← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 128

Sashe 49

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saida tayi kukanta me isarta kafin ta share hawayen ta cikin Jan zuciya ta fara bin yanayin parlon da kallo, duk wani tunani nata ya kunce Bata da wani zabi a yanzu sama da tayi Abinda yace din, Haka dai jiki ba kwari ta Kama stairs Dan haurawa sama Bayan ta kwaso duk wasu kayan aiki data gani daga can gefen parlon kamar dama Dan ita aka ajiye, tana share kwalla Haka ta Isa gaban dakunan biyu, budesu tayi duka taga duk sunyi kura ba komai a ciki Dan ko furnitures Babu, Haka ta bude toilet din ciki ta cika shi da ruwa kafin ta dawo daki ta fara sharewa, kafin wani lkci harta Gama sharar abinka da an riga an Saba tun a gida, Bayan ta Gama ne ta fara mopping gashi tiles din fari Kal tun daga na toilet har na dakunan na corridor ne ma yadan banbanta, da nishi da komai Haka ta Gama gyaran saman gaba1 harta gangaro izuwa matattalaka ta karshe dake kasa, hatta gefe d gefen matattakalar Suma ta goge, Bayan ta Gama ta rike qugunta cikin wani irin yanayi na wahala sake duba girman Parlon tayi Nan taga lalle fa akwai sauran aiki a gabanta Dan Haka ta daure taci gaba da aikinta tana me Jan zuciya har yanzu.***** Shigowar Saratu gidan Alhaji Abdullahi kenan ta hango Sageer da Hajjaju a tsaye d alama surfa Masa bala'i take, Karasawa tayi wajen tace, "barkanku da safiya" tayi mgnr tana Dan tsayawa Dan son Jin Akan me suke mgn, ko kallon inda take basuyi ba saima ci gaba da mgn da Hajjaju tayi tace, "Kai sageeru badakai nake ba?" Sageer cikin Rashin kunya yace, "nifa Hajjaju kin fara kaini bango Taya za'ai komai nayi kice banyi daidai ba? Yanzu Shigar Nan tawa ko a birnin London Wlh takai" cikin jin haushi Hajjaju tace, "Bantan ubanka, nace kaci Bantan ubanka kaji Koh? Yanzu ka dubi Shigar Nan taka wando Koh gwiwa be Kai ba wuya nannade da sarkoki sai kace jikan Dan bori Koh Kuma Karen kiwon makwabtan mu..." "habaaa Hajjaju" Sageer ya katse ta Yana saka hannayen sa cikin bujen wandon sa yace, "idan kikace jikan 'yan bori Toh ya tabbata kece dai borin Dan tanan na biyo" tafa hannu Hajjaju tayi hade da salati tace, "nice 'yar borin?" "Atho? Haka dai kikace sa'idawa" ya fada Yana juyawa, juyowar da zaiyi yaga Daddy tsaye bayansa ba tare daya tantance komai ba yaji an dauke shi da Mari, Wannan Marin ya jawo hankalin Saratu kansu Dan duk Basu San da zuwan daddy ba Ada kawai ta tsaya tana dariya ne ta ciki sbd Abinda takeso Sageer keyi wato ya daina ragawa Hajjaju Dan ta cika takura da sa Ido wani abin ma idan ta yunkura zatayi a gidan idan ta tuno da tsohuwar Nan tsoron Yi take.., "Ashe Rashin hankalin naka yakai Nan Sageer ban sani ba?" Daddy ya katse shirun da mgn cikin fada, dafe kumatun sa Sageer yyi Yana huci kamar zai fashe, kamar daga sama tsugul Saratu ta tsoma baki da fadin, "Dan Allah ayi hakuri Alhaji yarinta ne watarana idan ance yyi bazaiyi....." "Dallah kauce" Hajjaju ta katse ta hade da ture ta can gefe saiga Saratu a kasa Tim bin Hajjaju tayi da sauri ganin yadda taji ta sa Mata Kashi, Hajjaju taci gaba da fadin, "munafukar