← Book details Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 128

Sashe 92

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

su Saratu kuwa dakyar suka samu me napep din daya kaisu kasurgunmin dajin da aka Basu lbri ance akwai wani zazzafan boka da aikinsa yake tamkar yankan wuka Da baya2 suka karasa jikin bukkar bokan Kamar yadda yace suyi, suna karasawa kuwa ya Mike zumbur jikinsa na karkarwa kafin su zauna ya dakatar dasu Yana fadin, "maza ku fice min daga waje kafin bala'in ku ya shafen" a razane Saratu da Nas suka dubi juna kafin suka kalli bokan harya fara nade taburmar sa da hanzari, a rikice Saratu Tace, "boka baka sanmu ba bamu sanka ba Wannan shine zuwan mu na farko wajenka me mukayi Haka da zakace bala'in mu zai shafeka" bokan ya zaro jajayen idonsa kwala2 sai kace Aljani yace, "ke har kina da bakin tmbyr Abinda kukayi?" A tsorace suka sake duban juna, bokan ya dauko wani madubin tsafi Yana nuna musu shi yace, "ku kalli Nan waye?" Nan suka ga fuskar wancan bokan nasu ya bayyana, ja baya sukayi a firgice baki na rawa sukace, "ai Wannan bokan da muka Saba zuwa wajen sa ne" wasu tofi ya sake Yi jikin madubin sai gashi Kamar film Yana nuna wancan bokan wuta ta Kama dashi, gaba1 yanzu gigice wa sukayi da ganin yadda wancan bokan yake ci da wuta Yana ihun kururuwa, Wannan da suke tare dashi ya daka musu tsawa Yana fadin, "Asirin da kuka birne shekara da shekaru ya balle a takaice mutumin da kuka rufe Masa baki ya samu lpy shine silar duk wani wargajewar komai" cikin matukar tashin hankali da rudani jikin Saratu na rawa Tace, "ka karamin haske boka Wai kana nufin mlm sale ya samu lpy?" Nas dake gefe ma jikinta Banda kyarma ba Abinda yake, tsaki bokan Yaja bayan ya zura madubin tsafin sa cikin jaka yace, "Abinda nake nufi kenan Dan Haka sai kusan inda dare ya muku" "Mun shiga uku mun lalace" Nas da Saratu suka Furta hakan hankali tashe, tsoro ne da firgici ya musu dirar makiya lkci guda, bokan na fara tafiya Saratu tayi saurin kiransa tana fadin, "Dan Allah kayi wani Abu gaba1 a tarwatsa su subar min Dana da dukiya" Juyowa yyi a razane yace, "Ashe kekam kin Gama haukacewa kafin lkcn haukar naki yyi Banda ke bagidajiya ce kina ganin Wanda ya muku aiki ya kone d ransa Nima so kike na kone?" Nas da itama duk ta rikice tace, "Dan Allah ka rufa Mana Asiri Wlh bamu San inda zamu dosa ba tunda Asirin Nan ya tonu shikenan tamu ta Kare" wani banzan kallo ya musu kafin yace, "sai kuyita zama anan har Mahdi ya bayyana" Yana Gama fadin Haka yyi gaba abinsa kafin ma wani lkci harya bacewa ganinsu, Wannan Abu ya sake birkita tunanin Saratu da Nas Nan suka dinga ihu a dokar daji ba salati bare neman taimakon ubangiji, tafiya suka farayi batare da sunsan inda suka nufa ba Haka sukaci gaba da tafiyar hartakai ga sun gaji sosai ga mmkinsu hanyar da suka biyoce da Amman yanzu ta bace masu batt sai suka tsinci kansu cikin wani kasurgumin dajin daya zama gaba jeji baya jeji Nan hankalin su ya sake dugunzuma kafin wani lkci harsun fita hayyacin su. Koda Meera suka Shiga jirgi murna ce fal ranta sai washe baki take abinka da sabun shiga tana dab da dad dinta suna cikin tafiya Tace, "dad" Ya Amsa Mata Yana kallon ta, Saida tadan Debi mintuna kafin Tace, "Wai meya faru bayan bana Nan?" Murmushi me sauti dad yyi yace, "nasan tun dazu kike dauke da Wannan tmbyr, nikuma na zabi damu Isa can Adamawa sai nayi maki bayanin a tsanake dukda dai bana son tuna fuskar su bare lbrn su Amma zan sanar dake komai Abinda ya faru" Dan murmushi Meera tayi Tace, "Toh Shikenan Dad Nagode" 'yar dariya yyi Yana fadin, "har yanzu Meera banyi Abinda Zaki godemin ba" Meera na murmushi sosai tace, "iya kasancewa dakai dad ya isar min komai Wlh Wannan shine burina a Koda yaushe Naga Ina tare da dad cikin farinciki Kamar lkcn da Ummah take raye" ta karasa mgnr muryar ta nadan rawa, shi kansa Dad kwallace ta Dan ciko Masa ido har Ila yau bazai taba yafewa Mom ba domin ta cutar dashi cutarwa ta karshen karshe ta rabashi da gudan jininsa Meera, saidai bazai gaji da yiwa Allah godiya ba daya kawo Masa agaji a lkcn da yake cikin duhu.
Chapter 92 · 0% Book details