Sashe 71
Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
take ciki kafin ta fito a parlon, tana zuwa gun su Anty shafa suka Mike Anty shafa na fadin, "Mom Sageer yace masu daukar suna hanya muje muyiwa dad sallama kafin su iso" kallon su Mom tayi tana murmushin yake tace, "yanzun Nan daga wajen sa nake ina shiga Naga ya fito da key a hannun sa Wai anyi Masa Kiran gaggawa ne acan ma'aikatar su" Jamila ce Tace, "kasshh Amma dai Mom kinsan dai Babu kudi ajikin mu da baki Bari ya tafi ba sbd munaso ya sallame mu da wani abun" ja baya Mom tayi Tace, "Kiran yanada muhimmancin ne saidai kuyi amfani da sadakin ku" Anty shafa tace, "Mom Wai har kin manta ne?" Mom Tace, "me kenan?" a hankali Anty shafa tace, "kudin cikon boka ne fa muka Kai Masa gaba daya sadakin mu 200k akan samun mallakar mazajen mu bita zaizai Nan fa kudin namu ya tafi" dafe goshi Mom tayi gaba1 ta manta da sunyi Wannan Shirin sbd yadda kanta yadau zafi ji take kamar ya rabe biyu ga tashin hankalin da canjin dad yake kunno mata ga Rashin ishashe kudin dake wajen su, Anty Jamila ce Tace, "ba matsala idan ya dawo saiki karba Mana kisa Lami takai Mana" (sabuwar me aikinsu sbd lalaci sun kasa yin komai a gidan Saida aka Nemo me tayasu) Mom na murmushin yake tace, "Toh Shikenan" suna tsaye Haka akace Wai Ina amare ne har an gama kwashe masu rakiya? Anan Mom ta rungume yaran nata tana hawaye su kuwa ko a jikinsu, saima dariya da suke sbd sunsan daular da zasu Shiga, a Haka aka rabata dasu har suka fice a gidan Suma ba dadewa aka kwashe su sai gidan mazajen su. Tun ranar da Dr. Omar ya gayawa Meera matsayinta a gunsa da yadda ya dauketa ta dauke Masa wuta, Sam yanzu Bata bi ta kansa itama sai idan suna tare da Abba suyi drama kamar Ana zaman Dadi hakan yasa Abba Sam be fahimci Rashin jituwar dake tsakanin su ba, Kuma dukda Haka Meera Bata fasa sauke hakkin duk wani Abu daya rataya a kanta ba so take kafin tabar gidan saita Tabbatar Bata da hakkin Omar a kanta, daga Nan tasan cewa Allah zaiyi Mata sakayya ta inda Bata zato domin Yanason masu hakuri. Yauma kamar kullum Meera tana dakin ta Dan yanzu Bata cika zama parlo ba tunda Omar yace komai tanayi ne Dan ta samu kusanci dashi shiyasa ta koma zaman daki dukda tanajin soyayyar sa a zuciya hakan be hanata danne wa ba Dan gani take Son maso wani take wato koshin wahala, Gama cire kayanta kenan ta samu Dan karamin kwalinta ta daura Bata da towel din Wanka Dan Haka da dankwalin take daurawa idan zata Shiga, Dan kwalin ko hips dinta be Gama rufewa ba ta Isa gaban mirror, karon farko dai yau ta tsaya tana yiwa kanta duba na tsanaki, a hankali take karewa surar jikin nata kallo, Doguwace daidai misali ba irin sosai dinnan ba, Haka zalika kirjinta a cike yake fam Kamar Wanda aka hurasu da iska, cikinta a shafe yake kamar an kifa faranti yyinda Ramin cibiyar ta yake fari Tass Babu Alamar dauda a ciki idan aka gangara Kan duma-duman hips dinta kuwa abin ba'ace komai domin a dunkule idan aka hada zai baka asalin me ake Kira da figure 8, dogon gashin kanta na daure dukda Haka ya sauko baya ta cije lips dinta a hankali tana tunano munanan kalaman da Omar ya jefeta dasu ranar, tana tsaye a bakin mirror taji iska na kadawa sosai ashe hadari ne ya taso kafin wani lkci har an kece da ruwa kamar da bakin kwarya, Meera dake jikin madubi tabar wajen ta Isa jikin window take ta tsuwara ruwan dake sauka da karfi Ido, washe baki tayi tanaji Kamar Ana janta ta fada ruwan tayi Wanka a inda takeyi duk lkcn da ruwan sama yazo, ata wajen lungu yadan Shiga ba lalle ma a ganka ba sbd ta saman da ruwa yake zuwa ta wajen anan Meera ke tsayawa tayi Wanka, Mika hannun ta tayi ta window take ruwan ya fara jika mata shi sai juya hannun take tana wasa dashi, Ganin hakan bazai Mata ba Kawai ta fito da Wannan daurin kirjin nata tayi waje da Dan gudun ta gashin kanta na warwarewa da kansa ta zaga baya, daidai lkcn Dr. Omar dake dakinsa ya Gama zuge labulen dakinsa dake can sama Yana kurawa ruwan dake zuba da karfi Ido.