Allah Ina lura dake tunda kikazo Nan kinajin dan banzan yaron Nan yanata zazzaga min Rashin kunya baki dakatar dashi ba sai yanzu shi da ake Masa fada zakice a daina? Kewai meye hadinki da shi ne? Dan na lura kullum akayi Masa fada ranki bayaso" A mugun tsorace Saratu tace, "kiyi hakuri Hajjaju dazun ma Ina Shirin Yi Masa mgn Alhaji yazo" daddy ya katse zancen da fadin, "maza jeka ka canza Shigar Nan idan ba so kke ranka yyi mugun baci ba" juyawa Sageer yyi cikin fushi kamar zai bangaje daddy ya wuce su ko waiwaye bayayi, "ai ka gani koh?" Hajjaju Tayi mgnr tana kallon Alhaji Abdullahi daya bi Sageer da mmki, Hajjaju tace, "bana tunanin Wannan yaron yanada cikakken hankali, Kai nifa hankali na yafi karkata Anya yaron Nan jininmu ne?" A firgice suka maida kallon nasu wajenta, daidai lkcn Safna ta karaso wajen Dan fita zasuyi da daddy zai nuna Mata sabon GM din company dinsa Dan yadda sukeji yabon da daddy yake Masa yasa Safna tace itakam bazata jira sai an kawo shi ba zataje can ta ganewa idonta, Hajjaju ce tace, "Toh meye duk kun wani zubamin Ido? Abinda zuciyata ke rayamin na fada" tayi mgnr tana juyawa Dan barin wajen, Safna na ganin Haka itama taja hannun daddy suka bar wajen ya rage sai Saratu datayi suman zaune, hankalin ta ba karamin tashi yyi dajin furucin Hajjaju ba Anya zata Bari Wannan matar takai lbri kuwa? Domin a hankali dai gashi nema take ta nusar da mutanen data rufe musu Ido zuwa Kan Abinda ta birne shekara da shekaru, Ganin kamar ta fara janyowa kanta kallo agun sauran ma'aikatan gidan yasa kawai ta Mike tana kade zanin ta Nan ta nufi part din Hajia Aisha zuciyar ta na wasu tunanin daban. Acan bangaren Dr. Omar kuwa, zaune yyi cikin sabon office dinsa Yana duba wasu takardu da aka ajiye Masa, tunda Dr. Omar ya karbi ragamar aikin company din komai ya fara dawowa tsari Yana daidaituwa, hakan ba karamin mmki yake bawa Alhaji Abdullahi ba yadda yaga kamar Wanda ya zauna a aji aka koyar dashi, shiyasa kullum baya gajiya wajen jinjina Masa da Kuma sa Masa Albarka, Yana cikin cike takardun kuwa yaji anyi Masa knocking, zaton sa PA dinsa ne Dan Haka yace, "yes come in" Ya Furta hakan Yana ci gaba da Abinda ke gabansa, "Amincin Allah ya tabbata a gareka" yaji wata siririyar murya ta daki dodon kunnen sa, shiru yyi shi be dago ba shi be Amsa ba saima mmkin yadda akai PA dinsa yabar mace tazo Masa har cikin office yake batare da an nemi izinin sa ba, Dan Haka ya dago Rai a hade a takaice yace, "Ameen" tsaye take cikin Shigar doguwar riga pink ta yane kanta da mayafi hade da 'yar karamar jaka rataye a kafadar ta, doguwace sosai Dan da kadan ma Dr. Omar din ya fita tsayi duk tsayinsa kuwa sai hips dinta dake a cike Tam ga kirjinta shima tsaitsaye sun cika sunyi fam a takaice dai shape dinta ya fito sosai cikin kayan data saka, Kawar dakai Dr. Omar yyi cikin kakkausar murya yace, "get out" Dan murmushi yarinyar tayi tace, "haba Omar bansan me sunan ka da irin Wannan halin ba domin Shidin ya kasance me maraba da bakinsa" tayi mgnr tana kokarin Jan kujera zata zauna, tashi tsaye yyi da sauri cikin zafin zuciya yace, "I said get