun sa Yana matsawa a hankali, hakan yasa Dr. Omar yaji zuciyar sa tadan rage zafi a hankali ya juyo Yana kallon Abba da murmushin yake yace, "Zamu tafi dakai Abba kafin ta dawo" yyi mgnr Yana dukar da kansa, dago kansa Abba yyi Yana girgiza Masa Kai Alamar bayaso, Dr. Omar yace, "Dole muje tare sbd Nan din waye zai kula dakai? Tunda ba yanzu tace zata dawo ba"
Chapter 60 · 0% Book details