← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 128

Sashe 19

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A bangaren Saratu kuwa ji tayi kamar ruwa ya cinyeta lkcn da Sageer yake caccakar ta da mugayen kalamai, ji take kamar tace Sageer nice uwarka Amma ba halin hakan, sai dai kurum ta tsaya sauraron sa hankalin ta a mugun tashe ace Dan data Haifa shine yake nuna Mata tsana karara? Wanne wacce irin rayuwace? Har sai yaushe zata huce ta dangwali Arzikin da take buri tun shekaru talatin baya? Lkcn da Hajia Aisha ta dauke Sageer da Mari Saratu ji tayi kamar ita aka Mara har cikin zuciyarta taji Marin shiyasa yanzu haushin Hajia Aishan Ya mamaye Halin da Sageer din ya jefa ta dazu Dan jin son danta Sageer take har cikin ranta...

"kiyi hakuri kinji"

taji mgnr Hajia Aisha ta katse Mata tunanin ta, Dan kankaro murmushin dole saratun tayi tace,

"ba komai ai Hajia yaro ne wataran akace yyi bazaiyi ba"

Hajia Aisha tayi Mata alama da hannu tazo Saratu ta matsa ta zauna kasan carpet, Hajia Aisha tace,

"bansan meyasa Sageer yake Miki irin Abubuwan Nan ba dukda irin son da kike Masa shiyasa kullum bazan gaji da baki hakuri ba sbd kinsan ance uwa na son Wanda yakeson danta shiyasa har kunya nakeji bisa Kan Abinda yake Miki"

Saratu a ranta tace Dan ki ko nawa? Ai dole nayi gaggawar gyara komai Dan Dana ya fahimci nice mahaifiyar sa, a fili kuwa cewa take,

"ayya karkiji komai ni duk Abinda yaron Nan yake banajin komai sbd nasan yarinta ce watarana zai daina musamman da Allah ya kawo mu wani Zamani da Dole sai muna hakuri da wasu halin na yaran namu"

Hajia Aisha ta dubeta da tausayi irin Wannan hakurin na Saratu shike Kara Mata girmanta a idonta, a nutse tace,

"shiyasa nakeson nayi mgnin sa ai, yaron Nan Sam yaki tsaida Mata gashi kullum shekarun sa Kara gaba suke"

Dan washe baki Saratu tayi tace,

"kice Hajia zaku hadashi da 'yar manyan mutane kenan Dole kowa yasan da zaman ubanta sbd shigowa Wannan ahalin da zatayi"

Hajia Aisha ta danyi murmushi tace,

"meyasa sai 'yar manyan mutane?"

Saratu tana Sosa Kai tace,

"kinsan masu iya mgn kance kwarya tabi kwarya toh fa lalle Babu me karawa da Wannan gidan sai Wanda shima ya jika da abin tagomashi"

Hajia Aisha ta girgiza Kai tace,

"ba burina kenan ba, nafiso ya samu yarinya me nutsuwa sai a Aura Masa Koda basuda Hali idan sunada Hali na gari da mutunci ai shikenan"

Saratu ba haka taso ba Amma a fili tace,

"Kinyi gsky Kam"

Hajia Aisha taci gaba da mgn,

"shiyasa nakeson zumuncin mu dake yaci gaba zamu biyo Masa ta Bayan fage saidai yaji an daura aurensa da 'yar wajenki Sahabatu...."

"Kanwar tasa????"

Saratu ta furta a gigice Hankalin ta a matukar tashe, zuba Mata ido Hajia Aisha tayi batace komai ba, ganin haka yasa Saratu Tasha jinin jikinta Ashe fa subutar baki tayi? Da sauri ta wayance da fadin,

"Ina nufin ai kanwar tasa ai..da..toh..ai..anyi Mata Miji..ehh.."

ta karasa mgnr bakinta na rawa, Hajia Aisha ta girgiza Kai cikin fahimta tace,

"ai Dama Abinda nakeson karasawa kenan kika katse ni dama so nake naji ko ba'ayi Mata Miji ba sai a hadasu aure"