out..." Ya Furta hakan cikin karaji, a firgice yarinyar ta juya ta fice saura kadan ma ta buge da kofa sbd waiwaye, duba inda PA dinsa yake yyi yaga baya Nan Nan ya Kuma Jan tsaki ya Rasa wanne irin shiririta ne da Habib, Ko 1hr ba'ayi ba kuwa yaga wayarsa na ringing, Daddy shine Abinda ya baiyana Kan screen din nasa, dauka yyi hade dayin sallama cikin nutsuwa, daddy dake can barin shima ya Amsa kafin yace, "idan ba damuwa inaso kazo office Dina yanzu" "Okay Daddy" Dr. Omar ya Furta Yana Shirin tashi Dan Amsa Kiran nasa, daddy daya aje waya ya dubi Safna da murmushi yace, "yanzu Zaki ganshi" Safna tana murmushi itama tace, "ai tuni na kosa" dariya suka sa a tare Safna najin dadin yadda taga daddy ya ware sabanin dazu dayake cikin bancin ran Sageer. Dakyar ta karasa jikin motar ta tana haki, budewa akayi ta ciki Nan ta shige da sauri tana sauke ajiyar zuciya, "yadai Salma ko baki dace bane?" Salma na kallon me mgnr ta lumshe ido tace, "kedai Bari lubna Wannan gayen yadda muke zaton sa ya zarce tunanin mu" lubna tace, "haba dai kamar bakisan Kan mazan ba? Kece fa salmy mace me yaudarar maza Kuma kici nasara" Yatsina fuska Salma tayi tana me kallon lubna tace, "ai tunda nasa Raina Akan shi saina aureshi bazai yiyu na boye true color Dina a banza ba, Dana sameshi na watsar da komai Dan nasan irin kalar Wannan zaiyi Mai sosai" tafawa sukayi suna dariya lubna tace, "Amma bakida kyau sai kace wani Nama" Salma tace, "kedai Bari idan Ana Sallah ba'a mgn" lubna na dariya tace, "gskyne Dan Haka yanzu saimu tafi Kafin ki Kara komawa next time" murmushi Salma tayi tace, "ai bazan Kai kasa a gwiwa ba." Knocking Dr. Omar yyi daddy ya bashi izinin Shiga, Dr. Omar ya bude kofar hade da sallama, amsawa Sukayi kafin daddy ya nuna Masa wajen zama ya zauna, Sam Dr. Omar be lura da Safna dake gefen daddy ba Dan Haka Yana zama ya fara gaishe da daddy, amsawa daddy yyi yace, "ya aiki" "Alhamdulillah" Dr. Omar ya Amsa da murmushi, Daddy yace, "yaudai da kanwar ka mukazo" ya Furta hakan da murmushi Yana nuna gefen da Safna take, kallon gefen Dr. Omar yyi da mmki sai yaga Ashe akwai mutum a wajen karaf idanun su suka hade Ashe tun dazun daya shigo Safna ta kafe shi da ido ko kiftawa batayi, shima samun kansa yyi da kallon ta ya kasa janye idonsa daga gareta wani irin Abu dukkansu sukaji Yana fisgar su, daddy ne ya katse musu shirun da fadin, "Wannan itace Safna Auta kenan" ya karasa mgnr Yana dafa kafadar Safna sai a lkcn ta dawo tunanin ta tana Dan Murza Ido a kunyace tace, "daddy" daddy yace, "ga sabon Yaya da nayi Miki kamar yadda kika sani Dr. Omar Amma Zaki kirashi da Ya Omar" murmushi sosai Safna tayi ta zamo daga Kan kujera sbd yadda taga yyi Mata kwarjini ainun cikin ladabi tace, "Ya Omar Ina kwana, ya aiki? Da fatan mun sameka lpy." Tayi mgnr a jere ga mmkin su sai suka ga Dr. Omar din ya fara murmushi harma fararen hakoransa suka bayyana sosai Yana kallon Safna cikin wani yanayi wanda shi kansa besan dashi din a jikinsa ba yace, "haba lil sis irin Wannan gaisuwa wanne Zan Amsa a ciki?" Dariya Safna tayi tana dukar da kanta,
Chapter 49 · 0% Book details