← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 128

Sashe 36

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ke rabamu da kaska mukasan me zatayi Masa idan ta ganshi?"

Anty Jamila na dariya tace,

"kice bakyason ayi kwace ai na manta Ashe mayya ce"

Anty shafa na latsa wayar ta Dan Kiran su Surry tace,

"Naki Wasa ne aini ko kadan bazan Bari ya Kara ganinta ba"

Anty Jamila tace,

"Harshi Dr. Omar din plan dinmu Yana tafe kansa Dole ya kware Mana"

dariya Anty shafa tayi tace,

"Kina manta wanne hukunci akayi Masa Koh?"

Anty Jamila tace,

"Toh Dan an koreshi ai kyawu da cikar surar sa tana Nan"

a firgice Meera ta dago kanta sbd Jin furucin da da sukayi, baki na rawa Tace,

"Dan Allah ku fahimtar Dani me kuke nufi da zancen Dr. Omar?"

Wani irin mugun kallo Anty shafa ta bita dashi kafin tace,

"Korar sa akayi daga school din kinada Abinda zakiyi ne?"

Ta fada tana Kama qugu.

"Qalu innalillahi wa'inna ilaihin raji'un"

Ameera ta Furta hakan cikin matukar tashin hankali.
8/15/20, 8:03 PM - Ummi Tandama: *200 ne kacal👌🏻ba yawa Domin sanin yadda Zaki biya ki nemi Wannan number 09039118754*

....🐓🐓🐓

Na
*Nuceeyluv😘*

22...

"Ke dallah rufe Mana baki"

Anty Jamila ta Furta hakan cikin fada2, saurin Kama bakinta Ameera tayi tanajin kwalla na cika Mata Ido, Anty shafa na saka takalmi tace,

"ke Kika biye ta ma ki kyaleta Mana tayi ta ihu Tanada Abinda zatayi ne?"

Anty Jamila na Saba jaka tace,

"ai Naga nema take ta cika Mana kunne gwara idan muka fita sai tayi ta ihunta ita ta sani"

dariya Anty shafa tayi tace,

"Matsalar ta"

Nan suka fice a dakin cikin yauki da yanga Kai kace sun Isa wajen su Sageer din, fitarsu keda wuya ya yasa ta fashe da wani irin kuka me tsuma zuciya, Nan ta kifa kanta tana kuka hade da surutai Fadi take,

"banyi maka Adalci ba Dr. Omar, nayi Dana sanin shaidar Dana bayar a kanka Wlh ba laifina bane dole tasa nayi haka, daliline ya jawo haka, ban taba zaton cewar Abinda na aikata zai taba karatun ka ba, yanzu ta Ina Zan ganka domin na sanar maka gskyr Abinda ke tafiya??"

Ta karasa mgnr tana sake rushewa da kuka tamkar wata sabuwar kamu.

*****
Dr. Sadeeq ne ya zubawa Dr. Omar Ido cikin matsanancin tashin hankali yace,

"frnd meyasa tun a jiya baka sanar Dani Abinda ke faruwa ba? Kasan bana gari naje jigawa wajen granny bansan Abinda ke faruwa ba sai yau Dana Shiga skul naji anata yamididi da zancen"

Dan tabe baki Dr. Omar yyi kafin yace,

"look frnd karka wani damu d Abinda sukai just focus on your exam kasan befi 2days ku fara ba"

cikin kunar Rai Dr. Sadeeq yace,

"Sageer again? Wai uban me ka tare Masa aduk fadin makarantar Nan ne?"

Dan murmushin takaici Dr. Omar yyi yace,

"Ita rayuwa bazaka taba sanin kana ci gaba ba sai ka hangin Tarin makiyan ka masu hassada, So Abinda Sageer yyi min tare da sauran Wanda suka Mara masa baya Yana nuna nidin Allah yyi min wata baiwa wacce ba kowa ke samun irinta ba shiyasa sukaga na cika musu Ido, na zame musu karfen kafa dole suyi yadda zasuyi domin su fitar Dani"

"No Wlh bazamu barsu haka ba Dole a dauki mataki a kansu shiyasa tun farko nace a daukaka Kara a tsananta bincike nasan dole gsky zata bayyana"

Dr. Sadeeq ya Fadi hakan ransa na Kara baci duk ji yake shima B.U.K din ta fara fice Masa a Rai, Dafa kafadar sa Dr. Omar yyi kafin yace,

"Kasan wani Abu?"