Tashin hankali Saratu ta fada a ranta, a fili ta washe bakin Dole Fadi take,

"ai Hajia tuni ma akai Mata Miji Wlh kuwa ehh ai yanzu haka zancen da nake Miki an kusa sa ranar Tata"

Saratu ta saki baki sai zuba take bakai ba gindi, Hajia Aisha tace,

"Toh Allah ya kaimu lkcn"

"Ameen Ameen"

Saratu ta furta tana goge zufar goshinta data feso Mata lkci guda sbd shiga rudani, Hajia Aisha tace,

"Toh ko a unguwar ku Koh Wanda Kika sansu na mutunci masu karamin karfi ki tayani nema Dan so nake na bashi mmki Dan tun wuri nake binsa ya fitar da Mata yaki shi Wai be girma ba shiyasa na yanke shawarar saidai yaga matar kawai"

ta karasa mgnr da murmushi, wani kululun takaicine ya makure a makoshin Saratu a ranta Fadi take kaji 'yar bakin ciki Dan nawa kikeso ki maida baya? Bayan Allah ya daga darajar sa? Billahillazi bazata Sabu ba haka kurum Zamani ya canja auren jari ake Yasin....,

"bakice komai ba"

Hajia Aisha ta katse Mata tunanin, Saratu na yaken Dole tace,

"gani nayi hajiya kar muyiwa yaron Nan Shigar sauri tana iya yiyuwa ko yanada matar Basu Gama daidaitawa bane bare ma da Matsayin ki Hajia 'yar da zata zama surukar ku ai sai 'yar babban mutum kamar ku."

Hajia Aisha ta maida bayanta jikin kujera tace,

"Zanyi tunani akai Amma fa auran 'yar me karamin Hali Babu fashi matukar be canja halinsa ba"

Saratu tace,

"sai hakuri, hakuri ake hajiya"

Ta furta tana kokarin tashi, Hajia Aisha tayi murmushi kawai tanajin zafin yadda Sageer yake neman maida Rayuwar sa. Anan dai Saratu tayi Mata sallama tabar parlon cike da bakin cikin Abinda Hajia Aisha ke Shirin Yi.

••••�
Da sauri suka fito daga harabar hospital din cikin mota, Sadeeq Yana kallon Dr. Omar yace,

"kamar fa mun makara"

Dr. Omar Yaja tsaki yace,

"I don't know why sukace sai ni zanyi Bayan Nima akwai aiki a gabana"

Sadeeq yace,

"ai ba wani dadewa zamuyi ba just one hour kawai"

Dr. Omar ya duba agogon hannun sa 10am akwai littafin da yakeson dubawa sbd dab suke da zana final year exam dinsu ta barin makarantar, Amma tun jiya 'yan faculty dinsu suke son yyi musu tutorial, Bece komai ba Kawai ya maida kansa jikin window,

"karbi Wannan"

Sadeeq ya Miko Masa envelope Dr. Omar ya kalleshi Yaja tsaki sannan ya sake kauda kansa, Sadeeq ya danyi dariya yace,

"Kai nifa na gaji da ajiyar su Duk Zan tattaro maka na kawo maka message din da ake turo maka duk lkcn daka bushi iska dan niyyar kanka saika karanta, Dr. Omar ya Harare shi yace,

"Wannan Kuma matsalar ka ce"

Sadeeq Yana dukan steering cikin dariya yace,

"kodai taka matsalar ba? Nidai nawa ajiya toh takardun sun fara cikamin daki gara na tattaro maka saika karanta daga masoyan ka ne na sani."

Tabe baki Dr. Omar yyi daidai lkcn suka iso cikin makarantar. A gurguje suka wuce faculty dinsu lkcn har an taru a hall kuwa ba Bata lkci ya fara gudanar musu Abinda ya kaishi.

Tunda ta sako kafarta skul din ta hade fuska sosai Addu'a take a ranta Allah yyi Mata tsari ga duk wani me mugun nufi a kanta, haka kuwa ta samu damar yin signing dinta successfully, befi daya ya rage Mata ba Lkcn taje gun Wanda zaiyi ance baya Nan Amma bazai Dade ba zai dawo Dan haka take sauri yanzu ta koma karya tafi, so take gaba1 ta Gama ta huta especially da taji har an fara lecture su har yanzu suna shiririta.

