Sashe 58
Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
tasa sakwarar a gaba ta fara ci tana korawa da ruwa Saida taji ta koshi Tam kafin ta tashi ta fito waje, zaton ta zata ganshi Kan kujera saita ga sabanin haka, itama kawai saita wuce nata dakin ta rufo kofa. **** "Haba Shafa jibi yadda kikayi kaca-kaca da kitchen dinnan kamar wacce zatayi abincin mutum dubu" Anty shafa da tun dazu take kiciniya da fulawa sai gumi take tace, "banason iya shege Jamila idan Zaki zauna muyi Abinda ke gaban mu gwara ma ki zauna Dan lkci tafiya yake" ta karasa mgnr tana yarfe gumi, karasa Shiga kitchen din Jamila tayi tana Jan tsaki tace, "nifa Wlh na gaji haba tun jiya sai asara muke mun gagara hada meatpie bare samosa Toh inaga cake Kuma?" Shafa tace, "idan bamuyi ba Dame kikeso mu tari Sageer din dashi? Ko so kike ajinmu ya zube?" Sake Jan tsaki Jamilan tayi tace, "Toh Wai Ina mom ne? Ai itace matar gida ita ya dace ace tasan irin Abubuwan Nan" Wannan karon shafa ce taja tsakin tace, "kinsan halin mom dai Sarai Bata zama sai kace kanta aka fara kasuwanci" ajiye Ledar hannun ta Jamila tayi tana debo kayan siyayyar datayo musu tace, "lalle kuwa aiki na gaban mu" shafa zatayi mgn kenan Sukaji waya na ringing hakan yasa tayi shiru tana daukar wayarta ganin Sageer ne me Kiran yasa ta gyara murya tana iyayi tace, "hello" Sageer dake can bangaren yace, "yauwa frnd inason Naga babyn tawa taci gayu" tabe baki shafa tayi tana danne haushinta tace, "baka da matsala ai muna Nan muna shirya maka ita" Murmushin Jin Dadi Sageer yyi yace, "Thanks you aikin ku na kyau" "Nevermind" Shafa ta Furta tana katse layin d sauri Dan dab take data dura Masa zagi, Jamila ce tace, "Dan anacen ita yake tmby Koh?" Cikin kunan zuciya tace, "bar Dan dur*n uwa duk yadda na sakar Masa jikina ace har yanzu zuciyar sa tana gun Ameera?" Jamila tace, "ai kima daina Bata ranki a banza ba mun riga mun dauki matakin da zamuyi ba idan yazo?" Kwafa Shafa tayi tana hura hanci ta turar da robar gabanta da take kwaba fulawa tace, "haba abin ne dacin Rai Yarinya ko 'yar gwal ce iyakaci kenan" Jamila tace, "Toh Kinga yanzu ba lkcn maida zance bane ni da ke duk kanwar Jace babu me iyayin Abubuwan da muka lissafo dama Meera nanan ne duk sai tayi Amma yanzu da Bata kusa dole kudinmu yyi ciwo Dan Haka kafin ya iso muje waje mu siyo snacks dinnan" "Kwarai kuwa kin kawo shawara" Anty shafa ta Furta da murna Dan dama duk ta gaji gashi ba'ayi komai ba, tashi sukayi suka koma dakinsu a gurguje suka shirya kafin suka bar gidan gaba1. Acan bangaren Sageer kuwa lkcn da suka Gama Waya da Anty shafa be damu da katse Kiran da tayi ba saima murmushin Jin Dadi da yake Yana kallon Faisal dake gefen sa, Faisal yace, "lalle da alama ka mato Akan yarinyar Nan" Sageer yace, "Kai ba Dole ba? Wai nake Gaya maka kasan me ake Kira da kayan Alatu? Billahillazi Dan iskan Omar dinnan ya cuceni ranar, da tuni na Dade da maida kwadayina a kanta, haba ai tunda na gansu na sake birkicewa dole na kwashi Wannan ni'imar domin yarinyar Nan zatayi ruwa-ruwa" dariya Faisal yyi yace, "haba harda wani ruwa-ruwa?" Sageer yace, "naka wasa ne domin ni Naga Abinda na hango kiris ya rage nayi nutso a korama Dan bakin cikin ya karaso" Faisal yace, "yanzu Kam ai ka Gama dashi" sageer yace, "sosai ma kuwa ai so nake na Aureta na Kara kunsa Masa takaici nasan duk lkcn daya ganmu tare kila ya hadiyi zuciya" ya karasa mgnr Yana wata irin dariyar mugunta har Yana shekewa. 8/15/20, 8:05 PM - Ummi Tandama: *YADDA ZAKI BIYA* Zaki turo da 200 ta Wannan Account din 0030202448 Nusaiba Mustapha Sterling Bank saiki turo da shaidar biya ta Wannan Number 09039118754 ko Katin MTN ta waccar number👆ðŸ»