Yyi hakan Dan kawar da zancen Sageer din Dan ji yake idan Ana zancen sa zuciyar sa tafasa take Yana ji kamar yaje ya dauki doka da hannu, yanaji kamar yaje ya zubar Masa hakora shi da duk sauran masu Sanya hannu a ciki, Amma Inaa so yake shima ya dandana Masa bakin ciki cikin ruwan sanyi Wanda zaiji gaba1 duniyar tai Masa zafi matuka, Dr. Sadeeq ya girgiza Kai batare da ya Furta komai ba, Dan cije lips dinsa Dr. Omar yyi kafin yace,

"mun hadu da mutumin Dana baka lbri"

Dr. Sadeeq yace,

"Wanda ka taimaka a wajen 'yan daba?"

Dr. Omar yace,

"Yes shi dai"

Dr. Sadeeq yace,

"Da alama akwai Abinda kuka tattauna a tsakanin ku"

Dr. Omar ya girgiza Kai sannan ya fara sanar dashi dukkan Abinda sukayi da Alhaji Abdullahi hatta sunan company din Saida ya Gaya masa, Tunda Dr. Omar ya ambato sunan company din Saida Dr. Sadeeq ya girgiza, Tabbas company din Alhaji Abdullahi Omar me fata ne wato baban Sageer, Jin beyi mgn ba yasa Dr. Omar ya dubeshi yace,

"banji kace wani Abu akai ba"

Wani mugun yawu Dr. Sadeeq ya hadiye ya fahimci kwarai Dr. Omar din besan cewa Alhaji Abdullahi shine mahaifin Sageer ba, Dan sosa kansa yyi yace,

"eh..Toh.. A gsky na jinjinawa lamarin ubangiji dubi yadda cikin kankanin lkci Allah yyi maka canji da mafi Alkhairi"

Dr. Omar ya danyi murmushi kadan sannan yace,

"ni Ina kallon Abubuwan ne takmar a film ko novel Kai kamar wani mafarki ma zakayi mmki idan nace maka I'm feeling comfortable Idan Ina tare dashi, Sai nakejin wata irin yadda a gareshi 100% I don't know what is going on"

Dr. Omar ya Furta hakan Yana shafa sumar kansa, Shiru Dr. Sadeeq yyi tabbas a yadda yakejin lbrn Alhaji Abdullahi yasan cewa mutum ne da baya tolerating nonsense, mutum ne da yake kaifi daya, akwaishi da kwazo da neman na kansa shiyasa companies dinsa suka samu karfi a Nigeria Yana Kuma da hadin gwiwa da wasu kamfanin na kasashen ketare, karyar ma'aikatan sa su kawo Masa wargi saidai idan baya Nan su shakata Amma daya dawo zakaga Ana aiki ka'in da na'in he's a busy man be cika zama sosai ba, shiyasa ake ganin wautar Sageer daya kasa maida hankali ya taimaki mahaifin sa sbd yau da gobe sai Allah idan Babu mutuwa akwai tsufa.

Dan numfashi Sadeeq Yaja a ransa yace tabbas bazan Bari Wannan damar ta kubucewa Omar ba, bazan sanar dashi company din baban Sageer bane Dan matukar ya sani bazaiyi aikin ba, sannan yanaso Sageer ya fahimci dukda an koreshi daga skul Allah be barshi haka ba, Allah baya zalunci, Allah yyi Masa canji da mafi Alkhairin rayuwa, zaiyi iya kokarin sa Dr. Omar be fahimci da waye yake aiki ba, sannan zaiyi kokari sosai yasa Sageer be fahimci Ina Dr. Omar yake aiki ba, zaiyi Masa hakan a Matsayin sa na aboki Abinda zai iya taimaka Masa kenan a Wannan Abinda ya same shi, Dr. Omar ne ya girgiza shi sosai yace,

"tun dazu sai tunani kke Ina lura dakai Koh akwai wata matsalar ne?"

Murmushi sosai Dr. Sadeeq yyi yace,

"Ba wata matsala"

Dr. Omar yace,

"are you sure?"