Form din nata ta nema ta rasa Dan haka ta fara binciken files din, Bata tsaya gefe ta duba ba Kawai taci gaba da tafiya a hakan tana dubansa shiyasa Sam batasan meye a gabanta ba,

Garaaam....., Taji tayi Karo da mutum take files din hannun nata suka watse kasa, batare da Bata lokaci ba Kawai taji an dauketa da wani irin gigitaccen Mari, Haba Meera itama batayi wata-wata ba ta sharara mari ga Wanda ya maretan yanzu, Dan Wannan Alwashi ta daukarma kanta duk Wanda ya sake kawo Mata raini bazata barshi ba Dan a dalilin haka akaso Yi Mata auren dole gwara ta Tabbatar wa su Anty shafa sabgar samari basa gabanta, take aka Shiga kallon kallo Tsakanin *DR. OMAR SALEES da HAFSAT IBRAHIM (AMEERA).*
8/15/20, 8:01 PM - Ummi Tandama: *ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA...🐓*
( _ko Ana Muzuru Ana Shaho Sai yayi_)

Na
*Nuceeyluv😘*

13....

Gaba1 mutanen dake harabar wajen shock ne ya Kama su Kai hatta Sageer dake nesa dasu tare da mutanen sa Saida ya Shiga shock, take Meera Tasha jinin jikinta sbd tunowa da aika aikar da tayi, Amma sbd yadda aka zuba musu Ido yasa ta maze kawai ta sunkuya tana tattare files dinta, tsananin mmki me cike da dunbin takaici ne ya makure Omar da har yanzu be daina Mata kallon mmki ba, Ji yake kamar ya harbeta da kafa Dan haushi, bacin Raine ya sake Kama shi dayaga ko a jikinta tana Shirin kwashe files dinta, Cikin zafin Nama ya fisgo hannun ta, Meera dake sunkuye ta dago da sauri tana kokarin kwace hannun ta cike da Rashin kunya tace,

"dallah mlm sakar min hannu ko an Gaya maka ni irin sakarkarun matan Nan ne da kuka Saba bigewa akan layi? Toh ku sani kunyi na farko na share yanzu Kam a shirye nake da naci mutuncin duk Wanda yake neman Shiga harkata"

Tayi mgnr cikin bacin Rai itama sbd tunanin ta irin wa'annan mazan da suka bangaje ta ne da gangan ranar da Sageer ya rungume ta, Wani kyakkyawan marin Omar ya sake kafta Mata take Meera ta duka kasa a gigice tana sakin wani marayan kuka, Sadeeq dake gefensa tun dazu yyi saurin matsowa wajen sa, riko hannun sa yyi Yana fadin,

"frnd ka barta haka Nan baka lura ita din new comer bace?"

Wani mugun kallo Omar ya bishi dashi, shi gaba daya ma ji yake Kamar ya buge duk mutanen da suke wajen sbd tsananin takaicin da yake ciki, ba'a taba wulakanta shi ba sama da Abinda akai Masa yau, Mari? Kuma Mace?

"Kaiiii...."

Ya furta hakan a fili Yana dunkule hannun sa tare da kaiwa dayan hannun naushi jikinsa sai tsuma yake ransa na suya, Sadeeq ya dafa goshin sa tabbas yau an tabo 'yan maza Dole ya sake kamo hannun Omar din Dan idan ya barshi ya sake zuciyowa zaiyiwa 'yar mutanen lahani cikin rarrashi da lumana Sadeeq ya samu nasarar janye Omar daga wajen especially daya ga mutane sun fara taruwa a wajen sosai. Tafiyar su keda wuya Sageer ya matso wajen ransa fari Tass Abinda ya Dade Yana buri kenan kullum idan ya kalli fuskar Dr. Omar ji yake kamar ya kafta Masa Mari Amma Babu damar hakan, Dan haka yyi murna kwarai da irin Marin da Meera ta sharara Masa,

"Weldon baby"

Sageer ya furta cikin tsananin farinciki Yana tafa hannu,

"kinyi babban aiki"
Chapter 19 · 0% Book details