"Very very sure"

Dr. Sadeeq ya Furta hakan sannan yaci gaba da fadin,

"kawai kayi accepting nasan zaka iya, kanka Yana ja sosai"

ya karasa mgnr da murmushi, Dan duka Dr. Omar yakai Masa yace,

"duk kaina ai ban kaika ba"

Dr. Sadeeq yace,

"kaiii rufamin Asiri muna dai saffa saffa"

Dr. Omar ya canja topic din Yana Dan yatsina fuska yace,

"Inason wani taimakon ka plss"

Dr. Sadeeq yace Fadi,

"meye shi?"

Yanayin Dr. Omar ne ya fara canjawa zuwa bacin Rai sbd tuno Abinda yake shirun fada, sosai bacin Rai ya bayyana karara Akan fuskar sa murya can kasa kamar bayason mgn yace,

"Inason ka Nemo min address din yarinyar Nan"

Dr. Sadeeq ya bishi da kallon mmki yace,

"Wai baka fasa ba?"

Dr. Omar yace,

"na fasa? Haba Amma ba sunana Omar ba kenan"

Dr. Sadeeq yace,

"Ana aure dan a samu farinciki da walwala a raya sunnar ma'aiki amma Kai naka bansan wanne iri kke nufi ba"

Dr. Omar Yana hade Rai sosai yace,

"Irin auren da kke fada Yana Nan tafe a lkcn Dana samu kalar yarinyar da nakeso, a lkcn zanyi tunanin auren walwala zanyi, Amma Wannan auren da zanyi na yanzu Ba lalle ne ya cika wata hudu ba"

Da mmki Dr. Sadeeq yace,

"haba Omar wanne irin aure ne na wata hudu? Ina lefin ku sasanta kanku"

"God forbid"

Dr. Omar ya Furta hakan da sauri Yana ci gaba da fadin,

"kaiiii Amma ka cuceni Wlh, ba'a taba kwarata ba irin yau me zanyi da Wannan jaririyar yarinyar? Haba gsky ka Gama Dani"

Dr. Omar ya Furta hakan ransa a mugun bace,

"Okay calm down"

Dr. Sadeeq ya Furta hakan Yana ci gaba da fadin,

"a kalla idan bakayi Dan ita ba sai kayi Dan mutuncin ka da Kuma Ahalin ka, tunda ba sonta kke ba ka hakura kuyi kamar shekara 1 kaga shikenan Babu me zargin kayi Rashin adalci"

Tabe baki Dr. Omar yyi yace,

"bana tunanin zama da ita har tsawon Wannan lkcn kawai inason na koya Mata hankali ne kafin na tsinka igiyar aurena da ita"

Badan Dr. Sadeeq yaso ba haka yyi shiru Yana tausayin Abinda Zai faru da Ameera.

~~~~~
Tun daga bakin gate da aka sauke Saratu take Jin kida na tashi da karfi, haka a darare ta karasa Shiga cikin gidan, Nan taga Abinda ya girmi tunanin ta Mata da maza ne cunkushe sunata rawa a tsakiyar field din gidan kowa sai ihu ake Ana raye-raye, can ta hango Sageer rike da wata yarinya sun manne qugu-qugu d kugu anata shagali,

"Yau na Shiga uku"

Saratu ta Furta hakan a rude, daidai lkcn Sageer ya juyo Yana kallon ta yace,

"yauwa ke saratutu maza wuce ki fara Abinda ya kawo ki"

yyi mgnr Yana nuna Mata cikin parlon gidan, Kasa motsi Saratu tayi sbd Shiga tashin hankalin Abinda taga danta nayi Akan idon ta,

"ke dallah wuce"

yyi mgnr Yana zuqar tabar dake hannun sa, a tsorace ta wuce tana waiwayon sa daidai zata Shiga kawai taga ya zura harshen sa cikin bakin Anty shafa Yana tsotsa, tsabar firgitar da tayi batasan lkcn da tudun kofar parlon ya bugeta ba sai ji tayi ta zame a wajen ji kke kwall kanta ya bugi da tiles din wajen,

"hehehehe..."

Gaba1 mutanen wajen suka kwashe Mata da dariya, Wani daga cikinsu anace dashi wizy yace,

"ke tsohuwa Kalli gabanki tun dazu sai kallon mu kike ko har yanzu da sauran sha'awa a jikin ne?"
Chapter 36 · 0% Book details